Yadda Na’urar ATM Ke Aiki (1)

Bayan kasidar da muka gabatar a shekarun baya kan manyan matsalolin tsarin ATM a Najeriya, a halin yanzu wannan fasaha ta habbaka, kuma masu amfani da ita sun yawaita. Hakan ya dada taimakawa wajen samun karin ingancin tsari da mu’amala da na’urar ita kanta. Da yawa cikin masu karatu sun bukaci a musu bayani kan hakikanin wannan na’ura da yadda take aiki, amma a kimiyyance. Wannan shi ne abin da za mu fara gabatarwa a wannan mako. A sha karatu lafiya.

428

Matashiya

Shekaru biyu da suka gabata idan mai karatu bai mance ba, mun gabatar da kasidu guda biyu masu take: “Matsalolin Katin ATM Sun Fara Bayyana a Najeriya.”  A cikin wadannan kasidu guda biyu masu magana kan abu daya, mun yi tsokaci ne kan matsalolin da suka fara bayyana a wancan lokaci na sace-sacen kudade da ake yi ta hanyar wannan na’urar cire kudi mai suna Automated Teller Machine, ko ATM a gajarce.  Fadakarwa ce musamman ganin daidai lokacin ne wannan sabuwar fasaha ta bullo wannan kasa, kuma da yawa cikin jama’a basu san makaman amfani da ita ba.  A yau kuma ga mu dauke da bayani kan yadda wannan na’ura take aiki. Da bayanai kan tsarinta, da bangarorinta, da kuma yadda take sarrafa bukatun mai amfani da ita a lokacin da yake neman cire kudadensa daga gareta.  Har wa yau akwai bayanai kan ‘yan matsalolin da ke faruwa musamman idan mutum ya zo cire kudi sai katinsa ya makale; me ke haddasa hakan? Kuma me ke sa wasu lokuta za ka sa katinka a cikin wannan na’ura da niyyar cire kudi, sai ka kasa?  Wasu lokuta ma sai a aiko maka tes cewa ka cire kudaden, bayan na’urar ta ce maka “Babu kudi…” ko wasu zantuka makamanta wadannan? Sai a biyo mu.

Bangarorin Na’urar ATM

Kafin mu san bangarorin da ke dauke cikin wannan na’ura, zai dace mu san me ye kalmar ATM ke nufi, kuma wasu ayyuka take iya gudanarwa a tsarin cinikayya da kasuwanci.  Da farko dai, kalmar “ATM” haruffa ne guda uku da ke nufin “Automated Teller Machine,” wato na’ura ta musamman da ake iya amfani da ita wajen cira ko sanya kudade tsakanin banki da mai ajiya a bankin.  Bayan cire kudi ko adana su a taskar ajiyar banki da wannan na’ura ke iya taimakawa a yi, har wa yau ana iya amfani da ita wajen duba adadin kudin da mai ajiya ke da su a taskar ajiyarsa ta banki.  Sannan kana iya sayan katin waya (wato Recharge Cards) ta wannan na’ura.  Kana iya biyan kudin wuta (wato Electricity Bill), ta hanyar na’urar ATM.  A wasu kasashe ma kana iya sayan tikitin shiga sinima, da na shiga filin wasan kwallo, duk ta wannan na’ura.  Har wa yau kana iya adana kudinka a cikin taskar ajiyarka (wato Cash Deposit) ba tare da wata matsala ba.  Wannan na’ura ce mai saukin mu’amala saboda tana sarrafa kanta ne, da zarar ka ba ta umarni.

- Adv -

Wannan na’ura dai ta yadu a duniya, musamman kasashen da suka ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa, inda kusan duk ka shiga a birane za ka same ta a girke a wuraren da jama’a ke yawan taruwa, musamman shagunan sayar da kayayyakin masarufi, da gidajen mai, da filayen jirgin sama, da manyan ofisoshi ko hukumomin gwamnati da na masu masu zaman kansu.  Dangane da wanda aka girke ko kafa su, na’urar ATM ta kasu kashi biyu; akwai wadanda bankuna ke kafawa a kofofinsu ko inda ressansu suke a manyan birane. Sai kuma wadanda kamfanoni masu zaman kansu ke kafawa ko girkawa a wuraren taruwan jama’a.  Wannan kashi na biyu sun kebanta ne da wasu kasashe.  Amma a Najeriya bankuna ne kadai ke kafa wadannan ire-iren na’urori a kofar bankunansu ko ressan da suke da su a wasu wurare.

Muhimman Bangarori

Kamar sauran na’urorin sadarwa na zamani, na’urar ATM na dauke ne da manyan bangarori guda biyu. Akwai bangaren ruhi, wato Software, da kuma bangaren gangar  jiki, ko Hardware a turance.  Bangaren ruhi dai ya kasu kashi biyu ne; akwai bangaren masarrafar da ke sarrafa na’urar a yayin da kake amfani da ita.  Wannan bangare na dauke ne da babbar manhajar kwamfuta, wato Operating System. Na’urorin ATM na zamanin da, sun yi amfani ne da babbar manhajar kwamfuta na kamfanin IBM mai suna RMX ko kuma OS/02. Amma saboda ci gaban tsarin manhajar kwamfuta da aka samu a duniya yanzu, kusan galibin na’urorin yanzu suna amfani ne da babbar manhajar kwamfuta na kamfanin Microsoft mai suna Windows XP Professional, da kuma Windows XP Embedded.  Akwai kuma kadan da ke amfani da babbar manhajar Linux har wa yau. Sai nau’in ruhi na biyu mai suna Host Processor.  Wannan ita ce babbar cibiyar gudanarwa da ke hada alaka tsakanin wannan na’ura ta ATM da kwamfutocin bankin da kake ajiya da shi. Hakan na yiwuwa ne ta hanyar tsarin sadarwar tauraron dan adam da ake kira V-Sat.  A zamanin da, wannan babbar cibiyar gudanarwa kan aiwatar da sadarwa ne ta hanyar tarho nau’in Dial-up ko kuma Leased Telephone Lines, kamar yadda ake kiransu a kasashe irin su Amurka da sauransu.

Sai bangaren gangar jiki da shi ma ya kasu zuwa kashi biyu.  Akwai bangaren da ya danganci shigar da bayanai, wato Input Device, wanda ya hada da kafar shigar da kati, wato Card Reader, da maballan shigar da bayanai, wato Keypad – wanda ke hada alaka ta kai-tsaye tsakaninka da babbar cibiyar gudanarwa, wato Host Processor kenan.  A karkashin wannan bangare na shigar da bayanai akwai wata ‘yar karamar masarrafa da ke mayar da kalmomin da ka shigar zuwa kuramen bakake.  Wannan masarrafa ita ake kira Secure Crypto-processor, wacce ke kuramtar da kalmomin zuwa kuramen bakake a tsarin mataki mafi tsauri da ake kira Triple-DES (Triple Data Encryption Standard).  Sai bangare na biyu da ake kira Output Device, wato bangarorin da ke miko maka bayanai – ko na kudin da ka bukata, ko bayanai rubutattu, ko kuma na sauti.  Daga cikinsu akwai lasifika, wato Speaker, da fuskar nuna bayanai, wato Display Screen, da kafar cillo rasit, wato Receipt Printer, sai kafar miko kudade, wato Cash Dispenser. 

Wannan kafa ta Cash Dispenser tana dauke ne da bangarori muhimmai a jikin wannan na’ura ta ATM. Ita ce ke da sinadaran da ke kirgawa tare da tantance nau’ukan kudaden da na’urar ke turowa (misali: ‘yan naira dari-dari ne, ko dari bibbiyu, ko dari biyar-biyar ne na’urar ta turo).  Bayan haka, wannan kafa ta Cash Dispenser ce ke dauke da na’urar kididdige adadin masu mu’amala da wannan na’ura; nawa suka cira? Meye lambar rasitinsu? Yaushe suka cira? Da wani lokaci? A ina na’urar take kafe?  Wannan bayanai da na’urar ke taskancewa a can ciki suke, ba za ka iya isa gare su ba balle ka gani, kuma su ake kira Journal Print Out.  Bayan haka, wannan kafa ta Cash Dispenser tana dauke ne da ‘yar karamar ma’adana da ake kira Reject Bin.  A duk lokacin da ka zo cire kudi, da zarar kafar da ke cillo maka kudin ta fara zakulo su daga inda suke, takan tantance su ne, ta mike su; duk wanda ya lankwashe, sai ta sake shi kasa, haka duk kudin da na bogi ne, wato Counterfeit, duk za ta zubar dasu ta dauko wasu.  Da zarar ta zubar dasu, za su fada cikin wannan ma’ajiya ce mai suna Reject Bin. Wannan ke baiwa bankin damar gane nau’ukan kudaden da ake zubawa, idan tsofaffi sun fi yawa, nan gaba sai a rika samun masu sabunta ana zubawa.  Har wa yau wannan kafa ta Cash Dispenser ce ke dauke da akwatin kudin da na na’urar ke cillowa ga duk wanda ya bukata, wato Cash Vault.  Wannan akwatin a can kasan na’urar take, dukkan sauran bangarorin na samanta ne. Kuma ta bayan na’urar kadai ake iya budewa don tsaro.  Wadannan, a takaice, su ne bangarorin da ke dauke a jikin na’urar ATM.  Abu na gaba da mai karatu zai so ji shi ne yadda wannan na’ura ke aiki a yayin da aka zo cire kudi ko aiwatar da wasu ayyuka makamantansu.  A biyo mu a makon da ke tafe.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA says

    MASHA ALLAH

Leave A Reply

Your email address will not be published.