Facebook Gidan Rudu: “Profile” Mai Cike Da Rudu

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook, a shekarar 2015.

454

“Profile” Mai Cike da Rudu

Daga cikin manyan rudu masu dada rikitar da kwakwalwar mai lura a shafukan Facebook akwai irin tufka da warwara dake makare a bangaren bayanin hakikanin zatin mai shafi, wanda hukumar facebook ta kira da suna: “Profile.

Mafi girman rudun da yafi kowanne fitowa fili a facebook shi ne tufka da warwara na bayanai dake shafin da ya danganci hakikanin bayanan da suka shafi mai shafin. Wadannan bayanai kuwa na “Profile” ne. Daga sunan makarantar da ake bayarwa zuwa nau’in sana’a ko aikin da ake, da abin da ake sha’awa, da wuraren da ake zaune, duk akwai kwamacala a ciki.  Wasu da gangan suke cakuda bayanan saboda shafin ba na Allah-da-Annabi bane, wasu kuma tsabar cakwaliya ce.

Mutum ne zai ce: littafinsa shi ne Kur’ani, Manzonsa shi ne Annabi Muhammad (SAW), Musulunci ne addininsa; zai ma iya mutuwa don kare shi. Haka za ka gani karara a bayyane. Amma a bangaren abin da yake sha’awa ko wadanda suke abin koyi gare shi, sai kaga ya rubuta sunayen wasu gaggan arnan duniya, manyan miyagu wajen manyan sabo, mawakan kasashen yammacin duniya wadanda hatta a kasashensu ma ana Allah-wadai da dabi’unsu.  Su ne abin koyinsa.  Haka idan ka shiga bangaren abokansa (Friends) sai ka ga har da ‘yan luwadi da madigo akwai; ga hotunansu da nau’in sunayensu kana gani.  Wannan tufka da warwara ne.  Ire-iren wadannan bayanai suna nan birjik.

- Adv -

Wani kuma zai ce shi gwauro ne (Single) alhali yana da mata har da ‘ya’ya.  Wata za ta ce tana da aure (Married) alhali tikekiyar tuzura ce.  Duk dai don a boye kai.  Wani kuma a shahararriyar makarantar Rumfa College yayi karatu, amma sai yace “Kaduna Capital School,” wai don ace mahaifinsa mai sukuni ne, ko yace a “Zaria Academy” yayi sakandare.  Akwai ‘yan mata da yawa da  duk a jami’o’in gwamnati suke, amma a Profile sai suce a “ABTI American University” suke, ko “Turkish Nile University,” ko “Baze University”, inda a shekara ake biyan miliyan daya da dubu dari takwas kudin makaranta.

Akwai kuma ‘yan karya, gayu mutanen Allah.  Gidansu watakila a birged yake, amma sai yace suna Maitama, wadda unguwar masu hannu da shuni ce a nan Abuja. Wani yana zaune a Sokoto ne, watakila ko karamar hukumar “Dange/Shuni” bai taba ratsawa ba, amma sai yace a Kano suke, ko a Landan.  Ya dauko hotunan wani gaye dake shanawa a kasar Turai, ya lika a shafinsa, wai duk shi ne.  Ka ji tsagwaron karya.  Wani gayen kuma bai ma da aikin yi, amma saboda son karya zai ce a babban bankin Najeriya yake aiki (CBN), ko a hukumar matatar mai ta kasa (NNPC).  Da zarar ka fara tambayarsa sunayen wasu ma’aikata sai yace maka ai shi sabon ma’aikaci ne, ko yace maka bai cika damuwa da mutane ba balle ya san sunayensu, ko kuma, a karon karshe, yace maka ai babbar ma’aikata ce; kowa harkar gabansa yake yi.

Darasi:

  1. Yin karya wajen bayar da bayanai a Profile kuskure ne mai girman gaske, domin idan hukumar Facebook ta gane nan take za ta rufe maka shafin. Ganewa a wajenta ba abu bane mai wuya; wani karamin sababi ne zai iya zama dalili, sai dai ka ji ka a waje;
  2. Yin karya a Profile zubar da mutumnci ne, musamman idan ya zama ba wani dalili na maslaha ga kanka ko al’umma;
  3. A kasashen da ake lura da shawagin jama’a a kafafen sada zumunta, idan aka gane bayanan da ka bayar a shafinka na Facebook duk karya ce, laifi ne mai zaman kansa, kari a kan laifin da yasa har aka gano hakan;
  4. Ta yiwu kace amma bayyana hakikanin bayanai kuma zai sa rayuwarka cikin hadari. Eh, ta wani bangaren haka ne.  Amma akwai hanyoyin da za ka bi wajen hana kowa ganin bayanan da ka rubuta, daga hukumar Facebook sai kai, sai kuma wanda ka ga dama.  Za ka iya tsara hakan a bangaren “Settings”;
  5. Ta yiwu kuma kace ai idan ka ba ‘abokanka’ misali, daman ganin bayananka a Profile, kila a samu miyagu a cikinsu. Eh, haka na iya faruwa. Amma akwai kariya daga hakan. Kariyar kuwa ita ce, kada ka karbi kowa a matsayin aboki sai wanda ka sani.  Wannan ita ce BABBAR MANUFAR SAMAR DA DANDALIN FACEBOOK HAR ZUWA YAU.  Kenan ashe idan ka ga ka fada cikin hadari da matsala, to, kaine ka jefa kanka.

Jama’a a kiyaye.  Idan kunne ya ji, gangan-jiki ya tsira.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.