Dambarwa: ‘Yan Sa’o’i Kaɗan Bayan Karɓan Ragamar Shugabancin Kamfanin Twitter, Elon Musk Ya Kori Kashi 50 na Ma’aikata, Tare Da Sauya Wasu Tsare-Tsaren Gudanar da Kasuwanci

Shigansa hedikwatan kamfanin ke da wuya, nan take wasu daga cikin manyan ma’aikatan kamfanin suka ajiye aikinsu.  Hakan ya biyo bayan bambancin ra’ayi ne da masu lura da al’amuran Twitter suka ce zai iya aukuwa tsakanin manyan ma’aikatan da Mista Musk. – Jaridar AMINIYA, ranar Jumma’a, 11 ga watan Nuwamba, 2022.

165

A ranar litinin (31/10/2022) da ta gabata ne dai hamshaƙin mai kuɗin duniya, Mista Elon Musk, ya karɓi ragamar shugabancin kamfanin Twitter, bayan saye kamfanin da yayi kan zunzurutun kuɗi dala biliyan arba’in da huɗu ($44bn) a farkon wannan shekara.  Kafin wannan rana, Musk ya yi yunƙurin fasa cinikin sanadiyyar ‘yar saɓani da ta aiku tsakaninsa da masu kamfanin.  Amma da suka yi yunƙurin kai shi kotu, sai ya dawo.  A ƙarshe dai an kammala wannan ciniki, kuma an danƙa masa ragama da mallakin kamfanin gaba ɗaya a ranar litinin da ta gabata.

Shigansa hedikwatan kamfanin ke da wuya, nan take wasu daga cikin manyan ma’aikatan kamfanin suka ajiye aikinsu.  Hakan ya biyo bayan bambancin ra’ayi ne da masu lura da al’amuran Twitter suka ce zai iya aukuwa tsakanin manyan ma’aikatan da Mista Musk.  Bayan ‘yan sa’anni, Elon Musk ya fara aiwatar da sauye-sauyen da ya ƙudurci yinsu.  Kamar yadda ya bayyana a baya, kamfanin Twitter na fama da manyan matsaloli, wanda sanadiyyarsu ne ake ta samun raguwan kuɗaɗen shiga a duk shekara; bayan raguwan masu rajista da shafin ke fuskanta.

Sauye-Sauye

Daga cikin manyan sauye-sauye da ya fara aiwatarwa waɗanda suka ja hankalin duniya, akwai sauya tsarin gudanar da kasuwanci tsakanin kamfanin da masu ta’ammali da tashar ta Twitter.  Da kuma tsarin gudanar da ma’aikata.  Wannan, a cewarsa, zai taimaka wajen samun ƙarin kuɗaɗen shiga.  Ga kaɗan daga cikin sauye-sauyen nan:

Tsarin “Twitter Blue”

Shafin Twitter na ɗauke ne da masu rajista kala biyu; da masu rajistan kyauta gama-gari, da kuma waɗanda suke da rajistar kuɗi.  Na biyun su ake kira: “Twitter Blue”; domin suna da alfarmomi da dama da suke samu waɗanda ba kowa ke samunsu ba.  Daga ciki akwai rashi ko ƙarancin ganin tallace-tallacen da kamfanin ke ɗorawa a shafin.  Kamfanin ya ɓullo da wannan tsari ne a shekarar 2021.  A tare da cewa kuɗi suke biya, Musk yace adadin kuɗaɗen shiga da ake samu daga wannan tsari yana raguwa ne, ba ƙaruwa ba.  Don haka yace zai yi wa tsarin garambawul ta yadda adadin masu rajistan zai ƙaru don ƙaruwar kuɗaɗen shiga.  Yace fatansa shi ne zuwa shekara ta 2028, tsarin zai riƙa samar wa kamfanin dala biliyan 10 ($10bn).

Masu Shuɗin Maki (Blue Tick)

- Adv -

A shekarar 2009 kamfanin Twitter ya samar da tsarin tantance mutane ko kamfanoni, sanadiyyar yaɗuwar shafukan bogi da suka yawaita.  Wannan tsari mai suna: “Twitter Verification”, yana amfani da ingancin bayanan da ka bayar ne lokacin da rajista, da adireshinka, da yawaitan hawa shafin Twitter.  Da zarar tsarin ya gamsu da kai, zai liƙa maka shuɗin maki a kan sunanka.  Wannan shi ake kira: “Blue Tick”, kuma kyauta ake bai wa mutane.  Amfaninsa shi ne bai wa mutane da kamfanoni natsuwa cewa duk wanda ke ɗauke da wannan tambari ko maki, lallai ingantacce ne ba shafi bane na bogi.  A taƙaice dai, kamar yadda yake a shafin Facebook da Instagram da LinkedIn da Tiktok, masu wannan maki suna da matsayi a idon mutane – kusan dukkan shugabannin ƙasashe, da manyan hukumomin gwamnatoci, da shahararrun ‘yan jarida, da ‘yan siyasa, da zakarun wasanni da sauransu, an basu wannan maki.  Ya zuwa makon jiya dai akwai mutane 423,000 dake da wannan maki.  Kuma samuwarsu na ƙara wa shafin Twitter karɓuwa ne a idon kamfanoni masu ɗora tallace-tallacensu a shafin.

To amma da zuwan Mista Musk, yace wannan tsari na tantancewa zai koma na kuɗi.  A ranar litinin yace daga yanzu duk wanda shafinsa ke ɗauke da shuɗin maki (blue tick), zai riƙa biyan dala 20 ($20) a duk wata (kusan N15,000 kenan).  Nan take aka fara cece-kuce.  Gari na wayewa (ranar talata) sai ya sassauta; yace za su riƙa biyan dala 8 ($8) (kusan N6,000 kenan) duk wata.  Yace wannan zai taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga ga kamfanin, musamman don rage tarin basussukan da kamfanin zai riƙa biya.  A ɗaya ɓangaren kuma yace za a basu damar ɗora bidiyo da sauti masu dogon zango, sannan za su ga ƙarancin tallace-tallace a shafukansu.  Ƙari kan haka, za a bai wa saƙonninsu mahimmanci wajen ta’aliƙi, kuma duk wanda ya ambacesu a sahar nan take za a sanar dasu.

Sallamar Ma’aikata

Tsakanin ranar laraba da alhamis Musk ya fara sallamar ma’aikata ta hanyar saƙonnin Imel.  Da farko dai an yanke musu hanyar sadarwa ne tsakaninsu da kamfanin.  Inda da yawa cikinsu suka kasa amfani da manhajojin da suke aiki dasu na kamfanin.  Bayan ɗan lokaci kaɗan aka buɗe su, sannan aka sanar da waɗanda abin ya shafa da kada su zo aiki.  Sai kuma saƙonnin sallama suka fara biyo baya.  Wasu an sallame su ta hanyar aika musu saƙo cikin mutunci, kamar yadda ya kamata a tsarin aiki.  Wasu kuma ta hanyar shguɓe aka sallame su.  Akwai wanda ma ta hanyar emoji da aka sallame shi.  Wasu kuma ma har yanzu basu san matsayinsu ba.  A taƙaice dai, zuwa yammacin Jumma’a da washegarin Asabar, Musk ya sallami kusan ma’aikata dubu huɗu (4,000) dake warwatse a ofisoshin kamfanin a ƙasashen duniya daban-daban.  Wannan shi ne adadi mafi girma na kora da aka yi a wani kamfani na sadarwa a cikin ‘yan lokutan nan.  Bayan haka, shi ne kuma ke ɗauke da hanyar kora mafi muni da aka yi wa ma’aikata.

Dalilansa

Waɗannan sauye-sauye sun tayar da ƙura matuƙa.  Tashar Al-Arabiyya ta ruwaito yadda ma’aikatan kamfanin Twitter suka harzuƙa har suka rufe ofishin kamfanin a yammacin Jumma’ar da ta gabata.  Haka ma masana masu sharhi a fannin sadarwa na zamani sunyi sharhi kan waɗannan sauye-sauye.  Ra’ayinsu duk iri ɗaya ne; an zafafa sosai, kuma hakan bazai haifar da ɗa mai ido ba.  Wasu ma na ganin hakan na iya ɗurƙusar da kamfanin gaba ɗaya.  Domin matsalolin da kamfanin ke fuskanta sun ƙarfinsa.  Ga bashin dala biliyan 13 ($13bn) da Musk yaci don yin cikon kuɗin sayan kamfanin.  Wannan adadin kuɗi na buƙatar dala biliyan 1 ($1bn) na kuɗin ruwa (Interest) a duk shekara wajen biyan uwar kuɗin.  Bayan haka, sayan kamfanin ya sauya masa matsayi daga kamfanin jama’a zuwa kamfanin mutum ɗaya.  Abin da wannan ke nufi shi ne, Musk ne zai biya duk wani ma’aikacin Twitter mai riƙe da hannun jarin kamfanin.  Dole ne kuma wannan kuɗin ya fito daga hada-hadar da kamfanin keyi, wanda abu ne mai wuya a halin da ake ciki yanzu.

A nashi ɓangare, Elon Musk yace dole ne ya aiwatar da waɗannan sauye-sauye saboda halin ƙarancin kuɗi da kamfanin yake ciki.  Yace a duk yini kamfanin Twitter na hasarar dala miliyan 4 ($4mil) – kwatankwacin kusan naira biliyan uku kenan.  Dangane da sallamar ma’aikata kuma yace wannan dole ne, saboda kamfanin ya rage adadin kuɗaɗen da yake kashewa wajen tafiyar dashi.  Yace bayan waɗannan sauye-sauye ma, akwai da yawa dake tafe.

Tsawon zamani dai shi zai tabbatar da dacewa ko rashin dacewar waɗannan sababbin hanyoyin kasuwanci da Mista Elon Musk ke aiwatarwa a halin yanzu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.