Hanyoyin da Kafafen Sadarwa Na Zamani Ke Bi Wajen Kayyade Masu Amfani Da Shafukansu

Daga cikin hanyoyin samar da tsari akwai shardanta yin rajista, wanda ya kunshi bayar da bayanai irin: suna, da adireshi, da lambar waya ko adireshin Imel, da sana’a ko aikin yi, da tarihin karatu da aiki, da kuma adadin shekaru.  Galibi idan shekarunka suka gaza goma sha uku ma ba za ka iya rajista ba. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 29 ga watan Yuli, 2022.

686

A Nasu Bangaren…

Ta yiwu wasu su ga kamar wadannan kamfanoni na sadarwa ba sa yin komai wajen kawo karshen wadannan illoli dake yaduwa a shafukansu.  Watakila, mai karatu ya iya riya cewa, shi yasa hukumomi ke son yin hakan.  Ba haka lamarin yake ba.  A babin adalci, wadannan kamfanoni su ne a sahun gaba wajen samar da hanyoyi da tsare-tsaren da zasu rage samuwa da yaduwar wadannan illoli da cutarwa ga jama’a ko al’umma baki daya.  A kan wannan maudu’i ne makalarmu ta wannan mako za ta yi sharhi.

Tsarin Rajista

Daga cikin hanyoyin samar da tsari akwai shardanta yin rajista, wanda ya kunshi bayar da bayanai irin: suna, da adireshi, da lambar waya ko adireshin Imel, da sana’a ko aikin yi, da tarihin karatu da aiki, da kuma adadin shekaru.  Galibi idan shekarunka suka gaza goma sha uku ma ba za ka iya rajista ba.  Wadannan bayanai su ne asali wajen samar da tsari.  Duk abin da ka aikata mai kyau ko mara kyau, ta hanyarsu za a iya bibiyarka.

Ka’idojin Ma’amala

A yayin da kake rajista, kafin ka gama a baka shafi ko damar hawa shafinka, sai ka amince wa ka’idojin ma’amala da kamfanin ke son ka tsare yayin da kake amfani da shafi ko kafarsa ta sadarwa.  Wadannan manyan sharudda dai guda hudu ne. Haka abin yake a kowace kafar sadarwa.

Sharadi na daya shi ne, dole ka amince cewa ba za ka yada ko taimaka wajen yada sakonnin dake kunshe da cutarwa ga lafiya da rayuwar wasu ba, a ko ina suke.  Wato duk wani sako da zai iya sa a kashe wani, ko a cutar da lafiyarsa, dole ne ka kame da kirkira, ko yadawa, ko taimakawa wajen yada shi.  Sharadi na biyu, dole ne ka kame daga kirkira ko yadawa, ko taimakawa wajen yada sakonnin dake dauke da tsana ko batanci ga wani jinsin dan adam, ko wata al’umma, ko nuna wariyar launin farta, ko bambancin al’ada da fahimta ko mahangar rayuwa.  Sharadi na uku, dole ne ka kame daga kirkira, ko yadawa, ko taimakawa wajen yada duk wani sako dake dauke da tsagwaron batsa; hotuna ne, ko rubutu ne, ko bidiyo ne, ko sauti ne.  Sai sharadi na karshe, dole ne ka kame daga kirkira, ko yawada, ko taimakawa wajen yada sakonnin karya ko na bogi, masu dauke da yaudara wanda kuma hakan zai taimaka wajen salwantar dukiyar jama’a.  A takaice dai, wadannan dokoki ko ka’idoji na dauke ne da hanyoyin kariya ga rayuwa, da lafiya, da mutunci, da dukiya da kuma addini.

Hanyoyin Tantance Bayanan Jama’a

Bayan wadannan ka’idoji da dole ne sai ka amince musu sannan za a baka damar mallakar shafi da dora bayanai, wadannan kafafe na sadarwa sun samar da tsare-tsare a yanayin manhajoji dake taimaka musu wajen tantance bayanan da mutane ke dorawa a shafukansu.  Ta wadannan hanyoyi suke iya gane wanda ke bin ka’ida da wanda ba ya bin ka’idojinsu.  Sannan, ga duk wanda ya saba musu, akwai tsare-tsare da suka sa wadanda ke cire su, ko toshe shafinsu na wucin-gadi, ko hana su yin tsokaci a sakonnin wasu (kamar yadda Facebook ke yi a halin yanzu), da dai sauran matakai.  Bayan wadannan manhajoji, suna tanadar ma’aikata dake tantance bayanan wadanda aka rufe shafukansu.  Kamfanin Meta, mai mallakin Dandalin Facebook, misali, yana da ma’aikata a kalla dubu goma sha biyar (15,000) da ya dauka, masu aikin nazarin bayanan jama’ar da aka rufe shafukansu ko suka aiko koke da dai saurnasu.

- Adv -

Sakonnin da Suke Saukewa Dag Shafukansu

A babin misali, zai dace mai karatu yaga adadi da nau’ukan bayanan da wadannan kafafe ke hakilon cirewa ko saukewa, wadanda suka saba wa ka’idojinsu, ko suka saba dokar kasashensu kuma aka kawo koke.  Zan kawo misalai daga kafafe uku ne kacal, saboda karancin lokaci da mahalli.  Wadannan bayanai sun kunshi na watannin shekarar 2020 ne, sadda ake killace lokacin cutar Covid-19.

Dandalin Facebook

Kamar yadda na sanar a sama, a Dandalin Facebook kadai, akwai ma’aikata sama da dubu goma shabiyar (15,000) da ke aikin tantance korafe-korafen jama’a.  A shekarar 2020 shafin ya goge sakonnin bogi guda biliyan uku da miliyan dari uku (3.3 billion).  Da sakonnin batsa (rubutu, ko hotuna, ko sauti), sama da miliyan saba’in da biyar (75 million).  Sai sakonni masu dauke da tayar da fitina, ko hatsaniya, ko kisa guda miliyan arba’in (40 million).  Daga cikin sakonnin da suka goge ko sauke, akwai sakonni masu dauke da tsana ga wani jinsi ko al’umma.  An goge miliyan talatin da biyu (32 million).  Sai sakonnin batsa da yaudaran kananan yara.  Su kuma an goge miliyan goma sha takwas (18 million).  Sai kuma wasu nau’ukan bayanai munana daban, an goge miliyan arba’in da bakwai (47 million).

Youtube

A bangaren shafin bidiyo na Youtube kuma, shafin ya goge sakonnin bogi guda miliyan biyar da rabi (5.5 million).  Sai sakonnin da suka shafi rudin kananan yara don batsa dasu, guda miliyan biyar da dubu dari uku (5.3 million).  Da sakonnin bidiyo masu dauke da tayar da fitina ko haddasa kisa, guda miliyan daya da dubu dari tara (1.9 million).  Sai sakonnin bidiyo masu dauke da tsagwaron batsa, guda miliyan biyu da rabi.  Akwai bidiyo masu dauke da bayanan tsana da tsattaurar ra’ayi, guda miliyan daya da dubu dari biyu (1.2 million).  Sai kuma sauran bayanai munana da suka shafi wasu bangarori daban, guda miiyan daya da dubu dari daya.

Twitter

A bangaren shafin Twitter kuma, cikin shekarar 2020 dai har wa yau, kasancewar shi ne shafi mafi karancin masu rajista idan an kwatanta shi da sauran, ya goge sakonnin tsana guda dubu dari tara da hamsin da biyar (955,000).  Sai sakonnin cin mutunci da tayar da hatsaniya, guda dubu dari shida da dubu daya (601,000).  Sai kuma sakonni masu motsa rai, guda dubu dari da saba’in da daya (171,000).  Da sakonni masu dauke da hanyoyin yada kisa ko kururuta shi, an goge guda dubu saba’in da hudu (74,000).  Sai sakonni masu dauke da bayanan sirrin mutane, guda dubu talatin da takwas.  Sauran bayanan da suka shafi wasu nau’ukan laifukan kuma an goge guda dubu tamanin da bakwai.

A takaice, wannan kadan ne daga cikin yunkurin da wadannan kafafe na sadarwa ke yi wajen dakile illoli da matsalolin da ke yaduwa a shafukansu.  A makon gobe in Allah Ya so, za mu Karkare bayani kan hanyoyin da za a inganta wannan sabuwar doka da hukumar NITDA ta ke kokarin fitarwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.