Alakar Intanet da Harkokin Rayuwa (1)

Fasahar Intanet wata duniya ce da mutane ke gudanar da rayuwarsu kwatankwacin rayuwar da suke gudanarwa a rayuwa ta zahiri. A wannan kasida zamu dubi alakar dake tsakanin nau’ukan rayuwan biyu, ta la’akari da mahallinsu.

192

Mabudin Kunnuwa

Ga wadanda suka ziyarci wannan shafi a makon da ya gabata, sun karanta irin ci gaba da yaren Hausawa ya samu wajen shigar dashi cikin sabon babban manhajan kwamfuta da kamfanin Microsoft ke son fitarwa nan ba da dadewa ba, watau Microsoft Vista Office. Wannan ba karamin ci gaba bane da wannan harshe ya samu. Kuma wannan ke dada nuna ma mai karatau cewa nan ba da dadewa ba, Intanet zai fara shafan rayuwar Hausawa, tun da hakan na daya daga cikin muhimman dirkokin da ake bukata wajen hakan, kamar yadda bayanai suka gabata a kasidun baya. Ina taya mu murnan samuwan wannan al’amari. Wannan zai dada kara yawan kwamfuta a cikin al’umma, wanda zai sa mutane su kara sha’awan fasahar Intanet.

Daga karshe, yanda muke ta jin labarin tsarin kasuwanci ta hanyar Intanet a wasu kasashen duniya, za mu wayi gari ana damawa damu ta wannan fanni. Kafin nan, zan so in sanar da mu cewa a halin yanzu akwai wasu hanyoyi da za mu iya aiwatar da harkokin rayuwa na abin da ya shafi shiga makarantu, hulda da bankuna, neman aiki, zuba jari, kafin mu kai matakin aiwatar da saye da sayarwa ta Intanet, a Nijeriya. Wannan shi ne tsarin da a turance ake kira e-commerce a dunkule. Wannan makon za mu yi tsokaci kan matakan da mai karatu zai bi wajen yin hakan, da hanyoyin da zai kare kansa, wajen aiwatar da wadannan harkoki, sai mu karkare da kawo misalai daga wasu gidajen yanan sadarwa da ke nan Nijeriya, a makonnin da zasu biyo baya.

Harkokin Rayuwa a Intanet

Na tabbata mai karatu ya karanta cewa gidan yanan sadarwa (Websites) na daga cikin hanyoyi mafi sauki wajen tallata hajoji da ra’ayoyi da sauransu. A yau kusan duk abin da kake tunanin ana sayar da shi, ko da hidima ne (service) wanda wani zai maka ka biya shi, za ka tarar ya gina gidan yanan sadarwa, don tallata wannan sana’a nashi. Wannan ruwan dare ne a kasashen turai. Amma a kasashe masu tasowa irin kasashen Afirka, Asiya da wani bangaren Latin Amurka, sai daidai za ka samu suna da iirn wannan tsari. Sai dai hakan na wucin gadi ne, wannan tsari zai mamaye duniya gaba dayanta, ko ana so ko ba a so. Wannan tasa dole dan Adam ya zama yana tafiya da zamani, ta fannin abin da ya shafi ci gabansa da al’umman da yake rayuwa cikinta. Duk da yake a yanzu muna aiwatar da harkoki ne a fili, ga-ka-ga-abokin hulda, nan gaba matakin rayuwa zai zama galibin harkoki basu yiwuwa ta dadi sai an kai ga Intanet. Shiga makaranta sai da Intanet. Hulda da banki wajen ajiya ko canjin kudaden kasashen waje, sai da Intanet. Zuba jari sai da Intanet. Neman aiki sai ka iya kwamfuta, don ta Intanet za ka aika da duk abin da ake bukata daga gareka. Harkan ajiyan Fansho sai da Intanet. Wadannan harkoki ne na rayuwa wanda mai karatu ba ya iya rayuwa sai yayi a kalla daya daga cikinsu. Duk da yake kafin nan, al’umma ita kanta zata sadaukar da kanta ne ga tsarin da zamanin ya kawo. Don haka mallakan makami kafin zuwan yaki ba ya nufin kana fatan zuwan yaki ne, sam. Sai don kare kai da kuma gudanar da ingantacciyar rayuwa a fuskar da take gudanuwa. Don haka akwai matakai a kalla hudu daga bangaren masu kamfanoni ko hukuma, da kuma bangaren mai mu’amala da su, irinsu ni da kai kenan, mai karatu.

Matakai

Aiwatar da harkokin rayuwa ta Intanet, musamman abin da ya shafi saye da sayarwa, na bukatar abubuwa da dama. Duk kamfani ko hukumar da ke son aiwatar da hakan, dole ne ta bi su. Abu na farko, wanda yafi komai muhimmanci shi ne samar da kankararren gidan yanan sadarwa mai dauke da hanyoyin mu’amala da abokin hulda mafi sauki. Galibin ire-iren wadannan gidajen yanan sadarwan za ka samu suna da manhajar wasikar hanyar sadarwa mai zaman kansa, wanda ke hade da rumbun adana bayanansu (Database). Duk mai hulda dasu zai samu adireshin Imel da kuma kalman iznin shiga wanda babu mai irinsa. Ta wannan hanya ne kadai za a riƙa shaida abokin hulda da zarar ya shigo ko aiko da bayan da ake bukata ya aiko. A wasu lokuta kuma katin biya (scratch card) za ka saya, misali wajen biyan kudin makarata. Da ka shigo gidan yanan sadarwan, za ka samu inda aka tanada maka don shigar da kalmin da ke kunshe cikin katin. Dukkan wadannan bayanai da za ka aika, suna zuwa ne kai tsaye cikin uwar garken gidan yanan.

- Adv -

Hanya ta biyu kuma it ace samar da cikakken bayani kan haja ko tsarin da ake son mai mu’amala ya bi. Idan haja ce, nawa ake sayarwa, kuma ta yaya mai saya zai samu riskuwa da abin da ya saya? Da dai sauran bayanai. Misali, dole ne a tanada ma mai mu’amala hanyoyin da zai bi wajen shigar da bayanai da nau’in bayanan da ake so ya shigar. Wannan zai taimaka masa wajen aiwatar da abin da ake so, ba tare da matsala ba. Idan banki ne, a taimaka maka da bayanai kan yadda za ka shigar da nambobin ajiyarka da sauran bayanai. Idan makaranta ce, a tanada maka bayanai kan yadda za ka cika fam, da irin bayanan da za ka bayar, da kuma lokacin da za ka samu sakamakon abin da kake nema da sauransu.

Hanya ta uku kuma ita ce tsare sirrin abokin hulda, watau Privacy, a turance. Galibin gidajen yanan sadarwa a turai, sukan sayar da bayanan abokan huldansu, wanda suka tara sanadiyyar saye da sayarwa da suka gudanar a gidan yanansu. Wannan ta tilasta ma hukumomin wadannan kasashe tsara doka wanda ya zama dole a tsare ma masu mu’amala bayanansu. Mataki na karshe kuma shi ne tanada ma masu mu’amala sashin taimako, watau Help Section. Wannan zai taimaka ma mai mu’amala samun warware lalular da ya shiga wajen mika bayanai ko aiwatar da huldodinsa a gidan yanan sadarwan. Wadannan a takaice su ne matakan da duk wani kamfani mai mu’amala da kwamstomomi ta hanyar Intanet ke bukatar tabbatar dasu, don samun dorewa da amincewan abokin mu’amala.

A bangaren mai saye ko kuma mu’amala, yana bukatar matakai hudu shi ma, don samun saukin mu’amala wajen gabatar da harkokinsa. Na farko, ya tabbata cewa adireshin gidan yanan sadarwan da ka samu ingantacce ne, ban a bogi ba. Domin akwai wadanda suka shahara wajen tsara gidajen yanan sadarwan kamfanoni, musamman wadanda suka shahara a duniya wajen kasuwanci da hulda da jama’a, don kautar da masu hulda da kuma sace masu bayanan katin adashin bankinsu. Idan ba tsananin lura kayi ba, ba za ka gane banbancin da ke tsakanin adireshinsu da na asalin kamfanin ba. Idan ka shiga gidan yanan sadarwan kuwa, wayyo, ba wani banbanci. Don haka, ka samu ingantaccen adireshi. Idan banki ne, ka tabbata cewa adireshin daga bankin ka samu, ko kuma a jarida ka gani wanda su suka buga. Idan jami’ah ce, ka tabbata adireshin da ke jikin fam din ka yi amfani dashi. Idan ba haka ba, sai a sha ka misilla. Mataki na biyu, da zarar ka samu kanka a cikin gidan yanan sadarwan, sai ka natsu, ka karanta bayanan da ke da munasaba da abin da kaje yi. Ka tuna cewa, da zarar ka aika fa shi kenan.

Ka kuma tabbata cewa bayanin da ake so ka bayar. Wasu jami’o’in suna da gidajen yanan sadarwa iri biyu ne, misali Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, gidan yanan sadarwa biyu suke dashi. Akwai wanda suka tanada musamman don dalibai masu yin rajista, akwai kuma na hukumar makaranta. Idan ka shiga na hukumar makaranta, zai kai ka inda za ka yi rajista, amma sai ka lura da bayanan da ke ciki, idan ba haka ba, sai ka bace. Mataki na uku shi ne ka lura da sashin taimako, watau Help ko kuma FAQs (Frequently Asked Questions). Wannan shi ne inda za ka dosa da zarar ka samu matsala. Mataki na karshe shi ne tsare bayananka. Duk da yake wannan ba ya cikin huruminka, za ka iya tabbatar da cewa bayanan da ka aika (nambobin ajiyanka, namban katin biya, kalmomin izinin shiga dsr) a tsare suke ko ba a tsare ba. Idan kana son gane haka, duk lokacin da ka shigar da ire-iren wadannan kalmomi, ka matsa “enter” ko “go”, ka lura da adireshin da ke “address bar”, za ka ga harafin “s” a gaban “http” da ke bayyana a farkon dukkan adireshin gidan yanan sadarwan. Maimakon ka ga http:// za ka ga https://. Idan ka ga haka, to bayananka sun shiga inda ake kira “secured location” kenan, ba matsala.

Wadannan, a takaice su ne matakan da ake bukata a dukkan bangarorin biyu. A mako mai zuwa in Allah Ya yarda, za mu ci gaba da kawo bayanai kan tsarin saye da sayarwa da kuma gabatar da harkokin rayuwa ta hanyar Intanet. Daga karshe, ina mika godiyata da dukkan wadanda suka rubuto ko bugo waya ko yi addu’a a boye ga mahaifiyata. Allah Ya saka muku da alheri, Ya kuma sa Aljannah ce makomar mu gaba daya, amin. Na gode, Allah bar zumunci.

Sanarwa

Ina farin cikin sanar da masu karatu cewa na bude kundin sirri (Blog) ko mudawwana ta Intanet, inda nake zuba dukkan kasidun da aka buga a wannan shafi, da takaitattun labarai kan hanyoyin fasahar sadarwa. Kowa na iya ziyartan wannan kundin sirri nawa. Dalilin yin hakan shi ne don samun wurin ziyara. Ga adireshin nan kamar haka: http://fasahar-intanet.blogspot.com. Idan kana son yin sharhi kan bayanan da ke cikin kundin, sai ka matsa inda aka rubuta “comments” a kasan kowane kasida. Amma dole ya zama kana da Gmail. Har wa yau, akwai rariyar likau zuwa muhimman zaurorin hira da majalisun tattaunawa. Sai mun sadu a can!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.