Sakonnin Masu Karatu (2013) (4)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

127

Baban sadik barka da bincike.  Shin, da gaske ne wai bakan gizo yana shanye ruwa?  Don na ji mutane suna cewa yana shanye ruwa idan hadari ya taso, kuma ana samunsa ne a tsohon rijiya.  Meye gaskiyar wannan lamari?  – Ali Fancy, Garko, Kano: 08068418409

Samuwar “Bakan Gizo” da Tsarinsa  a Kimiyyance

Yanayin bakan gizo na cikin abubuwan da dan Adam ke iya ganinsu a muhallinsa shekaru masu tsawo da suka gabata, amma kuma saboda rashin kudura irin ta binciken kimiyya, ya kasa gano hakikaninsa.  Don haka ma ra’ayoyi suka sassaba tsakanin al’ummomin da ke duniya kan asali da kuma tasirin wannan yanayi na bakan gizo.  Daga ina yake samuwa, me ke haddasa samuwarsa, kuma shin, yana da wata tasiri ta musamman ne akan rayuwar mutane?  Wadannan tambayoyi suna da muhimmanci sosai muddin ana son fahimtar wannan yanayi na bakan gizo da tasirinsa.

Sai dai kuma inda matsalar take ita ce, duk wanda ka tambaya cikin al’ummomin duniya, zai baka amsa wacce ta sha bamban da irin wacce wasu al’ummomin ko al’ummar da ka tashi ciki za su baka ne.  Misali, mu a kasar Hausa idan aka ga wannan yanayi na bakan gizo ko gajimare, abin da ake riyawa shi ne, ba za a samu ruwan sama ba, domin shi ne wanda ke janye rowan, kamar yadda mai tambaya ya fada a sama.  Hausawa sun yi imani da hakan ne musamman ganin cewa sai lokacin da hadari ya hadu sannan wannan yanayi na bakan gizo ke bayyana.  Idan kuma ya bayyana, to a galibin lokuta, da kyar ake yin ruwan.  Idan muka koma kan wasu al’ummomin kuma za mu ji wani camfin da ya sha bamban da namu.

Misali, a al’ummar Girka (Greek), bakan gizo wata hanya ce da wani manzo mai suna Iris ke bi wajen isar da sako tsakanin sama da kasa.  Su kuma mutanen kasar Sin (China) ra’ayinsu ya sha bamban da na al’ummar Girka.  Suka ce allarsu mai suna Nuwa ce ke amfani da wannan yanayi na gajimare, don toshe wata kafa da ke samuwa a sama, ta hanyar amfani da wasu duwatsu guda biyar masu launuka daban-daban.  Idan muka shiga kasar Indiya, su kuma ra’ayinsu ya sha bamban.  A nasu camfi, suna kiran gajimare ne da suna Indradhanush, ma’ana “Bakar Indra”.  Shi Indra wani allan mutanen Hindu ne, wanda suka yi imanin yana da tasiri kan ruwan sama, da cida, da kuma walkiya.  Wata ruwayar kuma ta ce yanayin gajimare ita ce bakar allan Hindu mai suna Kama.  Shi yasa suke kiran gajimare da suna Kamanabillu. 

Idan muka koma Jaziratul Arab kuma, ta su fahimtar ba daya take da ta mutanen Hindu ba.  A wajen Larabawa (lokacin Jahiliyya), sun yi imani cewa gajimare shi ne bakan wani gunkinsu mai suna Quzah ko kuma ‘Uzzah.  Don haka suke kiran gajimare da suna Qausu Quzah, wato “Bakar Quzah”.  Abin bai tsaya kan camfin kabilu maguzawa kadai ba, hatta a cikin littafin mabiya addinin Kiristanci suna ganin akwai wani tasiri mai karfi da wannan yanayi na bakan gizo ke haddasawa.  A wajen Kiristoci, kamar yadda yake cikin littafin Farawa (Genesis), sura ta 9, aya ta 13 – 17, suka ce bayyanar gajimare  alama ce da ke nuna alkawarin Allah a wannan duniya, cewa ba zai kara aiko da irin bala’in da ya samu mutane a lokacin Ambaliyar Dufana ba.

A takaice dai, addinin Musulunci ne kadai (a iya sani na da bincike na) bai bayyana cewa wannan yanayi yana da wani tasiri na musamman ba ga rayuwar dan Adam.  Illa dai ma iya daukansa a matsayin wata alama ce har wa yau, da ke nuna tsarin da wannan duniya ke gudanuwa a ciki, da kuma cewa lallai akwai wanda ke tafiyar da duniyar – wato Allah Madaukakin Sarki kenan.  To amma a kimiyyance, me Malaman Kimiyya suka ce dangane da wannan yanayi na bakan gizo ko gajimare?

Gajimare, a Mahangar Kimiyya

Gajimare, ko Rainbow a harshen Turanci, wani irin yanayi ne da ake iya gani a sama mai kama da baka, wanda ya kunshi ayarin launuka guda bakwai da ke samuwa a duk lokacin da rana ta cillo haskenta a kan danshin ruwa ko yayyafi ko rabar da ke sarkafe a girgijen da ke sararin samaniyar wannan duniya tamu.   Wannan yanayi na dauke ne da wadannan launuka a sifar baka, wato rabin da’ira ko kuri kenan (Semicircle ko Arc a Turance) daga sama zuwa kasa.  Launin da ke sama daga waje, shi ne ja.  Sai kuma launin Violet da kasa, daga ciki.

- Adv -

Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, wadannan launuka na samuwa ne sanadiyyar hasken rana da ke bugowa a saman giragizai masu dauke da danshin ruwa ko yayyafi.  Akwai launuka daban-daban da suke bayyana a lokuta daban-daban.  Amma wadanda suka fi shahara su ne wadanda bayanai suka gabata a baya a kansu (wato Red, Orange, Yellow, Green, Blue, Indigo and Violet – ROYGBIV ake kiransu a ramzance).  Daga cikin wadannan launuka, launukan asali su ne Red (Ja), da Blue (Shudi), da Green (Kore), da kuma Yellow.  Amma sauran launukan duk hadaka ne daga wadannan hudun.

Har wa yau, wani abin da galibin mutane basu sani shi ne, wannan yanayi na gajimare na iya samuwa a saman teku, muddin aka samu irin yanayin da ke haddasa samuwarsa a sama. Wadannan abubuwa kuwa su ne samuwar danshi a cikin giragizai, ko watsuwar ruwa a sama, ko samuwar raba a cikin giragizai, a daidai lokacin da hasken rana ke ratsawa ta cikinsu daga baya, gab da lokacin faduwarta.  Lokacin da wannan yanayi na gajimare ke bayyana har launukan su bayyana radau-radau shi ne lokacin da duhu ya bayyana a rabin sama sanadiyyar hadari, ga giragizai na zubar da ruwa ko yayyafi, kai kuma kana tsaye a daidai wurin da haske ya bayyana, kana fuskantar hasken rana.  Za ka ga gajimare rau-rau, yana fuskantar wannan bangare na duniya ko sama, daidai inda duhun nan ya bayyana sanadiyyar hadari.

Har wa yau, gajimare na iya bayyana cikin dare, lokacin da wata ke kyalli, muddin aka samu irin yanayin da ke iya haddasa shi.  Sai dai kuma, sabanin lokacin yini, ba za a ga wadannan launuka rau-rau ba, domin a ka’ida, idanun dan Adam ba su iya riskar launi a lokaci ko yanayin da duhu ya kwaranye muhallin da suke ciki.  A irin wannan yanayi, sai dai a ga farin haske ya bayyana daidai inda gajimaren yake.

Binciken Malaman Kimiyya kan Gajimare

Binciken Malaman Kimiyya kan samuwar gajimare da tasirinsa, tun daga babban Malamin Musulunci Ibnul Haitham, har zuwa kan Gustav Mie (1908), babu wanda ke tabbatar da daya cikin dukkan camfe-camfen da al’ummomin da suka gabata suka yi dangane da gajimare.  Har wa yau, babu wanda ya nuna cewa akwai alaka tsakanin wannan yanayi da kame ruwan sama, ko zuke shi, ko hana shi zuba, sabanin yadda al’ummar Hausawa suke riyawa.  Da a ce akwai alaka, to da an gano hakan a kimiyyance tun tsawon wannan lokaci.

Wanda ya fara bincike kan wannan yanayi na gajimare dai shi ne Al-Imam Ibnul Haitham, daya cikin manyan Malaman Musulunci da ke bincike kan kimiyya da kere-kere a Daular Farisa (Persia).  Wannan malami ya yi fice sosai kan fannin kimiyya musamman bangaren Fiziya da Sararin Samaniya.  A cikin littafinsa mai suna “Maqaalah fil Haala wa Qaus Quzah”, wanda littafi ne da ya rubuta musamman kan wannan yanayi na gajimare, ya mike kafa sosai wajen bayani kan wannan yanayi.  A cikin littafin ya yi kokarin gano yadda wannan yanayi ne ke samuwa, kuma kamar yadda bayanai suka gabata, shi ne wanda ya fara bincike a wannan fanni.  Wannan malami yayi rayuwa ne shekaru dari tara da suka wuce.

Daga nan sai Ibn Sina, daya cikin manyan malaman Falsafa da Likitanci, ya kama tafarkinsa.  Duk da cewa sun yi zamani daya ne da Ibnul Haitham, Ibn Sina ya riga shi rasuwa.  Bayan Ibn Sina kuma sai wani babban malami dan kasar Sin mai suna Shen Kuo da ya zo a bayansu.  Shi ma ya taba nasa binciken ya tafi. Bayan Shen Kuo, sai ga wani malamin Musulunci dan Daular Farisa mai suna Qutubud Deen Al-Shiraazi wanda ya rasu shekaru dari shida da suka gabata.  Da ya tafi, sai wani almajirinsa mai suna Kamalud Deen al-Farisi yayi nazarin littafin Ibnul Haitham mai suna Kitabul Manaazir, ya kuma gabatar da nasa binciken shi ma kan wannan yanayi na gajimare.

Da tafiya tayi nisa, sai aka sake samun wani cikin malaman kasar Turai mai suna Robert Bacon, shi ma yayi bincike mai fadi kan wannan yanayi.  A daidai wannan lokaci ne aka fassara wani littafin Ibnul Haitham mai suna Kitaabul Manaazir, wanda Robert Bacon yayi nazari mai zurfi a kansa.  Daga nan kuma sai ga Rene Descartes da littafinsa mai suna Discourse on Method, duk a kan wannan yanayi na gajimare.  Da shekaru suka kara nisa sai ga Isaac Newton, wanda ya haddade iya launukan da ke jikin gajimare da cewa guda bakwai ne, kuma ya sanar da sunayen wadanda suka fi shahara ko bayyanuwa daga cikinsu, kamar yadda muka sanar a sama.

Bayan Isaac Newton sai Thomas Young, shi ma yayi bincike kan wannan yanayi na gajimare.  Da ya wuce kuma sai ga George Biddell Airy, wanda ya gano cewa, kaifin launukan da ke jikin gajimare ya danganta ne da girman digon ruwa ko hazo ko danshin da ke jikin giragizai.  Mutum na karshe da ake tinkaho da sakamakon bincikensa a halin yanzu shi ne Gustav Mie, wanda ya fitar da wata ka’ida ta binciken ilmi mai suna “Mie Scattering”, kuma ita ce ka’idar da masu bincike a wannan fanni ke amfani da ita har zuwa yau. Wannan malami ya yi wannan bincike ne a shekarar 1908.

Daga bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa lallai Malaman kimiyya sun bayar da lokacinsu sosai wajen bincike da kokarin gano wannan yanayi mai cike da tsari da mamaki.  Kuma a iya bincikensu, babu wanda ya gano cewa wannan yanayi na gajimare na da wani tasiri na musamman kan al’umma ko duniya, sabanin bayyanannun dalilan kimiyya da suka fito fili.  Har wa yau, tun da addinin Musulunci bai sanar da haka ba, to mu ma tuni muka takaita kan abin da muka ji kuma muke gani.  Imaninmu kuwa ya takaita ne kan cewa: “wannan yanayi na gajimare, kamar sauran yanayin kimiyya masu faruwa – irinsu kisfewar hasken rana ko wata da sauran makamantansu – yanayi ne da ke tabbatar da tsarin da duniyar ke gudanuwa a kai, da kuma cewa lallai ba su suka samar da kansu ba, akwai wanda ya samar dasu – wato Allah Madaukakin Sarki”.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.