Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster) (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar jumma’a, 3 ga watan Janairu, 2020.

241

A yau za mu xan dakata da bayani kan maudu’in da muka xauko makonni uku da suka gabata don yin bitar littafi na farko da aka wallafa kan fannin kwamfuta.  Da zarar mun gama wannan bita in Allah Ya so, za mu ci gaba da bayanin da muka xauko a baya.  Da fatan za a fa’idantu da wannan xan taqaitaccen sharhi.  Aci gaba da kasancewa tare damu.

————————-

A ranar asabar, 28 ga watan Disamba 2019 ne aka qaddamar da littafin Malam Salisu Hassan wanda aka fi sani da “Webmaster” a garin Kaduna. Malam Salisu Hassan dai Malami ne mai karantar da ilimin kwamfuta a shahararriyar makarantarsa dake unguwar Sanusi mai suna: “Duniyar Computer”, kuma mawallafin mujallar “Duniyar Computer” dai har wa yau.  Wannan littafi nashi, duk da cewa akwai wasu littattafai da aka rubuta a baya kan kwamfuta cikin harshen Hausa, sai dai, a hukumance, ba a samu irin wannan ba. Hakan ya faru ne saboda dalilai da dama.  Na farko dai shi ne littafi mafi girma da aka taba wallafawa a wannan fanni.  Shi ne littafi mai xauke da lambar jerin littattafan da aka rubuta a qasar nan, wato: ISBN.  Kuma littafi ne da ya kandamo abubuwa masu mahimmanci kan ilimin kwamfuta da haqiqanin abubuwan da ta qunsa.

- Adv -

Littafin, wanda aka yi wa suna da: “Kwamfuta – Ilimin da Kowa Ke Buqata”, mai shafuka 353, yana xaukene da babuka 11, a karshensa kuma aka bibiyi babukan da jerin kalmomin kwamfuta guda 500 tare da ma’anoninsu. Ina daga cikin waxanda suka yi bitar wannan littafi makonni 3 kafin qaddamar dashi.  Don haka naga dacewar rairayo mahimman abubuwan da littafin ya qunsa, don fa’idar masu karatun wannan shafi.  Haqiqa qaddamar da wannan littafi ba karamin ci gaba bane ga al’ummar Hausa a wannan zamani.  Ko ba komai dai, zai kara fadada fahimtar al’ummar Hausawan wannan zamani kan fasahar sadarwa na zamani; domin kwamfuta ita ce asalin dukkan wani ci gaba da ake samu a wannan fanni a duniya yanzu.

Malam Salisu ya kasa littafin ne zuwa vangare uku, duk da cewa bai bayyana hakan ba a zahiri ko a rubuce.  Vangaren farko ya kunshi Mukaddima ne. Wannan shi ne babi na xaya, kuma mawallafin littafin bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayanin ma’anar kwamfuta, da nau’ukan bayanan da take mu’amala dasu, irin su “data” da “information”.  Waxannan su ne nau’ukan bayanan da kwamfuta ke mu’amala dasu.  Ko dai ya zama bayanai ne da ake shigar mata, take sarrafawa don bayar da ma’ana; wannan shi ake kira “data”.  Sai kuma nau’ukan bayanai sarrafaffu, waxanda duk mai karatu zai iya gane me suke nufi kuma ya fitar da hukunci daga abin da suka qunsa.  Waxannan su ake kira “information”.  Daga nan yayi bayani kan irin ayyukan da kwamfuta ke iya gudanarwa.  A karshen babin ya kawo tarihin kwamfuta a takaice.  A Babi na biyu kuma mawallafin ya yi bayani kan karkasuwan kwamfuta ne ta amfani da ma’aunai daban-daban – tun daga farkon kwamfutar da aka fara qerawa zuwa zamanin da muke ciki yanzu.

Vangare na biyu na xaukene da babuka guda shida (babi na 3 zuwa babi na 8).  Wannan vangaren ne ya yi bayani filla-filla kan gangar-jikin kwamfuta, wato: “Hardware” Kenan.  A Babi na 3 mawallafin ya yi bayani kan ma’anar kalmar “Hardware”, da vangarorinta irin su na’urorin shigar da bayanai, da na fitarwa, da na aiwatar da sadarwa, da ma’adana, da vangaren sauti da na wutar lantarki duka.  Bayan wannan gabatarwa kan gangar-jikin kwamfuta a Babi na 3, sai mawallafin ya bibiyi babi na 4 zuwa na 8 da bayani filla-filla kan wadancan vangarori da ya fara bayaninsu a babi na 3.  Misali, a Babi na 4 ya yi bayani kan vangarorin shigar da bayanai ne ga kwamfuta, wato: “Input Devices”. Wannan ya haxa da allon shigar da bayanai (Keyboard), da beran kwamfuta (Mouse), da na’urar xaukan hoton bayanai (Scanner), sai kuma na’urorin shigar da sauti ko murya.  A Babi na 5 kuma marubucin ya fayyace bayani kan vangarorin fitar da bayanai daga kwamfuta, wato: “Output Devices”. Na’urorin sun haxa da talabijin kwamfuta (Monitor), da na’urar haskaka bayanai (Projector), da lasafika, da na’urar dab’i, da dukkan nau’ukan waxannan na’urori.

Bayani kan ma’adanar kwamfuta, wanda mawallafin ya kira da suna: “Ma’ajiya”, yana qunshe ne cikin Babi na 6, wanda yayi wa lakabi da: “Storage Devices”.  Qarqashin wannan Babi Malam Salisu ya fayyace ma’ana da nau’ukan ma’adanar kwamfuta, inda ya jero shahararru daga cikinsu, irin “Hard Disk Drive – HDD”, da “Solid State Drive – SSD”, da wasu ma’adana na musamman irin su: “Floppy Disk”, da “Optical Disc” – kamar su: CD da DVD da kuma Blue Ray Disc.  Marubucin ya bambance tsakanin ma’adanar da ake iya shigar mata da bayanai ta vangaren mai mu’amala da kwamfuta, da wacce ba a iya shigar mata; sai dai a wadatu da abin da tazo dashi.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Aliyu Sunusi Dalhat says

    Mungode sosai Allah ya sake da Mafificin Alkhairi gaskiya wannan abun farin ciki ne sosai matuqa koh a haka na qaro sosai ina ga ace zan samu wannan hardcopy din

Leave A Reply

Your email address will not be published.