Satar Zati a Kafafen Sadarwa Na Zamani (1)

Satar Zati (Identity Theft) yana cikin miyagun abubuwan da suka fi komai shahara a kafafen sadarwa na zamanin yau. Daga wannan mako za mu fara gudanar da bincike don hankado irin matsalolin dake tattare da wannan nau’i na ta’addanci, da kuma hanyoyi da za a iya bi don kariya.

399

Gabatarwa

A cikin kwanakin karshe na watan Maris (2018) ne dai Sashen Hausa na BBC suka gayyace ni don kasancewa cikin shahararren shirin nan nasu na musamman mai take: “Ra’ayi Riga,” wanda shiri ne na tsawon awa guda da suke gudanar dashi don tattauna wani al’amari da yake shafan al’umma kai tsaye, ko yake son shafansu – ta hanyar amfani ko cutarwa – a bangaren siyasa, ko addini, ko al’ada.  Sukan gayyaci masana daga wurare daban-daban wadanda suke kwararru ne a fannin.  Bayan ni, akwai jama’a da dama da suka gayyata cikin wannan shiri; wasu ta wayar tarho, wasu kuma a nan dakinsu na watsa shirye-shirye dake Abuja.  Daga ciki har da dan majalisar dattijai wanda shi ne ya taba daukan nauyin wani kuduri a majalisar dattajai don samar da doka kan kayyyade mu’amalar yan Najeriya a shafukan sada zumunta, wato: Sanata Bala ibn Na-Allah.

Maudu’in dai shi ne kan matsalar tsana da tsangwama musamman ga mata, a kafafen sada zumunta.  Da yadda wasu mazaje ke muzanta su ta hanyar sace hotunansu ko ma kwace musu shafukansu a dandalin.  Wasu kuma kan musu batanci ta hanyar sace hotunansu da yada su a Intanet, a matsayin su ne suka saka.  Ko kuma su yi amfani da manhajar kintsa hotuna don muzanta su a matsayin mazinata, ta hanyar nuna tsaraicinsu.  Kasancewata cikin wannan shiri ne ya kara tabbatar mini da yadda lamarin yayi muni, musamman a arewacin Najeriya.  Domin anyi hira da ‘yan mata da maza wadanda abin ya shafe su kai tsaye.  Cikin dukkan wannan hira dai, abin da yafi munanta al’amarin shi ne samuwar sace-sacen shafukan mutane da kuma yin amfani dasu wajen aikata ta’addanci.  Wannan bala’i ne mai girman gaske, ba karama ba kuwa.

Dalilin samuwa da saurin yaduwar wadannan al’amura masu bakanta rai a kafafen sadarwa dai ba nesa yake ba.  Shi ne bunkasar fasahar Intanet, da samuwar hanyoyin mu’amala da yada bayanai cikin sauki, wanda ke kunshe mutane a wuri daya, ta yadda kowa na iya ganin abin da dan uwansa ke yi muddin akwai alaka ta abota a tsakaninsu.  Bayan wannan, a fannin kimiyyar kere-kere ma, wanda ke da alaka da sadarwa, akwai abubuwan mamaki dake samuwa wanda dan adam bai taba tunanin faruwarsu ba a wannan duniya.  Idan masu karatu basu mance ba, cikin shekarun da suka gabata na gabatar da wata kasida mai kunshe da binciken yadda nan gaba ake sa ran za a iya sace wa dan adam tunaninsa daga kwakwalwarsa.  Ma’ana, kana zaune da tunaninka a kwakwalwarka, wani na iya amfani da hanyar sadarwa wajen gano abin da kake tunani, inda hali ma, ya nade tunanin a kwamfuta ko wayarsa ta salula, ta amfani da manhajar sadarwa, cikin sauki.  To a yanzu kuma ga wata matsala, wato: Satar Zati.  Mai karatu bazai yarda ba, ba kuma zai amince ba ace ga shi a zaune, amma an sace masa zatinsa.  Zatin mutum ba wani abu bane face hakikaninsa.  To wannan tuni ya fara yiwuwa.

A cikin watan Satumba na shekarar da ta gabata (2017) na gabatar da kasida kashi na farko kan wannan al’amari, wanda na sanya wa take: “IDENTITY THEFT – Hattara Dai Jama’a!”.  Na gabatar da wannan gajeriyar kasida ne a shafina dake Facebook (www.facebook.com/babansadik), inda na san wannan matsala ta fara shafar al’ummarmu ta arewa, kai tsaye.  A cikin kasidar na yi bayani ne kan ma’anar kalmar “Identity Theft”, da yadda hakan ke faruwa, da dalilan da ke sa hakan ya faru, da kuma hanyoyin da masu yin wannan ta’addanci suke bi wajen aiwatar da shi.  Sai dai na yi hakan ne a takaice.  Kuma bangaren satar zati a kafafen sada zumunta kawai nayi bayani a kai.  A karshe nace zan ci gaba, amma hakan bai yiwu ba saboda yanayin shagulgula da suka sha gabana.

To amma wannan gayyata da Sashen Hausa na BBC suka mini ya kara zaburar dani wajen ci gaba da wannan silsila na fadakarwa kan wannan al’amari.  Musamman ganin cewa a wancan lokacin da na fara kasidar ma, bayanai ne suka bayyana na yadda ake sace wa manyan malamai dake kafafen sada zumunta shafukansu, ana ta’addanci dasu.

Na samu gayyata kan haka don kokarin magance wannan al’amari daga malamai da dama dake arewacin Najeriya.  Kuma ni kaina cikin shekarar 2015 in ban mance ba, na kai kwarmaton rufe shafukan bogi da aka bude da sunan mai martaba Sarkin Kano mai ci a yanzu, wato: Alhaji Muhammadu Sunusi na II, ga hukumar Facebook, wajen guda 4 ko biyar in ban mance ba.  Da shafukan da suka shafi shugaban kasa mai ci a yanzu, wato: Shugaba Muhammadu Buhari.  Da kuma babban attajiri na Kano, wato: Alhaji (Dr.) Aliko Dangote.  Dukkan wadannan mutane ba su da shafi a Facebook.  Duk inda ka gani, to shafin bogi ne.  Haka ma shafin uwar Gidan shugaban kasa, wato: Hajiya Aisha Buhari.  Idan ka sake kayi mu’amala da mai shafin, kai ka jiyo, sautun mahaukaciya.

- Adv -

Ina gab da hada wannan kasida ne naci karo da wani rahoto na musamman da jaridar Daily Trust ta buga a ranar 30 ga watan Mayu da ta gabata, kan yadda wannan matsala na satar zati ke yaduwa kamar wutar daji a Najeriya.  Da yadda masu ta’addanci a kafafen sada zumunta ke amfani da wannan tsari wajen damfarar mutane a matsayinsu ne masu sunayen.  Rahoton ya kara tabbatar da cewa wadanda aka fi satar zatinsu a Najeriya dai su ne shahararrun mawaka, da shahararrun ‘yan siyasa, da shahararrun masu kudi da manyan hafsoshin tsaro na kasa – irin soji da ‘yan sanda.  Wannan  ke nuna yadda lamarin yaci gaba da Kamari a wadannan kafafe.  Nan gaba mai karatu zai samu cikakken bayani kan wannan rahoto na Daily Trust.

Makunshi

A cikin wannan jerin kasidu dai, wanda nake sa ran zasu tsawaita iya gwargwadon hali, zan fadada bayani ne kan wannan maudu’i.  Da farko za a fahimci ma’ana da asalin Kalmar “Identity Theft”; me take nufi?  Yaushe aka fara amfani da ita?  Sai bayani kan nau’ukan wannan ta’ada da launukanta.  Bayan wannan, mai karatu zai samu bayanai kan dabarun da masu wannan ta’ada ke amfani dasu wajen kaiwa ga bayanan mutane na sirri ko na bayyane, don amfani dasu wajen aiwatar da ta’addanci.  Wadannan hanyoyi suna da matukar yawa; iya zurfafa bincikenka iya yawansu.  Domin dabaru ne, kuma ita dabara tana da fadi – iya gwargwadon kaifin basirarka take samuwa.  Za mu dubi iya wadanda suka fi shahara ne kawai.

Bayan haka, sai bayani kan alamun dake nuna cewa lallai an sace maka zatinka.  Me yasa haka?  Saboda wannan tsari na satar zati abu ne boyayye.  Idan barawon bai bayyana ba ta hanyoyin da nan gaba zamu gani, kai mai shafi ko bayanan ba ka iya ganewa, sai dai ka ga mummunar sakamakon aikinsa kawai yana aukuwa.  Wannan yasa satar zati take da hadari matuka.  Domin a wasu kasashe idan mutum ya fahimci an sace masa zatinsa kuma har an fara amfani da ita wajen ta’addanci, wasu kan kashe kansu kai tsaye.  Abu ne mai hadari jama’a.

Daga nan sai bayani kan nau’ukan sakaci da mutane ko ma’aikatan hukumomi ko jami’an tsaro ke yi da bayanai, wanda hakan ke sawwake wa dan ta’adda wahalarsa na neman bayanai.  Cikin sauki ya same su.  Za mu kuma duba kasashen da suka sanya doka ta musamman kan wannan tsari na ta’addanci, sannan mu dubi wasu fina-finai ko rubuce-rubuce da aka yi su don fadakarwa kan wannan mummunar hanyar ta’addanci.

Bayan dukkan wannan, mai karatu zai ga mummunar tasirin wannan al’amari na satar zati ga daidaikun jama’a, da kasashe.  A nan ne mai karatu zai fahimci hakikanin munin wannan tsari na ta’addanci.  Kamar yadda nayi ishara ne a sama, wasu kan kashe kansu idan suka fahimci an sace musu zatinsu.  Domin a kasashen da suka ci gaba, idan aka ci nasarar aiwatar da wannan ta’addanci a kan mutum, to, ya shiga uku, musamman idan barawon yayi amfani da bayanansa wajen aiwatar da wani ta’addanci na kisa ko sata, ko zamba.  Ba wanda za a kama sai mai asalin bayanan.  Wannan ya faru ne saboda a wadannan kasashe, hukuma tana da bayanan kowa da kowa a rumbun adana bayananta (National Database).

A karshe za mu kawo hanyoyin da mai karatu zai iya kare kansa daga wannan matsala tun kafin ta auku.  Da hanyar da za ka bi wajen wanke kanka idan ta riga ta auku baka sani ba, musamman idan abin ya shafi jami’an tsaro Kenan.  Wadannan su ne abubuwan da nake sa ran za mu tattauna kan su in Allah Yaso.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. […] jerin makaloli ba, suna iya ziyartar Taskar Baban Sadik.  Ga adireshin dake dauke da bayanin: https://babansadik.com/satar-zati-a-kafafen-sadarwa-na-zamani-1/, ko kuma shafin AMINIYA dake: https://aminiya.dailytrust.com.  A karshen kashi na daya, za a ga ci […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.