Sakonnin Masu Karatu (2021) (5)

Matsayin Can Wa Wayar Salula Lambobin IMEI

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 19 ga watan Fabrairu, 2021.

184

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya kuma komai na tafiya daidai. Bayan haka, ina cikin daliban dake bibiyar shafinka a jaridar AMINIYA.  Kwanan baya ka bada amsa ga wani da yace in yayi “Restoring” wasu wayoyi suna nuna alamar INVALID IMEI bayan gamawa, sai ka bashi amsa inda har aka je ga inda kace ana dora sababbin lambobin IMEI. Tambayata a nan ita ce: idan aka dora sabuwar lambar IMEI din, wannan ya nuna ainihin lambar IMEI wayar ya bata kenan? Kuma idan aka sace wayar, ta bace kenan? Idan haka ne, yaya za ayi tracking wayar ko Kuma gano ta tunda an canza mata lambobin?  Lawal Yusuf:  08031592602 – lawalyusufabba@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Lawal barka dai.  Na ji dadin wannan tambayar neman karin bayani da kayi.  A wancan karo nayi bayanin yiwuwar canza wa wayar salula lambobin IMEI ne, saboda yadda aka samu ci gaba wajen manhajojin da ake iya amfani dasu wajen farke wayar salula, wato: “Rooting”, ko “Flashing”, kamar yadda nayi rubuce-rubuce a baya.  Amma ban bayyana cewa ba kowace nau’in wayar salula ake iya mata haka ba cikin sauki.  Misali, wayoyin salula masu dauke da masarrafar MTK, irin su Tecno, da Infinix, da Gionee, da Itel, da Oppo, da Vivo da sauran makamantansu, ana iya farke su ta dadi, kuma har a iya canza musu lambar IMEI.  Amma wayoyin salula masu dauke da masarrafar Qualcom, irin su Samsung, da Sony, da Huawei, canza lambar IMEI dinsu yana da wahala sosai, in ma bance bai yiwuwa ba.  Haka ma wayoyin salula nau’in iPhone.  Domin ba kowace manhajar filashin ke iya farke su ba.  Don haka, amsar da na bayar a baya ta la’akari da wayoyin Android ne da suka fi shahara a kasashenmu, wadanda ke dauke da masaraffar MTK.  Sai dai a galibin kasashen duniya, canza wa wayar salula lambar IMEI ya saba wa doka.

Mu dawo kan tambayar, ya danganci yanayin waya, da dokar kasa da kuma zamanin da ake ciki.  A baya sadda ake yayin wayar salula nau’in Blackberry, da yawa cikin mutane kan canza wa wayoyinsu lambar IMEI don samu iya mu’amala da manhajar BB Chat a lokacin.  Musamman masu amfani da katin Glo, ina nufin a Najeriya kenan.  Kuma kamar yadda na fada a baya, har yanzu akwai masu canza wadannan lambobi, duk da cewa ba abu bane da ya dace.  Idan aka canza wa wayar salula lambar IMEI dinta, wanda su ne lambobin da ake amfani dasu wajen gano inda wayar take, abubuwa biyu ne muhammai zasu iya faruwa:  na farko, canza wa wayar salula sababbin lambobin IMEI, zai sa ta rasa asalin wadanda tazo dasu ne, kamar yadda ka, sannan ko da an sace ta, ba za a iya amfani da wadancan lambobin da tazo dasu na asali, wajen iya gano inda take ba.  Kuma idan wanda ya canza lambar barawon da ya sace ta ne, shikenan, an rasa wayar kenan.  Amma idan asalin mai shi ne ya canza mata, kuma yayi amfani da sababbin lambobin da ya canza wajen kokarin gano ta bayan ta bace ko an sace, nan ne bayani na biyu zai shigo.

- Adv -

Idan yayi nasarar canza lambobin, kuma har yaci gaba da aiki da ita wajen karban kira da aiwatar da kira, to, akwai sa ran za a iya ganota, muddin sababbin lambobin da ya canza mata suna tare dashi.  Amma idan wayar na cikin nau’ukan wayoyin da ba a iya canza musu lambar IMEI cikin sauki ne – irin su Samsung da Huawei ko iPhone – to, a nan kuma dayan abu biyu ne zai iya faruwa.  Abu na farko shi ne, wayar salular na iya lalacewa gaba daya, ma’ana ta kasa tashi, bayan an canza mata wadannan lambobi.  Galibin wayoyin salula na kamfanin Samsung sun fi nuna wannan dabi’a.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, wayar ba za ta karbi sabuwar lambar da aka loda mata ba.  Idan kuma anci nasarar canza lambar wayar ta karba har ta tashi, to, a nan kuma, kamfanin wayoyin salula na iya kin karbarta a na’urorinsu.  Ma’ana, da zarar an kunna ta tashi, baza ta iya hawa kan yanayin sadarwa ba, wato: “Network”.  Domin na’urar kamfanin way ana iya gane cewa an canza wa wayar salula wadancan lambobi, kai tsaye.  Kuma a wasu kasashe, dokokin hukuma na iya tilasta kamfanin waya ya ki karbar wayar.  Wannan zai sa ya zama barawon wayar yayi batan-baka-tantan kenan.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba:  don ka yi resetting din waya, ba shi zai sa ka iya canza mata IMEI ba.  Sai in filashin na musamman aka mata, kuma aka dace (ko aka yi rashin dace) masarrafar wayar nau’in MTK ce.  Shi kuma irin filashin din dake baiwa mutum damar canza lambar IMEI, ba kowa ke iya mallakar abubuwan da zan iya gudanar da aikin ba.  Meye dalili?  Amsar ita ce: CANZA LAMBAR IMEI GA KOWACE WAYAR SALULA CE, LAIFI NE MAI GIRMA A GALIBIN KASASHEN DUNIYA.  DOMIN HANYA CE MAFI SAUKI DA WASU KE IYA BI WAJEN HALASTA WAYOYIN SATA DA SUKA SATO, KO AKA SATO AKA KAWO MUSU.  KUMA KAMAR YADDA NA FADA A BAYA, GALIBIN KAMFANONIN WAYAR SALULA A DUNIYA SUNA IYA GANE CEWA AN CANZA WA WAYAR SALULA LAMBOBINTA NA IMEI.  IDAN HAKAN YA FARU KUWA, SUNA HANA WAYAR HAWA NA’URARSU.  MA’ANA BA ZA A IYA AMFANI DA ITA BA KENAN, TUNDA AN MATA TAMBARI MUMMUNA.  DON HAKA, CANZA LAMBAR IMEI GA KOWACE WAYA CE, AIKI NE HARAMTACCE A GALIBIN KASASHE, SAI DA IZININ HUKUMA.  A TARE DA CEWA BAN SAN WATA DOKA TA MUSAMMAN A NAJERIYA KAN HAKAN BA KARARA, YANA DA KYAU MUTANE SU KIYAYE.

A karshe dai, idan aka sake loda wa wayar salula sabon lambar IMEI, kuma har ta dauka, kuma ta iya hawa na’urar kamfanin waya, akwai sa rai (ba garanti bane) cewa za a iya gano duk inda take idan ana amfani da ita, kai tsaye; muddin kamfanin wayar salular da SIM dinsa ke kan wayar bai toshe ko hana wayar hawa na’urarsa ba.  A tare da haka, zan maimaita cewa yin hakan, duk da cewa akwai manhajoji da dama a cibiyar Play Store dake taimakawa, aiki ne haramtacce a galibin kasashe, kuma zai iya zama laifi a Najeriya ma.  Domin ba shi da bambanci da wanda lambar motarsa ta karye, ko ta fadi ta lalace, sai yaje aka masa wani daban, ba asalin nata ba.  Sai a kiyaye.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.