Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (19)

Kashi na 19 cikin jerin makalolin da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Asha karatu lafiya.

208

Hanyoyin Kariya (3)

Takatsantsan Wajen Saukar da Manhaja

Manhajojin kwamfuta ko na wayar salula da ake saukarwa kyauta, suna nan birjik, kuma bayan fa’ida ko alfanun da suke dauke dasu, a daya bangaren suna tattare da matsaloli masu girman gaske.  Ko kuma ince hadari mai girman gaske.  Hadarinsu kuwa shi ne, na farko dan adam ne ya gina su, kuma da manufa ta musamman.

‘Yan dandatsa masu neman bayanan mutane a sawwake sukan gina manhaja ne, wacce a zahirinta zaka ga tana dauke da fa’idoji masu girman gaske.  Amma a daya bangaren kuma, da zarar ka loda wa kwamfuta ko wayarka ta salula, za ta ci gaba da kwasan bayanan da suka danganceka ne kai tsaye, tana aika wa uban gidanta.  Kai baka sani ba.  Babbar matsalar ma ita ce, idan ba kwararre bane kai a fagen kimiyyar sadarwa na zamani, tantance ire-iren wadannan manhajoji daga manhajoji ingantattu abu ne mai wahala kwarai da gaske.  Idan kayi kuskure ka saukar da manhajar wayar salula ko kwamfuta, mai dauke da ire-iren wadannan tsare-tsare na leken asiri, duk abin da kake rubutawa ko karba a kan wayarka ko kwamfutarka, tana nadewa ne, ba tare da saninka ba.  Da zarar magininta ya gama tara bayanan da yake bukata, sai dai kaji ana sanar dakai cewa ka

- Adv -

Takatsantsan Wajen Rajistan Shafi a Dandalin Sada Zumunta

Hanya mafi sauki wajen samun jama’a a Intanet ita ce ta shafuka ko dandalin sada zumunta.  Hakan ya faru ne saboda dalilai da dama.  Mafi girma daga ciki shi ne irin tsarin da mahallin ke dake dashi, da zarar ka mallake shi ba tare da canza komai daga cikin tsare-tsaren da maginansu suka yi ba.  Wannan yasa dole a matsayinka na mai son zaman lafiya, ka san me ya kaika wajen, sannan mece ce manufarka?  Amsar wadannan tambayoyi ne za ta tabbatar da hakikanin shafinka.  Don haka, da zarar ka zo rajista, za a bukaci ka bayar sunan da kake son amfani dashi, wanda da shi ne manhajar dandalin za ta yi amfani wajen hada alaka tsakaninka da wadanda take ganin kuna da kamaiceceniya.  Za a bukaci adireshin inda kake zaune, da lambar wayarka, da adireshinka na Imel, da shekarar haihuwarka, da matsayinka a rayuwa, da tarihin karatunka, da kuma hotonka.

Dukkan wadannan bayanai ana bukatarsu ne don gina zatinka a dandalin, da kuma dauko wadanda kuke da kama na adireshi, ko karatu, ko zaman gari ko kasa daya, don bijiro maka dasu.  Wannan ita ce babbar manufar samar da dandalin Facebook; hada alaka tsakanin mutanen da ke da alaka ta zahiri.

Wadannan bayanai naka ne dan dandatsa ke bukata don sace maka zati.  Kuma a ka’idar Dandalin Facebook misali, muddin ka bude sabon shafi, to, duk wanda ke abota dakai zai ga da yawa daga cikin wadannan bayanai naka.  Amma akwai bangaren “Settings”, watau inda tsare-tsaren shafinka suke. Kana iya zuwa wurin, ka boye da yawa daga cikin bayanan da ka bayar, ta yadda ko abokanka ma baza su iya gani ba, sai wanda ya roka, in ka ga dama, ka bashi.  In Allah Yaso, nan da wasu lokuta zan yi darasi na musamman kan yadda ake boye bayanai a Facebook.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Abdulmalik Hassan gusau says

    Masha Allah Allah yakara daukaka abban sadik

Leave A Reply

Your email address will not be published.