Yadda Ruwan Sama Ke Samuwa

Yau kuma ga mu dauke da bayani a kashi na uku kan yadda ruwan sama ke samuwa. Wannan na daga cikin abubuwa masu sarkakiya dangane da samuwar ruwa, musamman ruwan sama. A sha karatu lafiya.

830

Yadda Ruwan Sama ke Samuwa

Da zarar wannan ma’adana mai dauke da danshin ruwa a yanayin tururi (wato Water Vapour) ta tumbatsa, sai ruwan ya sake saukowa kasa a yanayi uku.  Yanayin farko shi ne yanayin ruwan sama, kamar yadda muka sani. Yanayi na biyu kuma shi ne yanayin kankara; ko dai wanda ke zubowa a tare da ruwan sama (wato Ice Pellets), ko kuma dusar kankara da ke zuba a wasu kasashe inda sanyi ya kai matuka (wato Snow).  Sai yanayi na uku kuma shi ne yanayin raba; wato danshin ruwa mai sanyi da ke zuba cikin dare (ko Dew a kimiyyance).  Wannan ruwa da ke zuba yana zuba ne a kullum, kamar yadda wancan tururin danshin ruwa da ke haurawa ma’adanar ruwa a sama a kullum.  Bayan nan, malaman kimiyya suka ce a kowace rana a kan samu a kalla adadin yawa da fadin ruwa a ma’aunin yawa, wajen 300 (wato 300 Cubic Km).  Kuma cikin wannan adadi na ruwa da ke zuba a matsayin ruwan sama, ko kankara, ko raba, kashi daya cikin uku (⅓) ne kadai ke zuba a gundarin kasa, sauran kashi biyu bisa ukun (⅔) na zuba cikin teku ne, ko kogi, ko kuma rafukan da muke da su a duniya – su sake komawa cikin sama a yanayin da bayaninsa ya gabata.  Sai dai kuma, na san mai karatu zai so sanin yadda ruwan sama ke sauka, a kimiyyance.

Kamar yadda bayani ya gabata, ruwan da ke zuba daga sama shi ne ruwan da ke makare cikin ma’adanar danshin ruwa da ke yanayin tururi a sararin wannan duniyar tamu, wato Water Vapour kenan.  Daga nan sai su zubo, amma ba kai tsaye suke zubowa ba.  Domin ruwa, kamar yadda yake, yana zubowa ne daga jikin giragizai, wato Clouds a turance.  Su wadannan giragizai a sama suke, haka ma wannan ma’adana ta sararin duniyarmu.  Sai dai kuma, sabanin giragizai da dan adam ke iya ganinsu da ido, ita wannan ma’adana a yanayin iska take, a makare da ruwa cikin yanayin tururi mai danshi.

Tsakanin sararin samaniyar wannan duniyar ta mu da saman tekuna, akwai iska nau’uka daban-daban.  Akwai iskar da ke kada ruwan teku har a samu taguwar ruwa, sanadiyyar juyawar bigiren rana da wata. Wannan iskar ce sanadiyyar ambaliyar ruwa.  Akwai iskar da ke kintsa kasar da muke takawa kafin zuwan ruwan sama.  Akwai iskar da Allah ke kado ta zuwa duniya a matsayin bushara gare mu don samuwar ruwan sama. Akwai iskar da ke taskance ruwa a yanayin danshi kamar yadda bayanai suka gabata.  Akwai iskar da ke hado kan giragizai waje daya. Akwai iskar da ke yin barbaran giragizai, har su cika da ruwa, sannan ruwan ya zubo kasa. Akwai iskar da ke rarraba giragizan da ke shake da ruwa zuwa jihohin duniya daban-daban, iya yadda Allah ke so.  Sannan kuma akwai nau’in iskar da ke kora giragizai masu dauke da ruwa.  Dukkan wadannan nau’ukan iskoki suna nan, kuma ba iyakansu ba kenan, sai dai wadanda suka danganci ruwan sama ne wadannan.  Kuma wani abin sha’awa shi ne, dukkansu Allah ya yi bayaninsu, da yanayin aikinsu a cikin Kur’ani.

Da zarar Allah ya nufi saukar ruwa, sai ya aiko iskar da za ta kintsa kasa don karban ruwan da ke tafe.  Sannan sai iskar da ke bushara ta biyo baya.  Ita ce iskar da ke zuwa da karfi, cike da kura ko tarkacen da take dibowa.  Sakon da take aiko mana shi ne, “kowa ya kintsa kayansa, ga ni’ima nan tafe.”  Wannan iska ce ta bushara, musamman ga al’ummar da aka dade ba a musu ruwa ba, ko suke fama da fari. Daga nan kuma sai wannan iska mai makare da ruwa a yanayin danshi ta kada, sannan tayi barbarar giragizai, ta cika su da ruwa.  Nan take sai ka ga giragizai sun yi baki kirin, sai kaji rugugi, sai cida; ga kuma iskar bushara na bugawa.  Daga nan sai iskar da ke kada giragizan su fara nasu aikin, sai ruwan sama ya fara zuba.  Daga nan sai iskar da ke rarraba wannan ruwa ta biyo baya, ta rika warwatsa giragizan zuwa jiha ko bigiren da aka nufe su da samun wannan ni’ima. Nan take sai ka ga hadari ya fara zama fari daga launin bakin da yake a farko; saboda ruwa ya fara zuba.  Dangane da bayanan da suka shafi nau’ukan iska, da yadda suke barbarar giragizai, da rarraba su, da kora su, mai karatu na iya duba wadannan ayoyin Kur’ani: Suratul Hijri, aya ta 22; A’raaf, aya ta 57; Noor, aya ta 43 da 45; Furqaan, aya ta 48 da 49; da suratu Room, aya ta 48.

- Adv -

Ta yiwu mai karatu ya ce me yasa ruwan sama ke zuwa da kankara, kuma ruwan da sanyi yake zuwa, haka ma kankaran?  Kuma hatta raba da ke sauka cikin dare, da sanyi yake zuwa. Me yasa?

Fahimtar haka abu ne mai sauki.  Domin idan ba a mance ba, a kasidar farko na sanar da mu cewa wannan duniya ta mu Allah ya ajiye ta ne a wani bigire matsakaici, wanda ke dauke da yanayin zafi ko sanyin da suka yi daidai da yanayin dabi’a da rayuwar halittu.  Wannan yanayin zafi da sanyi su ne suke sa duk wani ruwa da ya bi iska ya haura sama a yanayin tururi, ya zama mai sanyi, a wasu lokuta ma har ya daskare.  A wasu duniyoyin, musamman duniyar Satun, babu ruwa narkakke, saboda yanayin wurin ya wuce kimar da za a samu ruwa narkakke kamar yadda muke da shi a duniyarmu.  Don haka duk ruwan da ke makare a sararin duniyar Satun, gundarin kankara ne, wanda ba a tunanin ranar fashewa balle narkewarsa. Dangane da duniyarmu kuwa, tunda akwai sabanin yanayi wanda hakan ke haifar da yanayi madaidaici, don haka muke samun ruwa narkakke da wanda ke yanayin kankara, da kuma raba, da ma ruwan da ke yanayin danshin tururi da ke bin iska.  A takaice muna da dukkan nau’ukan ruwa a wannan duniya tamu.

Har wa yau, mai karatu na iya tambayar dalilan da suka sa ake samun canjin yanayin damina tsakanin kasashe, ko nahiyoyin duniya. Shi ma amsar wannan ba nesa take ba.  Babban dalilin da ke haddasa hakan shi ne jujjuyawan lokutan dare da yini, da samun canji a yanayin bigiren rana da wata.  Da kuma tsarin juyawar duniya a kwanakin shekara.  Wadannan, na tabbata, suna cikin bayanan da muka karanta cikin littafin Dakta Adnan, na Gwagwarmaya kan Ilmin Sararin Samaniya. To, bayan saukar ruwan sama, sai me? Sai mataki na hudu.

Mataki na Hudu

Kashi biyu cikin uku (⅔) na ruwan da ke saukowa daga sama – a yanayin narkakken ruwa, ko kankara, ko raba –  yana zarcewa ne cikin tekuna, da koguna, da kuma rafuka. Kashi daya cikin ukun (⅓) ne kawai ke zuba a saman kasa.  Wannan kaso kan gangara cikin tekuna shi ma daga inda ya zuba, kasa tasha iya shanta.  Wadannan rafuka sukan cika su batse, daga nan su antayar da raran ruwan zuwa cikin teku.  Kamar yadda muka sani, dukkan tekunan duniya a jone suke da juna ta wasu hanyoyi.  Shi yasa a ranar Kiyama Allah zai kece dukkan shamakin da ke tsakaninsu, su zama teku guda, sannan a karshe ya kone su.  (Duba Suratut Takweer, Aya ta 6, da suratul Infitaar, Aya ta 3).  Sannan dukkan kogunan da ke cikin kasashenmu, da rafukan da ke ciki, duk karshensu yana hadewa ne da wadannan manyan tekuna da ke tsakani ko bayan kasashen duniya.  Dukkan kankaran dake fadowa a kasa, sukan narke, kuma ruwan kan gangara zuwa cikin rafuka ko kogunan da muke da su.  Da zarar sun antayo cikin tekuna, sai a sake samun maimaituwan wannan tsari kamar yadda bayanai suka gabata a baya. Wannan shi ne mataki na karshe.

Daga bayanan da suka gabata, mai karatu zai ga cewa lallai ruwan sama da ake samu, da sauran hanyoyin samun ruwa a duniya, duk abu ne guda daya, wanda ke maimaituwa, cikin kudura da iradar Ubangiji.  A mako mai zuwa za mu ci gaba, inda bayanai za su zo kan nau’ukan sinadaran da ke dauke cikin ruwa; narkakke ne, ko daskararre a yanayin kankara, ko kuma wanda ke yanayin tururi a cikin iska.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.