Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (18)

Kashi na 18 cikin jerin bayanan da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Asha karatu lafiya.

228

Matakan Kariya (2)

Takatsantsan da Bayanan Imel

Duk da cewa da yawa cikinmu bamu cika damuwa da yin rajistan Imel ba, idan ba tilasci bane irin ta aikin gwamnati, ko makaranta, ko wani abu makamancin haka, ga masu akwatin Imel, dole ne su rika takatsantsan da bayanansu.  Idan kana amfani da Imel a shafinka na sada zumunta, to, ka san cewa “Password” dinka na Imel yafi mahimmanci akan “Password” dinka na Facebook ko Twitter.  Domin duk wanda ya samu “Password” dinka na Imel, wanda ka dora a shafinka na Facebook, sace shafinka gare shi ba abu bane mai wahala.  Duk wanda ya bukaci adireshinka na Imel, adireshin kadai za ka bashi, ban da “Password” din.  Shi “Password” sirrinka ne a duniyar sadarwa.  Duk wanda ka bashi “Password” dinka, to, ka bude masa sirrinka ne gaba daya.  Wasu ba su bambancewa.  Idan kace “Ba ni adireshinka na Imel” sai ya cillo maka har da “Password”  din.  Wannan kuskure ne.  Don haka a kiyaye.

Takatsantsan da Bayanan Shafukan Sada Zumunta

Idan kana da shafi a Facebook, ko Twitter, ko Youtube, ko LinkedIn, dole ne ka rika takatsantsan da su; kada ka taba ba wani “Password” dinka na Facebook ko daya daga cikin wadannan shafuka, sai da hujja kwakkwara.  Watakila wani ya sace maka shafinka, ana kokarin ceto shafin, kuma kai baza ka iya ba.  To a nan ba laifi ka baiwa masanin da zai ceto shafin.  Domin a yanzu “Password” din, in ma yana da wani amfani, to amfaninsa kadan ne.  Da zarar an gama gyara shafin ko kwato shi, ko da wanda ya gyara shafin ya sanya maka sabon “Password”, kayi maza ka canza naka.  Sannan ka sani, ba a ba da aron “Account” ko shafin Facebook.  Da yawa cikin mata kan ba da aron account, nasu na kansu, ga kawayensu.  Wannan kuskure ne.  Munanan labaru kan haka na nan birjik.  Sai a kiyaye.

Takatsantsan Wajen Bayar da Bayanai a Gidajen Yanar Sadarwa

- Adv -

Ga wadanda ke shawagi a gidajen yanar sadarwa na Intanet don neman fa’idoji kan bincike ko fadakarwa ko Karin bayani, galibi idan ka bukaci wasu bayanai a wasu shafukan gidajen yanar sadarwa, akan bukaci kayi rajista tukun, kafin a ka samu damar shiga. Wannan rajistan galibi bai wuce ka bayar da adireshinka na Imel, sannan ka zabi “Password”.  Da wadannan bayanai ake sa ran nan gaba idan ka sake ziyartar gidan yanar, za ka yi amfani wajen shiga ko isa ga shafin da kake bukata.  Bayan adireshin Imel, akan bukaci ka bayar da sunanka, da a wasu lokuta ma da adireshin inda kake zaune.  Wadannan bayanai naka suna da mahimmanci a gareka, kuma sau tari ire-irensu ne dan Dandatsa ke bukata don kera jabunka.  A nan sai ka kiyaye.  In so samu ne, kayi rajistan adireshin Imel na musamman, wanda shi za ka rika bayarwa idan an bukata, kuma dashi za ka rika karban sakonni ko bayanan da kake bukata a ire-iren wadannan shafuka.  Ya zama adireshin Ime ne na jeka-na-yi-ka kawai.

Amma asalin adireshinka na Imel, wanda ke wakiltar sahihan bayananka, ka ajiyeshi don bukata ta musamman.   Haka ma suna, ya zama kana da wani lakabi da zaka rika amfani dashi a ire-iren wadannan mahalli.  Idan adireshi ne ma, ka rika amfani da takaitattun bayanai.  Amma hakikanin bayanan da suka shafeka kai tsaye, ka kebance su ga lokaci da yanayi da kuma mahalli na musamman.  Misali, ina da adireshin Imel wanda dashi nake karban sakonnin masu karatu a wannan shafi.  Ina da adireshin Imel wanda dashi nake gudanar da cinikayya a shafukan Intanet, ina kuma da adireshin Imel wanda shi nake bayarwa a gidajen yanar da naje neman bayanai.  Haka ma suna, ba na amfani da hakikanin sunana, ko hakikanin adireshina, ko kuma hakikanin Imel dina, a ko ina.  Wannan misali ne.

Sannan ka zama mai takatsantsan wajen tantance gidan yanar sadarwa sahihi daga jabunsa.  Akwai gidajen yanar sadarwa da miyagu ke budewa na musamman, ta hanyar kwafan gidajen yanar sadarwa sanannu a duniya, don yaudarar masu ziyara, da sace musu bayanai.  Hatta galibin tallace-tallacen da kake gani a shafukan Facebook, idan ka latsa su, da yawa daga cikinsu za su zarce da kai wani jabun gidan yanar sadarwa ne.  Wannan tsari shi ake kira: “Phishing”.

A dandalin Facebook akwai shafuka na bogi masu dimbin yawa, kamar yadda bayanai suka tabbatar kuma muka sha nanatawa.  Daga cikin ire-iren wadanna shafuka akwai wadanda ke dauke da tayi ga jama’a, cewa: duk wanda ya “So” (Like) ko “Yada” (Share) wani hoto ko bidiyo da aka turo, to, za a bashi tikitin jirgin sama kyauta!  Wannan ya fi shahara ne a galibin kasashen turai.  Sai dai dole mu fadaka mu ma, domin idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, sai ka nemi kogi kayi alkafira a cikinsa don jike naka gemun.

Tsarin “Like” da “Share” a Facebook suna da amfani sosai, kamar yadda kuma suke da matukar cutarwa, ga wanda bai iya mu’amala dasu ba. Idan kaga irin wadannan hotuna ko bidiyo ko bayanai masu dauke da irin wannan tayi na cewa idan kayi “Like” ko kayi “Share” din shafin, za a baka kyautar abu kaza, kada ka latsa.  Domin ire-iren wadannan shafuka da suke dauke da wannan tayi shafukan karya ne.  Watakila kace mini ai shafuka ne na kamfanonin jiragen sama sanannu, irin su: “British Airways” ko “KLM” ko “Qatar Airways” ko “Emirate Airways.”  Ko kuma, a daya bangaren, kaga kamfanoni irin su: “Arik Air” ko “Chanchangi Airlines” ko “IRS Airlines” ko kuma “Azman Air,” a Najeriya kenan.  Eh, sunayen kamfanoni ne da ake dasu, amma shafukan dake yin wannan tayin, shafukan bogi ne; ba shafukan hakikanin kamfanonin bane.  Masu wannan ta’ada mummuna suna gina shafin yanar sadarwa ne na musamman, mai dauke da bayanai iri daya sak, da na kamfanin da suke son kwafowa, sannan su hankado bayanan da suke son yaudarar jama’a dasu dauke da adireshin wannan shafi na bogi.

Idan kaga haka, kada ka matsa “Like” kuma kada kayi “Share,” in kuwa ba haka ba, za ka gwammace kidi da karatu.  Ma’ana, da zarar ka matsa za a zarce da kai ne shafin can na bogi da aka tsara, sannan a bukaci bayanan katin asusunka na banki (ATM Card) da lambar wayarka da sauran bayanai masu mahimmanci a rayuwarka.  Kafin kasan me ke faruwa, aikin gama ya gama.  Watakila bayan karanta wannan bayani kace, “To ai yanzu na waye, zan matsa in je can shafin in ga abin da ke faruwa.”  Wannan kuskure ne mai girman gaske.  Domin ba ka da aminci a hakan ma, kana iya zuwa ka rudu da irin tsarin da suka yi amfani dashi na yaudara.  Ka sani, mai son kayanka ya fi ka dabara.  Jama’a, mu fadaka!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.