Sakonnin Masu Karatu (2019) (20)

Rajistan Akwatin Imel

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na ranar Jumma’a, 22 ga watan Nuwamba, 2019.

70

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya ibada? Da fatan Allah ya karbi ibadarmu. Na yi rajistan akwatin imail na Gmail amma ba na iya buxe shi, kuma na shigar da komai daidai. Ina matsalar take? Daga A. A. Hashim. 08061308265

Wa alaikumus salam, Malam Hashim barka ka dai. A qa’idar mu’amala da kayayya da hanyoyin sadarwa na zamani, duk bayanin da ka shigar, to, sakamakonsa ne ake aiko maka a matsayin jawabi. Wannan qa’ida ita ake kira: “Garbage-in-garbage-out”, ko “GIGO” a gajarce. Abin da nake cewa a nan shi ne, muddin ka yi rajista ta hanyoyin da aka tanada, ba matsala. Sannan ka shigar da bayanan da kayi rajista dasu wajen buxe akwatin Imel din, su ma daidai kamar yadda ka ba da su a farkon buxewa, to, ban ga dalilin da zai sa a hana ka shiga ba. Domin ko da kulle akwatin suka sanadiyyar tsawon lokaci na rashin amfani dashi (wanda yanzu ma an daina rufe akwatin Imel don wannan dalili), to, za su sanar dakai cewa an rufe akwatin na wucin gadi. Wannan shi ake kira: “Deactivation of Account”, kamar yadda bankuna kanyi, idan ka dauki tsawon lokaci baka yi amfani da taskar ajiyarka ba.

A yanzu kamfanonin manhajar Imel na Intanet sun daina rufe akwatin Imel don rashin amfani dashi na tsawon lokaci. Don haka, ka bincika dai. Ina kyautata zaton dai akwai abin da baka shigar dashi daidai ba, musamman kalmar sirri, wato: “Password”. Amma a babin tunatarwa, idan tashi hawa akwatin Imel, za ka buxo manhajar ne idan ta wayar salula kake amfani, ko kaje shafin ta hanyar manhajar lilo, wato: “Browser” – Chrome, ko Edge, ko Opera dsr – ka shigar da adireshin: https://m.google.com. Nan take shafin da ake shigar da suna (username) da kalmar sirri (password) zai buxo. Sai ka shigar da sunan da ka bayar wajen yin rajista, sannan da ka kalmar sirrin da ka zaba a wancan wuri ko lokaci. Muddin ka shigar da komai daidai, za a zarce da kai akwatin Imel xinda kai tsaye. Idan hakan bai faru ba, to watakila ka mance kalmar sirrinka ne. Ga abin da zaka yi nan kasa:
A nan shafin shigar da suna daga kasa, ka duba zaka ga inda aka rubuta: “Forgot your password?”, ka matsa, shafi zai buxo inda za a tambayeka ka shigar da ranar haihuwarka wanda ka bayar sadda kake rajista. Sannan za a tambayeka kalmar sirri na karshe da kayi amfani dashi wajen hawa. Idan ba ka iya tunawa, ka sanya abin da kake da yakinin shine ka shigar. Idan bayanan sunyi daidai da abinda ka bayar, zasu baka damar canja kalmar sirrinka. Idan basu daidai ba, za a tambayeka lambar waya ko adireshin Imel din za a iya tuntuvarka don warware matsalar. Ba komai suke son yi ba illa don tantance ko kaine hakikanin mai akwatin Imel din. Idan sadda kake rajista baka ba da wani adireshin Imel ko lambar wayar da za a iya tuntuvarka ba, kuma a nan ka rubuta, to, za su ce ba kai bane mai akwatin Imel din, sai su rufe shafin su baka hakuri. Ba za kaji dadi ba saboda rashin biyan bukata, amma sunyi haka ne don kariya gareka.

Wannan shi ne dan abin da zan iya bayarwa na agaji. Ina maka fatan alheri kuma Allah sa a dace, amin. Na gode.

- Adv -

Salamun alaikum Baban Sadik, Allah ya kara basira. An sace min shafin Facebook dina watanni biyar da suka gabata. Na bi duk hanyoyin da zanbi amma na gagara gyarawa. Daga karshe sun ban wata uku cewa za su gyara mini, amma da suka saki shafin, iya sunana ne kawai ya dawo, da abokaina. Amma hotuna na basu dawoba. Shi ne nake tambaya ko akwai wasu hanyoyin da zanbi su dawo. Na gode. Daga: Ayuba Umar, Dutse, Jigawa: 08032702234

Wa alaikumus salam Malam Ayuba, da fatan kana lafiya. Lallai wannan abin a damu ne, kuma ruwan dare ne a Facebook. Kamar yadda suka maka alkawari kuma suka cika, sai dai ba yadda kaso ba, haka lamarin yake. Akwai dalilai kusan xari ba daya da suka sa hakan ke faruwa. Idan kaga an dawo maka da shafinka na Facebook amma babu wasu abubuwan naka, ko dai ya zama wani ne ya sace ko ya kwace shafin a farkon lamari, kuma ya goge maka waxannan bayanai naka. Wannan zai sa idan aka kwato shafin, ya zama ka rasa su.

Na biyu kuma ta yiwu sadda ya aka kwace shafin anyi amfani da bayanan dake kan shafin ta hanyoyin da suka saba wa ka’idojin Facebook. Wannan zai sa idan suka gane cewa ba laifinka bane, su dawo maka da shafin amma kuma su goge abin da ya saba wa qa’idarsu.
Don haka, tunda har ka rasa waxannan hotuna, babu wata hanya da za ka iya dawo dasu, sai dai ka sake dora su in har kana dasu a waya ko kwamfutarka. Domin duk abin da aka goge a shafin Facebook, babu wata hanya ta musamman da suka tanada don dawo dasu. Don haka ne ma yasa suka tanadi wata hanya da kowane mai shafi a Facebook zai yi amfani da ita wajen taskance dukkan bayanan da ke shafinsa. Ma’ana, za ka iya saukar da dukkan da bayanan dake kan shafinka na Facebook a kan waya ko kwamfutarka, don adana su. Sun yi haka ne don bacin rana. Shi yasa ma idan kayi yunkurin gogewa (Delete) ko rufe shafinka na Facebook (Deactivate) ta hanyar da suka tanada a vangaren tsare-tsare (Settings), kafin ka latsa mavallin gogewa sai sun tallata maka cewa ko za ka taskance bayananka kafin gogewa?

Wannan dan abin da ya samu kenan na Qarin haske. Allah qare gaba kuma yasa a dace. Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.