Hanyoyin da Kafafen Sada Zumunta Ke Samun Kudaden Shiga (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 16 ga watan Yuli, 2021.

340

Tsawon lokaci masu karatu basu gushe ba wajen tambayata kan wace hanya ce ko hanyoyi kafofin sada zumunta na zamani ke samun kudaden shigansu?  Galibin lokuta idan an mini wannan tambaya nakan ba da amsa a takaice ne, musamman idan ta hanyar sakon tes ne ko kuma ta shafin Facebook.  A yau in Allah Ya so zan yi bayani a fayyace; dalla-dalla, sanka-sanka kan wadannan hanyoyi.  Amma kafin nan, zan so mu fahimci tsarin samar da bayanai a shafukan Intanet, tsakanin jiya da yau. Wannan zai taimaka mana wajen fahimtar sauran bayanan da zasu biyo baya, cikin sauki.

Tsarin Samar da Bayanai a Intanet – Jiya da Yau

Akwai tsari biyu na samar da bayanai a giza-gizan sadarwa na Intanet.  Wadannan hanyoyin samar da bayanai dai, daya ne asali daga cikinsu, a yayin da dayar hanyar ta samo asali ne daga hanyar farko.  Ga bayanin kowanne daga cikinsu nan.

Bayanan Mai Shafi – “Owner-generated Content”

- Adv -

Hanyar farko ta samo asali ne daga farkon lokacin da aka samar da fasahar Intanet zuwa shekarun 1990s, galibin bayanan dake shafukan Intanet duk wadanda masu shafukan ne suka samar.  A wannan zamani, duk shafi ko gidan yanar sadarwa za ka ci karo dashi a Intanet a dauke yake da bayanan da asalin maginin shafin ko gidan yanar ya zuba. Idan shafin jarida ce, za ka tarar da labarun dake shafukan gidana yanar sadarwar duk na mai shafin ne, wadanda ya rubuta don labarta abin da ya gani.  Idan shafin sayar da kayayyaki ne, za ka tarar da bayanan hajojin da kuma hotunansu, duk na mai shafin ne. Galibin bayanan dake Intanet a wannan lokaci har wa yau, duk zallar rubutu ne, sai ‘yan hotuna da ba za a rasa ba.  Zuwa karshen shekararun 1990s ne aka samu ci gaban fasahar gina shafukan Intanet ta amfani da yaren JavaScript da Flash na kamfanin Macromedia.  Wannan yanayi ya samar da bayanai masu motsi na bidiyo ko flash da kuma sautuka da ake iya ta’ammali dasu a shafukan yanar sadarwa.  Har zuwa karshen shekarun 1990s, babu shafun sada zumunta irin wadanda ake dasu a yau.  Shafukan da suka shahara a wancan karo sune “Zaurukan Intanet” ko “Kauyukan Intanet” na kamfanin Yahoo! da MSN – irin su “Yahoo Groups”, da “MSN Groups”, sai kuma “Google Groups” da aka samar a karshe.  Dandalin sada zumunta da ya shahara, wanda ke kama da irin abin da muke dasu a yanzu, shi ne shafi ko dandalin “MySpace”, wanda a yanzu ya dade da macewa.

A wannan marhala na wanzuwar Intanet a duniya, bayanan dake shafukan Intanet ko gidajen yanar sadarwa, duk na asalin mai shafin ne; ba na masu ziyara ba.  Galibin masu ziyara sai dai suyi tsokaci kan abin da mai shafin ya rubutu ko wallafa a shafinsa.  Wannan tsari da nau’in bayanai shi ake kira: “Owner-generated Content”.

Bayanan Masu Ziyara – “User-generated Content”

Daga shekarar 2000 zuwa yau kuma, tsari da kintsin shafuka da fasahar Intanet sun canza matuka. An samu ci gaba wajen hikima da fasaha da tsarin aikawa da karban bayanai a giza-gizan sadarwa na Intanet, fiye da kowane lokaci a tarihin wannan fasaha.  Sai salon masu samar da masu bayanai ya canza daga ilmantarwa kadai zuwa kasuwanci da neman kudi.  Kuma tunda wannan fasaha ta Intanet an gina ta ne a turban ilimi wanda ingancinsa ya rataya ga ingancin bayanai, wannan yasa samuwa da bunkasar wannan salo ya habaka sosai.  Karkashin wannan tsari, galibin bayanan dake shafukan Intanet na masu ziyara ne, wadanda mai shafin ke basu damar samar da shafi na kansu, ya tanada musu abubuwan da za su yi amfani dashi wajen samar da bayanai.  A kan haka ne dandalin sada zumunta na wanna zamani suke gudanuwa.  Idan kayi rajista a shafin Facebook misali, da zarar ka hau shafinka, za ka tarar da komai kake bukata wajen samar da bayananka a nau’in zallan rubutu (Texts), ko hotuna (Images), ko bidiyo (Video) ko sauti (Audio).  Bayan haka, idan kana bukatar gina manhaja ta musamman da kake son wasu suyi amfani da ita, duk za ka iya hakan cikin sauki, muddin ka mallaki kwarewa kan haka.

Wanann tsari na bai wa mai ziyara damar samar da bayanai da kansa, shi ake kira: “User Content Style”, su kuma bayanan da aka samar dasu ta wannan hanya ana kiransu: “User-generated content”.  Kuma dukkan shafuka da dandalin sada zumunta na zamani – na kwamfuta da na wayar salula – an gina su ne karkashin wannan tsari.  Manufar yin hakan shi ne, tunda ra’ayoyin jama’a ne da kansu, wadanda ke bayyana hakikanin manufofinsu, to, amfani da wadannan bayanai da suka samar da kansu zai taimaka wajen samar da hajojin kasuwanci.  Domin ta wadannan bayanai ne ake sanin kasashensu, da manufofinsu na siyasa, da dandanonsu a rayuwa, da jinsinsu, da addininsu, da abin da suke so da wanda ba sa so.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.