Sakonnin Masu Karatu (2016) (8)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

91

Salaamun alaikum, barka da warhaka Baban Sadik.  Da fatan ka yi sallah lafiya.  Alla ya nuna mana na gaba da alheri, amin.  Ni makarancin jaridar AMINIYA ne ina kuma karanta shafinka na “Kimiyya da Kere-kere”.  Don Allah ina so kayi mana waiwaye kan bayanin jirgin ruwan RMS Titanic.  Na gode, Allah kara basira, amin.  Bello Kiyawa, Legas – 07032528895

Wa alaikumus salam Malam Bello Kiyawa.  Ai wannan kasida ta maimaitu a wannan shafi, tsakanin uwar kasidar da kuma tambayoyi da nayi ta amsawa kan wannan batu.  Abin da nayi a makon da ka turo wannan sako shi ne, waiwaye kan kasidun da suka gabata, da abin da muka karu dashi na ilimi.  Ba wai bitar kasidun muke yi ba.  Don haka, idan har kana bukatar sake karanta kasidar ne, kana iya turo adireshinka na Imel sai a cilla maka ita a ciki, ka karanta.

Ko kuma, idan kana dandalin Facebook kana iya tuntubata don sanar da kai yadda za ka samu kasidar a kan dandalin.  Ko kuma, a karo na karshe, ka hakura zuwa lokacin da zan gama gina shafin yanar sadarwa da nayi alkawarin a ciki zan zuba dukkan kasiduan da suka taba bayyana a wannan shafi.  Wannan gidan yanar sadarwa ne na kashin kaina da nake ginawa don wannan dalili.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah, shin, wani mataki ake bi don samun wadannan kammalallun kasidun da ka tura wa wasu bayin Allah, don ni ma ina son a tura mini.  Naka har kullum; Bashir Madaki: bashirmadaki1@gmail.com, 08092929735

Wa alaikumus salam Malam Bashir, barka ka dai.  Matakin guda daya ne ko biyu; ko dai ka aiko adireshinka na Imel in tunkuda maka kasidar da kake bukata na musamman, ko kuma idan na gama gina shafin yanar sadarwa da nake ginawa, sai ka shiga don daukan irin kasidar da kake bukata, kyauta.  Hanyar farko idan kana bukatar kasidar a yanzu kenan, don wata bukata ta musamman.  Sannan dole in san hakikanin kasidar da kake bukata.

- Adv -

Amma idan duka kasidun kake bukata, ko kuma na fannoni daban-daban kake so, ba tare da haddade yawa ba, wannan kam sai dai ka samesu a shafin idan an gama ginawa da kintsawa.  Domin bazai yiwu in iya tura maka kasidun duka ta Imel dinka ba saboda sun kusan 300.  Mizaninsu ma ya fi karfin yadda za a iya barina in tura su ta Imel.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya gida?  Don Allah me ake nufi da Wi-Fi kuma mene ne amfaninsa?  Daga Nura Buhari, Bodinga: 07033155737

Wa alaikumus salam Malam Nura, barka da warhaka.  Abin da Kalmar “Wi-Fi” ke nufi shi ne, “Wireless Frequency Radio,” kuma tsari ne dake killace a cikin yanayin sadarwa na zamani.  Idan kana son ganin wannan tsari a wayarka mai dauke da babbar manhajar Android, ka je: “Settings”, a bangaren “Network Connections” za ka ga wannan tsari, sai ka kunna shi.  Idan akwai na’urar Wi-Fi a inda kake, nan take wayarka za ta sanar da kai cewa: “Akwai tsarin sadarwar Intanet a nan, ta hanyar Wi-Fi.  Shin, kana a son a jona ka da shi?”  Idan kace eh, sai a jona ka.  To amma sai dai ba dukkan tsarin Wi-Fi yake kyauta ba.  Galibin wuraren da za ka je ka ci karo da wannan tsari za ka samu na wasu kamfanoni ne ko hukumar gwamnati, wanda dole sai an saita maka ta hanyar shigar da wasu kalmomi na sirri da suka kebanci kamfani ko hukumar da ke dashi.

Daga cikin amfanin tsarin “Wi-Fi” shi ne, kana iya jonuwa da yanayin sadarwa na Intanet a duk inda tsarin yake.  Haka idan kana na’urar Router, wacce ke dauke da wannan tsari a gidanka, kana iya amfani da tsarin a wayarka don amfani da Intanet ba tare da matsala ba, muddin ka sayi “Data” daga kamfanin sadarwar da ya sayar maka da na’urar “Router” din.

Bayan tsarin “Wi-Fi” da ake amfani da shi wajen hawa Intanet, akwai nau’I na biyu mai suna: “Wi-Fi Direct,” wanda ke taimakawa wajen aikawa da sakonni masu babban mizani, daga wayar salula zuwa wata wayar salular.  Misali, kana iya aikawa da sako na hoto ko bidiyo ko sauti mai mizanin 1GB, a kasa da minti biyu ko uku.  Galibi ana samunsa a wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Android.  Kuma shi kyauta yake, ba a bukatar biyan ko sisi ko sayan “Data”, domin an yi shi ne don aikawa da sakonni kai tsaye, a tsakanin wayoyin salula.   Kuma ko da babu katin SIM a wayar salula, kana iya amfani dashi.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.