Tsaga a Jikin Wata: Mu’jiza ko Yawan Shekaru? (3)

A kashi na karshe, kasidarmu ta dubi alakar dake tsakanin kimiyya da kuma mu’ujizar Annabawa ne. Sannan ta tantance hakikanin gaskiyar lamarin wannan hoto.

521

Alakar Kimiyya da Mu’jizar Annabawa

Wannan shi ya kawo mu ga duba alakar da ke tsakanin fannin kimiyya, wato Science a bangare daya, da kuma Mu’jizar Annabawa wato Prophetic Miracle, a daya bangaren.  Wannan sharhi ne zai iya taimaka mana wajen sanin tasirin abubuwan da ke faruwa a duniya ko a duniyar Wata, wadanda suka danganci tsarin kimiyya tsantsa, da kuma abubuwan da ke faruwa na mu’jiza da Annabawan Allah ke yi, wanda ya sha karfin fahimta da binciken duk wani mai bincike.  Hakan har wa yau zai iya taimaka mana wajen fahimtar tsaga da ke jikin Wata a halin yanzu: shin, tsaga ne na yawan shekaru, saboda tasirin muhallin da yake ciki, ko kuwa alamar tsagewar da ya taba yi ne sanadiyyar Mu’jizar Manzon Allah (SAW), lokacin da ya bashi umarni har ya rabe gida biyu a gaban kafiran Makka, suna gani?  Mu je kasar Siriya.

Dakta Muhammad Raatib Nablusi, daya cikin malaman kasar Siriya, ya kawo bambancin da ke tsakanin Kalmar “Sharhi ko Bayanin Tsarin Kimiyya” (Scientific Explanation), da “Mu’jizar Kimiyya” (Scientific Miracle), da kuma Kalmar “Mu’jizar Annabawa” (Prophetic Miracle).  Daktan yayi wannan sharhi ne cikin laccar da ya gabatar kan wannan lamari a shekarun baya.  A cewar Malamin, “Sharhin Tsarin Kimiyya” shi ne yin bayanin wani abu da ya auku a kimiyyance, a tsari ko al’adar rayuwa.  Ire-iren wadannan sun hada da ruwan sama, da yadda yake samuwa, da tsarin rayuwar taurari, da zazzabin Wata ko Rana (Moon/Solar Exclipse) da dai sauran makamantansu.  A samu masanin kimiyya yayi sharhi kan yadda wadannan abubuwa ke yiwuwa ko faruwa, shi ake kira “Sharhin tsarin Kimiyya.”  Dakta Ratib ya kawo wasu misalai da kowa zai iya fahimta cikin sauki.  Da farko yace lokacin da Ibrahim, dan Manzon Allah (SAW) ya rasu a Madina, daidai lokacin ne aka samu  yanayin kisfewar rana ko husufin rana a takaice.  Sai mutane suka kama surutu suna cewa rana tayi husufi ne sanadiyyar rasuwar wannan jariri.  Nan take sai Manzon Allah (SAW) ya  mike ya fahimtar dasu abin da ya faru.  Cewa da Rana da Wata duk ayoyin Allah ne; basu yin husufi don rayuwa ko mutuwar wani.  Abin da Manzon Allah (SAW) yayi a nan shi ne “bayani ko sharhin tsarin kimiyya”.  Ma’ana, wani abu ne da ke faruwa lokaci-lokaci, sanadiyyar tsari da yanayin da Allah ya dora duniya a kai.  Ba wai karama bace ko mu’jiza ta musamman.

Misali na biyu shi ne wani abin da ya faru dashi Daktan, lokacin da yaje yin umara a Makka.  Yana isa Makka, sai yaji wasu mutane suna cewa idan yamma tayi, magriba ta gabato, wani haske na hudowa daga saman kabarin Manzon Allah (SAW) a Madina, zuwa sama.  Wannan haske, a cewar masu bayar da wannan labari, mu’jizar manzon Allah ce mai tabbatar da darajarsa har yanzu.  Bayan ya gama umara, sai ya wuce Madina don yin ziyara.  Yana shiga masallacin, daidai lokacin sallar magriba, sai ya tarar wani malami na gabatar da karatun fikihu a masallacin, kamar yadda aka saba.  Yace bayan malamin ya gama karatu, sai yayi sanarwa cewa, sun yi hira da Sarkin Madina, inda Sarkin ya sanar dashi cewa hukumar Saudiyya ta sanya wata fitila mai haske, mai kuma dauke da sinadaran haske nau’in Laser, wadda ke cillawa cikin Sararin Samaniya, don ya zama alama ga direbobin jirgin sama a lokacin da suke halin tafiyarsu a sama.  Da zarar sun zo wajen wannan haske, zasu kauce, don kada su wuce ta saman kabarin Manzon Allah (SAW).  Wannan, a cewar Dakta Ratib, sharhin kimiyya ne yaji a bakin wannan malami.  Ma’ana ba mu’jiza bace, sabanin labarin da yaji a Makka.

Kalma ta biyu, wato “Mu’jizar Kimiyya” (Scientific Miracle), shi ne faruwar wani abu a kimiyyance, wanda ba a iya gane tasirin abin ko hikimar da ke tattare cikinsa sai bayan bincike ko lokaci mai tsawo.  Ma’ana, ba wani abu bane da kowa zai iya ganewa ba nan take, sai wadanda suka shahara a fannin kimiyya, kuma sai bayan lokaci da bincike mai tsawo.  Misali, a cikin hadisan Manzon Allah (SAW) an nuna cewa idan kuda ya fada cikin abinci ko abin sha, to a dulmuya shi cikin abin da ya fada ciki baki daya, sannan a ciro shi a yar.  Domin a dayan fiffikensa akwai cuta, wacce da ita yake fadawa cikin duk abin da zai fada.  A daya fiffiken kuma, wacce yake dage ta sama, akwai maganin wannan cutar.  Kenan idan aka dulmuya shi baki daya, anyi maganin cutar kenan.  Hadisi irin wannan, da sauran makamantansa, ba kowa ke iya hararo gaskiyar abin da aka fada ba, sai wanda ya gabatar da bincike na musamman kan hakan, bayan lokaci mai tsawo.  Amma a lokacin da aka fade su, sai dai ayi imani dasu kawai.  Wannan mu’jiza ce ta kimiyya wacce ta sha karfin tunanin dan Adam sai bayan lokaci mai tsawo yake gano tabbacin hakan.

Misali na biyu kuma shi ne, akwai lokacin da wasu mahaya kumbo suka haura can saman Sararin Samaniya, ma’ana suka ketare dukkan iskar da ke saman wannan duniya mai tazarar kilomita sittin da hudu (64km).  Suna gama wuce wannan tazara, sai suka shiga yanayin da basu ganin komai sai duhu.  Nan take daya daga cikinsu yace: “mun makance; bamu gani”.  A daidai wannan lokaci da yake sanar da masu lura da tafiyarsu a tashar da suka baro a duniya, sai aka yi dace akwai wani Balaraben kasar Masar masanin Kur’ani kuma masanin Kimiyyar Sararin Samaniya a wajen.  Yana jin haka, sai yace musu “wannan Mu’jizar Kimiyya ce”.  Da aka tambaye shi me yake nufi da hakan, sai yace ai Allah Ya fadi hakan cikin Kur’ani, inda yake cewa: “…kuma da mun bude wata kofa daga sama a kansu har suka wuni a ciki suna takawa (zuwa sama).  Lallai ne da sun ce, “ai ba abin da aka yi sai rufe mana idanu kawai.  A a, mu mutane ne da aka sihirce.” (Suratul Hijri: 14-15).  Me ya faru?  Wannan bawan Allah dan kasar Masar ya tuna cewa, da zarar ka wuce sararin wannan samaniya tamu bayan tafiyar tazarar kilomita sittin da hudu, to ba abin da zaka samu sai duhu mai tsanani.  Wannan tasa wancan bawan Allah da ke cikin kumbo yace “mun makance”, saboda sun daina ganin haske.  Daman iskar da ke sararin wannan duniya ce ke rarraba hasken da ke zuwa daga jikin rana.  Wannan tsari, wanda ake kira Scattering of Light a Kimiyyar Sararin Samaniya, yana samuwa ne a tazarar tafiyar da bata wuce kilomita sittin da hudu ba daga doron kasa.  Da zarar ka wuce wannan tazara, ba abin da ya saura sai duhu.  Wannan misali na biyu na nuna mana ne karara, cewa Allah ya tabbatar a Kur’ani cewa da za a bude wa kafirai wata kofa zuwa sama suna ta tafiya a cikinta, zasu kai wani tazara da zasu daina ganin haske.  Wannan zai sa su ce, “lallai sihiri aka mana”.  To amma a lokacin tunda ba a yi haka ba, babu wanda zai iya tabbatar da gaskiyar hakan.  Sai bayan shekaru sama da dubu daya aka samu bincike da ya tabbatar da hakan.  Wannan, a cewar Dakta Ratib, “Mu’jiza ce ta Kimiyya”.

- Adv -

Sai kalma ta uku, wato “Mu’jizar Annabawa”. Kalmar mu’jiza asali kalmar larabci ce, wacce Hausawa suka aro don nufin abin da take nufi a larabce, ma’ana: “wani abin da ya sha karfin tunani da hankalin dan Adam; ya gagare shi wajen karfi ko tunani”.  Mu’jiza sifa ce ta Annabawa, su kadai Allah ke ba wannan baiwa don gamsar da mutanensu cewa daga Allah suke, ba su suka aiko kansu ba.  Misalin mu’jiza na nan barkatai.  Akwai sandar Annabi Musa (AS), wacce ke zama macijiya, akwai taguwar Annabi Salihu (AS), da dai sauransu.  Mu’jizar Manzon Allah (SAW) mafi girma ita ce littafin da Allah Ya aiko shi da shi, wato Al-Kur’ani mai girma.  Sannan akwai Isra’i da Mi’raji da Allah yayi dashi zuwa saman sama na bakwai.  Dukkan wadannan mu’jizozi ne wadanda suka sha karfin wani dan Adam ya iya bayanin yadda suka auku. Misali, babu wani Malamin Kimiyyar Sararin Samaniya da ya isa yayi bayanin tsarin tafiyar da Manzon Allah yayi daga Masallacin Baitul Makdisi zuwa sama, a kimiyyance.  Wannan, a turance, shi ake kira Prophetic Miracle.  A wannan tsari, duk abin da ya faru na mu’jiza a kimiyyance (kamar tafiyar da Manzon Allah yayi zuwa sama), abu ne da ba wanda zai iya fahimtar yadda abin ya faru, kuma ba lale bane a ga wani gurbi bayan faruwar mu’jizar.  Misali, akwai lokacin da Manzon Allah (SAW) ya sunkuyar da yatsan hannunsa kasa, ruwa yayi ta zuba sahabbai suna sha, wusa na alwala da ruwan.  Hakan ya faru ne lokacin da aka je daya daga cikin yake-yaken da aka yi, inda aka yi karancin ruwa.  Bayan kowa ya gama amfana da ruwan, sai Manzon Allah (SAW) ya yarfar da yatsansa, ruwan ya dauke.  Wannan abu da ya faru bai sa an ga wata alama ko huji a yatsansa ba, saboda “mu’jiza ce ta annabta”, ba wani abu bane da ya saba faruwa ga mutane a al’adance.

Tantancewa Tsakanin Hujjoji

Daga bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa tsagewar Wata mu’jiza ce ta Annabta, ba wai mu’jiza ta Kimiyya ba.  Domin babu wanda zai iya gano yadda tsagewar ta  kasance, balle ya san kimar abin.  To amma kuma meye alakar hakan, da wannan hoto da ake ta yadawa?  A iya karatu da bincike na, idan ka dauke wancan labari na Dawood Mousa Biskok, inda wadancan masana Kimiyya suka tabbatar da cewa an gano alamar tsagewar Wata a wasu lokuta ko shekaru masu yawa da suka wuce a rayuwarsa, babu wani bayani na kimiyya tabbatacce da ke nuna gaskiyar abin da wannan hoto ke dauke dashi, duk kuwa da shahararsa.  Sabanin haka ma, abin da galibin bayanai ke tabbatarwa a kimiyyance shi ne, galibin tsage-tsagen da ke jikin Wata a halin yanzu, sun samo asali ne daga yawan buraguzan taurari masu tarwatsewa suna afkawa cikin wasu duniyoyin da ke makwabtaka dasu.  Ire-iren wadannan buraguzai su ake kira Meteriote a turance.  Don haka tsagar da ke jikin Wata, ko kadan, bata da alaka da wannan lamari na mu’jiza.

Bayan haka, malaman kimiyya sun kimanta zurfin tsagar da ke jikin Wata a halin yanzu da cewa ta kai tafiyar nisar kilomita dubu goma sha uku.  Amma idan muka dubi hoton da ke like a nan, za mu ga cewa alamar da ke jikin Watan, ko kadan bai shiga ciki ba.  Kamar ma zane ne kawai, ba tsaga ba.  Har wa yau, wannan hoto, idan muka dube dashi da kyau, karshenta ma wani ne ya zauna ya zana shi da manhajar zane na kwamfuta, wato Graphics Software, bayan wancan labari da masana suka bayarBa lale bane ya zama hoto ne na gaskiya da aka dauko daga can ba.

A karshe kuma idan aka ce abu kaza mu’jiza ce, to akwai siffofi guda uku da suka kamata a gane hakan.  Na farko shi ne ya zama ya sha karfi da tunanin mutane, babu wanda zai iya yin shi duk cikin mutane sai Annabi ko wani Manzo da Allah ya aiko.  Idan muka dubi tsagewar Wata, za mu ga haka ne.  Na biyu kuma ya zama babu wani zamani da za a kaiwa, ko mataki na ilimi, da wani zai ce ya gano wani abu daban cikin abin da ya faru, sabanin abin da ya faru din.  Abu na karshe kuma, wanda ke da nasaba da wannan hoto shi ne, ba ka’ida bace cewa idan mu’jiza ta auku kan wani abu, dole sai an samu alama bayan aukuwarta.  Kamar yadda ba a samu Wata alama ba a yatsar Manzon Allah (SAW) bayan bubbugar ruwan da ya faru, kamar yadda bayani ya gabata a kai.  Don haka ba dalili bane cewa don an ce an samu alama a jikin Wata, wani yace “dole ne ya zama alamar tsagewar da yayi ne lokacin Manzon Allah (SAW)”.  Ba hujja bace wannan.

Kammalawa

A karshe dai, ma iya cewa wannan hoto bai da alaka da rahoton binciken da wannan hukuma ta NASA tayi, shekaru sama da arba’in da suka gabata.  Ta yiwu wani ne ya zauna ya zana hoton, don suranta abin da wadancan masana suka tabbatar a hirar da talabijin BBC yayi dasu a shekarar 1978.  Sannan ba hujja bace cewa lallai alamar da ke jikin Wata ta samu ne sanadiyyar tsagewar da yayi lokacin Manzon Allah (SAW).  Domin ba ka’ida bace cewa idan mu’jiza ta auku dole sai an samu alama a gurbinta.  Tabbas Allah na iya tabbatar da wannan alama a jikin Wata, amma ba dole bane sai an samu alamar sannan abin da ya faru zai zama gaskiya.  Wannan mu’jiza da ta auku: ko da alama ko babu wata alama a jikin Watan, mu munyi imani da aukuwarta.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.