Me Ka Sani Kan Motoci Masu Amfani da Makamashin Lantarki? (3)

A yau ga mu dauke da ci gaban fassarar kasidar Steve Dent kan motoci masu amfani da makamashin lantarki.  Wannan shi ne kashi na karshe. Da fatan an amfana daga bayanan da suka gabata.

438

Me Zai Sa In Damu?

Nau’ukan motoci masu amfani da man fetur ko gas sun taimaka matuka wajen dumama yanayi, da gurbata manyan tekunan duniya, tare da samar da kazanta mai muni ga lafiya a mahalli.  Ire-iren wadannan motoci har wa yau sun dada taimakawa wajen sa kasar Amurka dogaro kan man fetur da gas, da sayo su daga wasu kasashe da a halin yanzu kasar ke zaman doya da manja dasu.  Idan wannan zance bai sa ka damu ba saboda rashin damuwarka da siyasar duniya, duk da haka, wadannan sababbin nau’ukan motoci masu rage dumamar yanayi (irin masu amfani da makamashin lantarki zalla ko hadakarsa da gas) suna da karin fa’ida masu dimbin yawa.  A halin yanzu akwai nau’ukan motoci masu amfani da hadakar makamashin lantarki masu saukin farashi idan ka gwama su da nau’ukan motoci na gama-gari (masu amfani da man fetur ko gas zalla).  Haka alkaluman bayanai suka tabbatar daga ofishin Hukumar Makamashi na kasar Amurka.  Bayan haka, hatta wajen karfin sauti nau’ukan motocin zamani masu amfani da makamashin lantarki zalla sun fi dadin sha’ani.  Domin ba su da inji mai kona mai sannan ba su da nauyi.  Don haka injinsu ba shi da kara sosai idan ka kwatanta da na gama-garin motoci masu injin da ke kona man fetur ko gas zalla.  Hatta sinadarin da ake amfani dashi wajen kera gabansu ba shi da nauyi.  Sannan ko da hatsarin taho-mu-gama aka yi (gaba da gaba), ba za a samu salwantar rayuka ba, saboda gaban motar ba shi da nauyi; fako-fako ne.  Kuma kana iya tuka ire-iren wadannan motoci ko da kai kadai ne a ciki, akan titin da aka tanada wa motoci masu dauke da fasinja masu nauyi (High Occupancy-Vehicle Lane).  Doka ta yarda da haka ga masu wadannan nau’ukan motoci.

Duk da cewa wadannan motoci suna da dan karen tsada (musamman batiransu), wanda hakan ke hana galibin masu mallakansu iya ajiya da adashi, sai dai a daya bangaren kuma, akwai tallafin haraji (Tax Credit) da gwamnati ke bayarwa ga masu mallakar wadannan motocin.  Misali, gwamnati na bayar da tallafin haraji na kusan kimanin dalar Amurka dubu bakwai da dari biyar ($7,500) ga duk wanda ya mallaki nau’in Chevy Volt.  A wasu jihohi irin su Kalfoniya, masu mallakar motoci masu amfani da makamashin lantarki zalla na samun tallafin haraji na dala dubu biyu da dari biyar ($2,500), yayin da masu mallakar nau’in da ke amfani da hadakar lantarki da gas ke samun tallafin dala dubu daya da dari biyar ($1,500).  Wannan tallafi na jiha kari ne kan tallafin tarayya da hukuma ke bayarwa.  Har wa yau, farashin nau’in Nissan Leaf ya kai dala budu talatin ($30,000), amma da zarar an zaftare tallafin harajin da hukuma za ta ba mai saye, sai farashin ya sauko zuwa dala dubu ashirin ($20,000) kacal.

Kari a kan haka, kamfanin Nissan yace duk wanda ya mallaki wannan mota mai amfani da hadakar lantarki da gas, zai samu rahusar kudin gas wajen dala dubu hudu ($4,000), wanda hakan ya kara rage farashin motar daga dubu talatin zuwa dubu goma sha shida.  Wasu kan ce: ai inda gizo ke sakar shi ne wajen rike motar da kulawa da ita.  Eh to, wannan kuma wani abu ne da ba wanda zai iya cewa komai a kai, tunda ire-iren wadannan motoci basu dade a kan titi ba.  Amma abin da yake bayyane shi ne: suna da saukin mu’amala, don haka ana sa ran su zama masu sauki wajen kula da tafiyar dasu.

A Ina Matsalar Take?

- Adv -

Akwai wasu ‘yan abubuwan lura ga nau’ukan motocin da ke amfani da zallan lantarki da masu hadakar lantarki da gas.  Na farko dai baturan ba su dawwama.  Na biyu kuma suna da dan karen tsada idan aka tashi canza su.  Ba nan kadai ba, kwangirin da ke dauke da batiran nau’in Nissan Leaf, wanda ke baiwa batiran kariya daga zafin mahalli ya kai dala dubu biyar da dari biyar ($5,500) a misali, a yayin da batiran nau’in Tesla S kadai suna tsakanin dalar Amurka dubu goma sha biyu ne zuwa dubu goma sha biyar ($12,000 – $15,000).  Dukkan wadannan batiran, duk da tsadarsu, garantin shekaru takwas ne kacal dasu, kuma karfin cajinsu na raguwa ne iya tsawon zamani da aka dauka ana amfani dasu.  Sannan dukkan nau’ukan biyu har yanzu suna da tsada, duk da cewa ingancin kirarsu bai kai farashin da ake basu ba a yanzu.  A karshe, nau’ukan dake amfani da cibiyar samar da makamashin lantarki mai dogaro da sinadaran kol wajen cajin batiransu, su ma an gano suna taimakawa wajen dumamar yanayi.

A halin yanzu an fara samun faduwar farashin batiran wadannan motoci sanadiyyar yawaitarsu a kan tituna.  Haka ma tsarin lura dasu.  A nashi bangare, kamfanin Tesla ya sha alwashin rage farashin batiran nau’in Tesla S zuwa dala dubu takwas ($8,000) ko kasa da haka, da zarar ya gama gina tafkeken masana’antarsa da yake ginawa ta hadin gwiwa da kamfanin Panasonic.  Sannan nan kusa ana sa ran fara samar da sinadarin Lithium anode wajen kera batura masu inganci, wanda hakan zai dada rage farashinsu da nauyinsu.  Domin manyan dalilan da suka taimaka wajen yaduwar wadannan nau’ukan motoci, tare da saukin farashinsu duk bai wuce dokoki da hukuma ta samar ba wajen lura da kamfanonin dake kera su, da tallafin haraji da take bayarwa, sai kuma gasa da aka samu a kasuwar. Wadannan abubuwa duk sun dada taimakawa wajen samar da kayatattun motoci.  Nan gaba farashinsu zai kara sauka warwas, ta yadda gwamnati za ta dauke tallafin da take bayarwa, har motocin su yadu kowa ya iya mallakarsu cikin farashi mai rahusa.

Me Kake Nema Kuma?

A yanzu zai yi wahala ka shiga giza-gizan sadarwa na duniya (Internet) har ka fita baka ci karo da wani gidan yanar sadarwa da ke bayani kan wadannan nau’ukan motoci ba.  Duk da yake akwai shahararru daga cikinsu, wadanda suka yi fice a fannin.  Akwai Mudawwanar Autoblog wacce ke zazzage bayanai kai dukkan nau’ukan motoci masu amfani da makamashin lantarki zalla da masu hadakar lantarki da gas.  Sannan akwai gidan yanar sadarwar Green Car Reports, da Clean Technica, da kuma Hybrid Cars.  Galibin kamfanoni masu kera ire-iren wadannan motoci suna kera masu amfani da makamashin lantarki zalla da masu amfani da hadakar lantarki da gas.  Amma wadanda suka fi shahara daga cikinsu su ne nau’in: Nissan Leaf, da Ford Focus Electric, da Fusion Hybrid SE, DA Chevy Volt, sannan da nau’in Tesla Model S.  Ga duk mai bukata, yana iya shiga gidajen yanar sadarwar wadannan kamfanoni don duba wacce ta masa.  Ko kuwa?


Steve Dent masani ne kuma mai sharhi a kan hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani, musamman a shafin Endgadget dake endgadget.com

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Yahuza Idris says

    Allah ya saka da alherinsa

Leave A Reply

Your email address will not be published.