Gaskiya da Gaskiya (14): Idan Bera da Sata…(4)

Wannan shi ne kashi na karshe a jerin tunatarwa kan gyara halaye don samun ci gaban kasa mai kyau.

205

A baya na nuna mana cewa tabbas, muddin muna bukatar shugabanninmu su gyaru, dole ne mu ma mu gyaru, tsakani da Allah, ba gyaruwar muzuru ba. Na fadi haka ne cikin kashi na 17 a wannan silsila da muke ciki, a farkon shekarar 2015. Rashin azamar gyaruwa daga gare mu na cikin dalilan dake sa mu zauna, ba mu da aiki sai fadan aibun shugabanninmu. Wannan shi ne abin da za mu duba a wannan kashi cikin yardar Allah!

———————-

Gab da karshen shekarar 2014 in ban mance ba, na raka iyalina kasuwar Bacci dake garin Kaduna, don karba da sayan wasu kayayyaki na maslahar rayuwa. Daga nan nace bari in dan leka shagunan masu sayar da littattafan addini, don neman littafin “Sharhus Sunnah” na Imamul Barbahaari, wanda Sheikh Fawzaan bin Saalih Al-Fawzaan yayi wa ta’aliki cikin halkoki 25.

Ina doso shagunan, sai na masu ‘yan uwana masu shagunan dake wajen kowa ya fito bakin kofar shagonsa, kamar yadda suka saba. An zauna – wasu na tsaye – ana ta muhawara kan girman munin karatun Suratul Fatiha da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo yayi, wanda ake ta yawo dashi tsakanin wayoyin salula da shafukan zumunta na Intanet, cikin izgili da raha. Kusan kashi 99 cikin 100 na masu sauraro da yada wannan karatu suna hakan ne don nuna aibu da nakasu ga mai karatun!

- Adv -

Amma cikin jarabawa ta Ubangiji, sai wani daga cikinsu ya dubi sauran yace, “Yanzu ma karshenta duk wannan abin da ake, watakila ya fi wasu daga cikinmu ma iya karatu.” Sai wanda yafi kowa zakewa daga cikinsu yace, “Haba dai, bazai yiwu ba.” Sai dayan yace, “Ba mamaki ma ya fi ka iya karatu.” Sai mai zakewar yace, “Allah tsare, ko kadan.” Sai sauran jama’an wurin suka ce, “To karanto mana Fatihar mu ji.”

Ina tsaye a shagon mai littattafai ina jinsu, wasunsu ma na kallona, suna murmushi. Bude bakinsa ke da wuya da fara karatu, sai ya bayyana a fili cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa ma ya fi shi iya karatu da wajen kashi 100!!! Kafin ya kare surar, sauran suka fashe da dariya. Suka ba ga irinta nan ba, ashe ma ya fi ka iya karatu. Sai kawai yayi turus!

Jama’a, kafin mu shagaltu da aibukan wasu, mu dubi aibobin tukum! Kuma mu sani, shugabanninmu na da hakki a kanmu na mu musu adalci wajen magana, ko da ba musulmai bane, sannan mu kiyaye musu mutuncinsu, kamar yadda yake wajibi mu kiyaye mutunci da martabar gama-garin mutane musulmi.

DUK WANDA YA SHAGALTU DA FADIN AIBUN WANI, TO, A KARSHE SAI YA SAMU KANSA CIKIN MAFI MUNIN DABI’A FIYE DA NA WANDA YAKE AIBANTAWA.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.