Fa’idojin e-Naira Ga Tattalin Arzikin Kasa (3)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 15 ga watan Oktoba, 2021.

679

Mece ce Fa’idar Samar da eNaira?

Fa’idojin da za a samu sanadiyyar samar da wannan nau’in kudi dai suna da yawa, sun hada da fa’idojin da daidaikun mutane zasu samu da kuma wanda zai game kasa.  Abu ne sananne cewa duk wani sabon abin mu’amala da ya bayyana cikin al’umma, musamman wanda hukuma za ta samar, an kirkireshi ne don samar da wata fa’ida ta musamman.  Wannan bai hana a samu wasu kalubale wajen amfani dashi.  Amma fa’idar za ta fi gamewa, domin ita ce asali.  Ga kadan daga cikin muhimman fa’idojin da samar da wannan sabon nau’in kudi zai samar, a jimlace:

Rage Kashe Kudin Buga Takardun Kudi

Na farko, fara amfani da eNaira zai rage yawan kudaden da babban bankin Najeriya (CBN) ke kashewa wajen buga takardun kudade.  Domin ba karamin kudi ake kashewa ba a duk sadda aka tashi buga sababbin kudade, musamman don maye gurbin wadanda bankin CBN ke Konawa sanadiyyar lalacewa da suka yi.  Da kuma kudaden da ake bugawa don cike gibin matsalolin da ake samu wajen tafiyar da tattalin arzikin kasa.  Amma bayyanar eNaira zai rage adadin kudaden nesa ba kusa ba.  Domin galibin kudaden za a ci gaba da amfani dasu ne ta hanyar kafafen sadarwa na zamani, musamman wayar salula.  Shekarar da na ziyarci kasar Amurka don wancan taro da na ambata a farko, na hadu da wani bature dan asalin kasar da yace mini, shi har ya mance sadda ya rike takardar kudi ma a hannunsa.  Katinsa kawai yake fita dashi. Dashi yake sayan duk abin da zai saya; ba ya bukatar rike takardar kudi.  Mu a nan Najeriya za mu ga kamar abu ne mai wahala hakan ya faru a kasarmu.  Amma nan gaba, sadda za mu shiga wancan yanayin ma ba za mu sani ba.  Ma’ana, rike takardun kudi zai ragu matuka.

Rage Sace-Sacen Takardun Kudi

Fa’ida ta biyu ita ce, samar da wannan nau’in kudi zai rage yawan sace-sacen takardun kudade wanda barayi da ‘yan fashi ke yi a gidaje, da tituna.  Kuma ko da an sace maka wayar salularka, bazai yiwu wani yayi amfani da ita wajen aika kudaden eNaira dake taskarka zuwa wata taska ba, sai da taimakonka.  Domin akwai kalmomin sirri da dole a shigar dasu a yayin da aka tashi aika kudaden.  Kuma wadannan kalmomi ba irin wadanda kake amfani dasu bane wajen hawa Imel ko Facebook dinka, a a.  Kwamfuta ce ke samar maka dasu, don ka aiwatar da hada-hadar kudi a taskarka.  Ka ga kenan, sai idan kaine ka bashi.  In kuwa ba haka ba, ya saci banza.

- Adv -

Rage Yawan Jabun Takardun Kudi

Abu ne uku shi ne, samar da eNaira zai rage yawan jabun kudade a cikin kasa.  Domin eNaira ba a yanayin takarda yake ba, sannan ko ta hanyoyin fasahar sadarwa, ba za a iya kirkirar jabunsa ba.  Wannan ita ce siffar da ta sa nau’ukan kudaden Intanet, wato: “Cryptocurrencies” suka zaka gagarau.  Dokin magudanar da ake amfani da ita wajen samar dasu, tana cike ne da tsaro mai tsauri, kuma ka’idojin dake tattare da ita suna tsauri su ma.  A takaice dai, a halin yanzu wannan ita ce hanya mafi aminci da tsaro wajen aikawa da karban kudade masu yanayi irin wannan.  Jabun takardun kudade zasu ragu sosai, domin adadin masu rike takardun kudi zai ragu.

Karanci ko Rashin Caji

Mafi yawancin abin da mutane ke korafi a kai, dangane da bankunan kasuwanci, shi ne yawan caji marasa kangado da ake musu daga taskar ajiyarsu.  Karkashin wannan sabon tsari na eNaira, babu caji da banki zai cira ko karba daga gareka idan ka tashi aika kudi daga taskar bankinka zuwa taskar eNaira dinka, wato: “eNaira Wallet”.  Kamar yadda babu wani caji da za a cira idan ka tashi aika kudade daga taskar eNaira dinka zuwa taskar ajiyarka ta banki.  Wannan ya shafi daidaikun mutane da ma kamfanoni da ‘yan kasuwa.  Wannan zai taimaka wajen rage kudaden da masana’antu da kamfanoni da ‘yan kasuwa ke kashewa a wannan bangare, kuma hakan zai kai ga rage farashin hajojin ko kayayyakin da suke sayarwa.

Rage Hauhawan Farashin Kayayyaki

Dalilan dake sa farashin kayayyaki ya haura a Najeriya suna da yawa, ciki har da karancin kwandala (kwabbai da silalla kenan – Coins).  Shi yasa yanzu da wahala ka samu wata haja da ake sayar da ita naira 3, ko naira 8, ko naira dubu da kwabo ashirin (N1,000.20k).  A takaice dai, farashin kayayyaki a Najeriya daga naira 5 ne, sai 10, sai 15, sai 20, ko 100 misali.  Ba ka samun farashi mai dauke da silalla, ko kwabbai.  A tare da cewa har yanzu suna nan a matsayin kudaden Najeriya.  Dalilin shi ne, an daina amfani da kwandala.  Samuwar tsarin eNaira zai dawo da wadannan nau’ukan kudade cikin farashin kayayyaki.  Kuma zai taimaka wajen rage musu tsada, ta wannan bangaren kenan.  Misali, idan dan kasuwa ya sayo kaya naira 75, karkashin tsarinmu na yau, kuma yana son cin ribar naira 3 ne ko naira 2.  Wanda hakan zai sa farashin kayan ya koma naira 77 ko 78.  To amma sanin cewa babu kwandala, wannan zai tilasta shi ya daga farashin zuwa naira 80.  Ka ga an samu karin farashi, sanadiyyar karin naira 2 ko 3 da yayi.  Amma a tsarin eNaira, zai iya barin farashin a naira 77.  Idan ka tashi biyansa kawai cikin sauki za ka iya aika masa da naira 77 ta taskar ajiyarka ta eNaira.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.