eNaira: Hanyoyin Mallakar e-Naira (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 8 ga watan Oktoba, 2021.

1,711

Ta Wace Hanya Zan Iya Mallakar eNaira?

Wannan sabon tsari yana dauke ne da manyan matakai guda biyu.  Matakin farko shi ne ya kunshi alaka ne tsakanin babban bankin Najeriya (CBN) da sauran bankunan kasuwanci (Commercial banks).  Mataki na biyu kuma tsakanin bankunan kasuwanci ne da masu ajiya.  A matakin farko, bankin CBN zai baiwa bankunan kasuwanci damar isa ga tsarin, tare da bude musu asusun ajiyarsu ta Intanet (eNaira Wallet), wanda ke dauke da adadin abin da suka saya na eNaira.  Karkashin wannan tsari ne zai basu damar bude wa masu ajiya dasu asusunsu su ma, da basu damar iya saya musu nasu nau’in eNaira din, ta amfani da babbar magudanarsa (CBN Blockchain).

Sai mataki na biyu, wanda zai kasance tsakanin bankunan kasuwanci da masu ajiya.  A wannan matakin, bankunan kasuwanci za su yi mu’amala ne da nau’in mutane biyu.  Na farko su ne masu taskar ajiya a bankunansu.  Na biyun kuma wadanda ba su da taskar ajiya a kowane banki.

Idan kana da taskar ajiya a bankinka, da zarar an fara amfani da wannan tsari, bankinka zai aiko maka sako ta lambar wayarka, ko akwatin Imel dinka.  Sakon na dauke ne da adireshin da zaka bi, don saukar da manhajar da zaka yi amfani da ita wajen bude taskar ajiya ta magudanar bankin CBN (CBN Blockchain), wato: “eNaira Wallet”. A wannan taska ne za ka rika karba da aika nau’in kudin eNaira, kai tsaye.  Da zarar ka bude taskar, kana iya loda kudi daga taskarka mai dauke da takardun kudi, zuwa taskarka mai dauke da eNaira, kai tsaye, kuma a kyauta – babu wani caji.  Misali, idan kana da taskar ajiya a GTBank, ko Jaiz Bank, kuma kana son aika naira N20,000 zuwa sabuwar taskarka ta eNaira, sai ka hau taskarka ta amfani da manhajar bankinka ko ta amfani da lambobin USSD ta wayar salula, ka aika kai tsaye, babu wani jinkiri.  Da zarar ka aika, nan take kudaden zasu shiga taskarka ta eNaira.  Daga nan kana iya amfani da wadannan kudade wajen aika wa wani mai taskar eNaira, ko ka sayi kayayyaki dasu kai tsaye a shagunan saye da sayarwa na Intanet (Internet online stores).

Idan kuma ba ka da taskar ajiya da wani banki, kana iyan amfani da lambar wayarka mai rajistar NIN (lambar katin shedar kasa – National Identity Number) wajen sayan eNaira kai tsaye, idan adadin kudaden da kake bukata bai shige N50,000 ba a yini.  Tsare-tsaren da zasu sawwake faruwan hakan, tare da ka’idoji da kuma lambobin da za a yi amfani dasu wajen yin hakan, duk zasu zo a fayyace nan kusa.

Yaya Karbuwan Wannan Kudi Yake  A Duniya?

- Adv -

Ba ka da matsala wajen hakan.  Yadda takardar kudin Najeriya take halattacciya kuma amintacciya wajen kasuwanci, haka wannan nau’in kudi na eNaira yake halattacce.  Da zarar ka loda wani adadi na kudi a taskar “eNaira Wallet”, za ka iya aiwatar da cinikayya dashi kai tsaye, a kowane shagon sayar da kayayyaki.  Ko da kuwa farashin hajar na wata kasa ce daban.  Wannan ba damuwa bane.  Da zarar ka shigar da bayanan taskar ajiyarka ta eNaira, nan take tsarin zai kimanta adadin kudin da za ka biya da eNaira, iya gwargwadon farashin kudin kasar da ka aiwatar da cinikayya dashi.

A daya bangaren kuma, kana iya aika wa dan uwanka ko wani naka wannan nau’in kudi a ko ina yake a duniya, ta amfani da lambarsa ta eNaira Wallet idan yana dashi, ko ta taskar ajiyarsa a ko ina yake a duniya.

Idan Ina Son Ciro Kudin a Zahiri Kuma Fa?

Wannan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.  Sai kawai ka loda kudin zuwa taskar ajiyarka na banki.  Daga nan kayi amfani da katin ATM dinka ka ciro su.  Ko kaje bankinka ka cira kai tsaye.  Ko kuma ka aika wa wani a taskarsa, shi kuma ya baka takardun kudi.  Wannan bai takaitu ga adadin kudin da wani ya aiko maka ta manhajar eNaira Wallet dinka ba kadai.  Hatta adadin kudin da ka loda daga taskar ajiyarka na banki, sai daga baya kaji kana bukatar ka dawo dasu don ka cire saboda wasu bukatu ko lalurar rayuwa da ta shafi kudi, kana iya sake dawo dasu taskar ajiyarka ta banki kai tsaye, ba tare da wani caji ba, sannan ka cire su don biyan bukatarka.

To, Yaushe ne Wannan Sabon Tsari Zai Fara Aiki?

A karon farko, babban bankin Najeriya wato CBN, yayi niyyar kaddamar da sabon tsarin ne a ranar 1 ga watan Oktoba, daidai da lokacin da kasarmu ke bikin murnar cika shekara 61 da samun ‘yanci daga turawan mulkin mallaka, amma awanni kafin wayewar gari, sai ya canza lokaci.  Ana sa ran nan kadan zai bayyana sabon ranar da za a kaddamar.  Wannan kaddamarwa don yin gwaji ne na tsawon watanni 3; wanda zai tike a karshen wannan shekara.  Daga nan kuma sabon tsarin ya game kasar baki daya.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. magaji says

    we hope this e-naira will help nigerian economics 4 future development

    1. Baban Sadik says

      Of course, that is our wish. May Allah protect our nation and make it resilient.

Leave A Reply

Your email address will not be published.