Yaduwa da Munanan Tasirin Labaran Bogi (Fake News) a Kafafen Sadarwar Zamani (3)

Hanyoyi 6 na Ta'ammali da Labarai a Kafafen Sadarwar Zamani

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 17 ga watan Satumba, 2021.

249

Hanyoyin Ta’ammali da Labarai

Abu na gaba da mai karatu zai tambaya shi ne, idan har yaga sako a kafafen sada zumunta ana ta yadawa, me ya kamata in yi?  Tabbas akwai abubuwan da suka kamata mai karatu yayi, a duk sadda aka tunkudo sako gare shi; ko dai kai tsaye ko a wani zaure da yake ciki – na WhatsApp ko Facebook da sauransu.  Abubuwan da zai iya yi sun kai guda shida.  Ga bayaninsu nan dalla-dalla.

Tuhumar Asali

Salon da masu yada sakonnin karya ke amfani dashi yana dauke ne da janyo hankali, da shigar da tausayi a zuciya kai tsaye.  Duk wannan suna yinsa ne don neman yardar wanda zai karanta sakon, nan take.  Hanyar farko na tantance sakonni ko rubuce-rubucen da ake tunkudowa a ire-iren wadannan wurare ne dai ita ce tuhumar asalin sakon:  shin, sako ne ingantacce ko na bogi?  Idan har zuciyarka da zama mai yawan tuhumar sakonnin da ake tunkudowa a wannan mahalli, idan ba wanda kake ta tabbaci kan ingancinsa ba, to, ka samu ginshikin gane sakonnin bogi.  Domin duk abin da dan adam ya fara tuhumarsa, to, da wahala ya karbe shi kai tsaye.  Misali, idan aka aiko sako mai dauke da wani labari mai tayar da hankali, abu na farko shi ne ka sanya shakku a zuciyarka kan ingancin labarin.  Wannan matakin farko ne zai kai ka ga mataki na biyu.

Binciki Asali

Wannan shakku ne zai kai ka ga binciken asalin labarin; daga ina ya samo asali?  Kana iya yin hakan ta bangarori biyu.  Idan kusa kake da inda aka danganta faruwar abin, kana iya bincikawa kai tsaye, ta hanyar kiran wadanda ke wannan wuri, ko zuwa da kanka, ko aika wani; iya gwargwadon mahimmancin al’amarin gareka ko ga al’umma.  Idan kuma nesa ne sosai, ko babu wanda zaka aika, kana iya tambayar wanda ya aiko sakon kai tsaye.  Ba dole bane ka samu waraka ta wannan hanya, domin kashi 80 cikin 100 na masu tunkudo sakonni a kafafen sada zumunta ba sa bincika asalin labara – tunkudowa kawai suke yi.  Masu kokarin ne ke rubutaL “Copied” ko “منقول”, idan cikin larabci sakon yake rubuce.  Abin da wannan ke nufi shi ne, su ma kwafowa suka yi, ko nakaltowa suka yi, kamar yadda aka nakalto musu.  Abu na karshe shi ne ka bincika a Intanet, ta hanyar kwafo wani bangaren labarin sai kaje Google (www.google.com), ka binciko.  Idan labari ne da aka danganta kasa baki daya, kana iya zuwa matattarar labarai na Google News (https://news.google.com), sai ka nemo taken labarin.  Idan har da gaske ne, zaka ga wasu kafafen yada labarai (Jaridun Najeriya ko kasar waje), sun nakalto shi.

Wa Ya Ruwaito Labarin?

- Adv -

Hanya ta uku ita ce sanin wanda ya rubuta labarin, ba wanda ya aiko ba.  idan kafar yada labaru ce, gane hakan bai da wahala.  Idan akwai sunan wanda ko kafar yada labarum da ta nakalto labarin a jiki, sai a koma matattar labarai na Google News.  Ina ambaton hakan ne don saukakawa.  Domin a wannan matattarar, akwai dukkan kafafen yada labarai na duniya, ciki har da na Najeriya, kuma za ka samu labaran ne a waje daya.  Idan kuma babu sunan wanda ya kirkiri labarin a cikin labarin gaba daya; kamar yadda ake nakalto labarai na kissa, ko kuma na fadakarwa, ire-iren wadannan labaru galibinsu ko dai su zama wani ne ya zauna kawai ya rubuta su don ya koyar da darasi, amma ba hakikanin gaskiya bane, karya ce kenan.  Ko kuma ya zama hikaya ce wani ya dauko a wani littafi.  Irin wannan kuma, sai dai kabi darasin dake ciki, in har yana da wani amfani a gareka.

Mece Ce Madogarar Labarin?

Galibin labarun karya ba su da madogara mai tushe.  Sai dai kame-kame.  Galibinsu akan ce wasu ne suka fada, ko wani ne da ba ya son a ambaci sunansa, ko har yanzu ana kokarin tantance wanda ya fada ne, ko wani zance mara kangado makamancin hakan.  A yanayi irin wannan, kana ganin hakan ka san labarin karya ne.  A wasu lokuta kuma za a iya ambaton asalin labarin, amma dole ka bincika, domin zai iya zama karya ne.  Ire-iren wadannan labarai sunfi yaduwa lokuta zabe a Najeriya, musamman manyan zabukan kasa.  Duk labarin da ba shi da asali tabbatacce, to, kayi jifa dashi.

Asalin Hotuna ko Bidiyo

A wani lokaci kuma sakon na dauke ne cikin hoto mai motsi, wato bidiyo kenan, ko daskararren hotu, wato: hoto dai da ka sani.  A nan kuma dole ne ka lura da hoton da kyau; shin, ingantacce hoto ne, ko hada shi aka yi ta amfani da manhajar sarrafa hotuna a kwamfuta?  Idan bidiyo ne, yaya ingancin bidiyon yake?  Muryar dake ciki ta yi kama da ta wanda ake jingina lamarin gareshi, idan har sanshi kenan?  Sannan wurin da abin ya faru – anguwa ko gari ko daki ko ofis – ya yi kama da asalin wurin da ake danganta labarin gareshi?  Kana iya gane haka ta hanyar kwafan hoton, kaje shafin Google Image (https://image.google.com), sai ka zuba a ciki ka matsa “Search” ko “I am feeling Lucky”. Idan a Intanet aka dauko hoton aka hada shi da wani, za ka ga asalin hoton, kai tsaye.  Wannan shi ake kira: “Image Reverse Search”.

Ingancin Ka’idojin Rubutu

Galibin sakonnin bogi suna dauke ne da kurakuran rubutu.  Domin galibin marubutansu ba kwararrun ‘yan jarida bane ko kwararru wajen sarrafa bayanai.  Duk sakon da aka aiko, musamman wanda aka danganta shi ga wata kafar yada labarai, kuma ka ganshi dauke da kura-kuran rubutu – turanci ne ko Hausa – musamman kura-kuran da bai kamata a ce an samu ta la’akari da kwarewar wanda aka danganta labarin gare shi ba, to, ka san wannan kai tsaye labarin karya ne.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.