Hira da Edward Snowden (5)

Ga kashi na biyar na hirar Peter Taylor da Edward Snowden. A sha karatu lafiya.

407

Peter Taylor:  Yaya take tafiyar da rayuwarka a nan?  Kuma daga ina kake samun kudaden kashewa, musamman ganin dai dole kaci abinci, ga kuma tufafin sa wa?  Daga ina kake samun kudaden?

Snowden:  Alhamdulillah kam, ina da kudi.  Domin kafin in baro kasar Amurka, na yi ayyuka masu yawa da kwarewata, kuma na samu kudi mai dimbin yawa daga wannan aiki.  Kuma ina tare dasu a halin yanzu.

Peter Taylor:  Amma ta wace hanya kake iya cire wadannan kudade?

Snowden:  A a, tsabar kudin ne tare dani (ba a banki suke ba).

Peter Taylor:  Sun kai nawa?

Snowden:  A a, bazan iya fada ba, don hakan zai saba wa ka’idojin hukumar kwastam.

Peter Taylor:  Masu jinka da sauraronka daga nan Rasha na iya cewa:  daga dukkan alamu, zai yi wahala kasar Rasha ta baka mafaka ba tare da wata yarjejeniya ta karkashin kasa ba.  Haka ma hukumar tsaron kasar Rasha ta FSB, baza su barka haka kawai ka shigo kasar ba tare da sun tatikeka da tambayoyi ba kan irin abubuwan da kayi a baya.  Shin, akwai wani abu makamancin hakan?

Snowden: (Ya fashe da dariya) Haba dai, ko kadan.  Ka fa sani, na rusa rayuwata ce gaba daya, sanadiyyar hankado wannan badakala (don nemo ‘yancin jama’a), ta yaya kuma zan zagayo ta baya in ci gaba da yin abin da nayi adawa dashi a baya?

Peter Taylor:  To amma mu kaddara idan hukumar FSB tazo tace tana son ka mata bayani kan abubuwan da kayi a baya da yadda kayi su, (shin za ka musu bayani)?  Domin yanzu ka zama wani kamammen yaki ne a hannunsu, mai tsada.

Snowden:  Ai ba wani abu boyayye kan haka.  Kuma duk abin da ka ga na bayyana daga cikin abin da na hankado, suna hannun ‘yan jaridun (Amurka da Burtaniya).  Ban shigo kasar nan da komai ba a hannuna.

- Adv -

Peter Taylor:  To amma da ka shigo kasar, hukumar FSB sun zanta da kai?

Snowden:  Eh, sosai kuwa.  A filin saukan jirgi suka zanta da ni.  Kuma ban shigo kasar da komai ba.  Tun daga kasar Hong Kong na mika dukkan bayanan ga ‘yan jaridu.  Na yi haka ne saboda n azan san shiga wata kasa ce inda bazan iya sarrafa bayanan ba muddin na shigo.

Peter Taylor:  To yanzu idan na baka kwamfutata, a matsayinka na kwararre wajen iya sarrafa kwamfuta, baza ka iya kai wa zuwa ga wadancan bayanan da ka hankado ba?  Ko ba ka da wata sila dasu yanzu?

Snowden: (Ya fashe da dariya) Ina, ko kadan bazan iya ba.

Peter Taylor:  Ko a ma’adanar tafi-da-gidanka (Personal iCloud) ba ka dasu?

Snowden:  Ko kadan, ban dasu.  Wadancan bayanai da muke Magana a kai, na mika su ga ‘yan jaridu.  Kuma a halin yanzu suna adane ne a wata ma’adanar da ba ta jone da Intanet, wacce ake kira: “AirGas.”  Ba a jone da Intanet suke ba.  Manufar ita ce don a basu kariya daga duk wani aikin leken asiri ko dandatsanci.  Hanya mafi sauki da za ka iya kare kanka daga irin wannan kutse na leken asiri shi ne ya zama ba ka hawa Intanet gaba daya.  Na san yadda ake adana sirri, har ya kubuta daga masu nemansa.

Peter Taylor:  Idan kayi la’akari da dukkan abubuwan da suka faru, da kuma marhalar rayuwarka ta nan gaba, musamman ganin cewa ta yiwu kana iya yin zaman kaso na lokaci mai tsawo, shin, kayi nadama kan abubuwan nan?

Snowden:  Nadamar da nayi shi ne na tsawon lokacin da na dauka kafin hankado wannan badakala.  Domin iya tsawon lokacin da ka dauka kana kallon irin wannan tsari na leken asiri da shiga hakkin jama’a na sirri, ba tare da kayi wani abu ba, iya yadda tsarin ya dada munana da tabbatuwa.  Kuma wannan zai sa gyara matsalar ya zama mai matukar wahala.  Na dauki kaddara kan abin da ya faru, da irin hasarar da nayi.  Amma duk da haka, ina cikin kwanciyar hankali.  Ina kuma samun bacci a natse yanzu.

Peter Taylor:  Edward Snowden, ina godiya matuka.

Snowden:  Ni ma na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.