Sakonnin Masu Karatu (2010) (2)

A yau kuma ga mu dauke da sakonnin da kuka aiko daga ranar bikin sallar azumi da ya gabata, zuwa ranar litinin din wannan mako.  Duk sakonnin gaisuwar salla ba su bukatar wani jawabi, don haka na jero su a farko.  Kamar sauran lokuta, akwai wadanda suka bugo waya, da yawa ba kadan ba.  Muna musu godiya kan haka.  Wadanda suka aiko sakonnin Imel kuma za su gafarce ni, sai mako mai zuwa zan buga sakonninsu in Allah Ya so.  A halin yanzu ga dan abin da ya samu.  A sha karatu lafiya.

82

Sakonnin Gaisuwar Sallah

Salam Baban Sadiq, yardar Allah, amincin Allah, taimakon Allah, rahamar Allah, alherin Allah, annurin Allah, wadatar Ubangiji Allah, arziki, budi, rufin asiri, su kasance a tare da kai da sauran al’ummar musulmi; duniya da lahira.  Barka da salla. Allah ya maimaita mana, ya karbi ibadarmu amin.   Daga Sagir A. Nasir Rijiyar Lemo, Kano.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik), Ina maka barka da sallah, da fatan kayi sallah lafiya, to Allah Ya nuna muna na badin badada lafiya, cikin kwanciyar hankali. Sako daga ‘Ali Garba Okene, Jahar Kogi

Salam ina yi wa Mallam Abdullah da manyan dalibanka da duk makaranta wannan fili, BARKA DA SALLAH. Ubangiji Ya karbi ibadarmu, Ya sa muna daga cikin wadanda aka ‘yanta, kuma Ya kara daukaka wannan fili, ameen. Khaleel Nasir Kuriwa Kiru 07069191677

Assalamu alaikum, Ina yi maka fatan alkhairi da fatan an yi sallah lafiya, Allah (SWT) ya karbi ibadunmu, ya kuma maimaita mana amin. Ahmad Ali Aliyu.

Assalamu alaikum, zuwa ga Baban Sadik, da fatan an yi salla lafiya. Daga masoyinka: Salisu Aduya K/Hausa

- Adv -

Assalamu alaikum, ina mika sakon an sha ruwa lafiya, tare da fatan an yi Sallah lafiya, ALLAH ya maimaita mana amin.

Ina wa Baban Sadik gaisuwa, ina sauraron hira da ake yi da kai na Fasahar Internet a bbchausa.  Muhammad, Daga gidan Sarkin Fadan Lafia, Jihar Nasarawa.


Assalamu alaikum Baban Sadik, dan Allah ina son ka wayar min da kai dangane da bambacin da ke tsakaninDVD da CD da LCD.   Daga Babawo Mai Takin Mamani, Toro.

Malam Babawo lallai akwai bambanci tsakanin “DVD” da “CD”, a daya bangaren kenan.  Sannan kuma da bambancin jinsi a tsakanin su da fasahar “LCD”.  Idan aka ce “CD”, ana nufin faifan garmaho na zamani; wato kamar kaset din garmaho irin ta da kenan in ka santa.  Ma’anar “CD” shi ne “Compact Disc”, kuma ana amfani da shi ne wajen taskance bayanai na rubutu, da sauti, da kuma hotona daskararru ko masu motsi, wato bidiyo kenan. A takaice dai, wannan fasaha ce ta maye gurbin faya-fayan garmaho da a zamanin da ake amfani da su wajen sauraron sauti kadai. Kuma tana iya daukan mizanin bayanai wajen miliyan dari bakwai (700MG) ne kadai.

Shi kuma “DVD”, wanda yake nufin “Digital Compact Disc”, ingantaccen nau’in “CD” ne, wanda ke cin bayanai daga biliyan hudu zuwa biliyan goma sha shida (4GB – 16GB).  Idan muka koma kan fasahar “LCD” kuma, wanda ke nufin “Liquid Crystal Display” a zamanance, it ace sabuwar fasahar nuna bayanai a  fuskar talabijin, ta amfani da sinadaran gilashi masu dauke a sifar ruwa.

A takaice dai, shi tsarin “LCD” nau’i ne na gilashin Talabijin, wanda ya sha bamban da nau’ukan gilasan da ke fuskar talabijin da na LCD ba.  Yana da inganci wajen nuna hotuna rau-rau, kuma ba ya fitar da sinadarai masu cutar da idanu a yayin da ake kallonsa, kamar yadda sauran gilasan Talabijin ke fitarwa kuma suke cutarwa.  Wannan nau’i na gilashi bai tsaya kan Talabijin kadai ba, har da kwamfuta akwai masu dauke da irinsa, musamman kwamfutocin kan tebur na zamani.  Wannan shi ne LCD, kuma sabanin sauran da suka gabata, ba ma’adar bayanai bane, tsarin gilashi ne.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.