Yaduwa da Munanan Tasirin Labaran Bogi (Fake News) a Kafafen Sadarwar Zamani (4)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 24 ga watan Satumba, 2021.

295

Hanyoyin Magance Yaduwar Labaran Bogi

A makon jiya masu karatu sun koyi yadda za su iya ta’ammali da kowane irin labari ne aka tunkudo musu shi ta hanyar kafafen sadarwa, musamman na abota, wato: “Social Media” kenan.  A wannan mako, wanda shi ne na karshe kan wannan maudu’i, za mu dubi hanyoyin da za a magance samuwa da yaduwar ire-iren wadannan labaru ne ma gaba daya, don rage fitinuwar mutane dasu.  Su ma hanyoyi ne guda shida.  Ga su nan:

Hadin Gwiwar Hukuma da Kafafen Yada Labaru

Hanya ta farko ita ce hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati da kwararru a kafafen yada labarai, don ganowa da dakile dalilai da hanyoyin da wadannan labarai ke samuwa.  Hakan zai yi tasiri matuka saboda samuwar hannun hukuma da masu ruwa da tsaki cikin harkar yada labarai.  Hukuma ta samar dokoki na musamman masu alaka da kafafen sadarwa na zamani, ko dai sababbin dokoki ko kuma yin gyaran fuska ga wadanda ake dasu.  Tabbas hakan ba abu bane mai sauki, musamman ta la’akari da zargin gwamnati a duk sadda tayi yunkurin samar da dokoki irin wadannan.  Amma idan aka samu fahimtar juna tsakaninta da kafafen yada labaru, wanda su ma abin na cinsu a rai da kasuwancinsu, za a samu mafita.

Wayar da Kan Jama’a

Hanya ta biyu ita ce wayar da kan jama’a kan illolin wannan mummunar al’ada ta samarwa da yada labaran karya.  Mafi girman kason wannan aiki ya rataya ne kan gwamnati, musamman hukumomin yada labaru da wayar da kan jama’a.  Alhamdulillah, gwamnatin tarayya ta fahimci hadarin wannan al’amari, kuma bata gushe ba wajen yunkurin samar da mafita.  A watan Agusta da ya gabata, shugaban Hukumar Wayar da Kan jama’a ta kasa (National Orientation Agency – NOA), wato Malam Garba Abari, ya tabbatar da cewa daga yanzu zuwa shekaru 5 masu zuwa, gwamnati za ta horas da matasa 37,000 – kowace jiha mutum 1,000 – don dakilewa da kawar da labaran bogi a kafafen sadarwa na zamani.  Bayan gwamnati, wajibi ne kan kafafen yada labarai – jaridu, da talabijin da rediyo – da sauran ‘yan kasa, iya gwargwadon karfi da fahimta da iko, su dafa wajen dakile hanyoyin da wadannan labaru ke samuwa.

Samar Da Labarai Masu Inganci Da Nagarta

- Adv -

Labaran bogi na samun gindin zama ne a al’ummar dake fama da karancin labaru masu inganci da nagarta a kafafen sadarwa.  Da kuma karancin aminci tsakanin masu amfani da labaru da wadanda ke samar dasu, a al’adance.  Idan kafafen yada labaru na jarida, da rediyo da talabijin da Intanet suka dukufa wajen samar da labaru masu inganci da nagarta, hakan zai taimaka wajen samar da natsuwa a zukatan jama’a.  Karin natsuwa da amintan ne zasu kai jama’a ga lazimci labaru daga wadannan kafafe.  Hakan ne zai kashe wa labarun karya kasuwa.

Fasahar Tantance Labarai

Hanya ta hudu ita ce, samar da wata fasaha sananniya, mai saukin aiwatarwa da mu’amala wajen tantance labaran bogi daga na gaskiya.  A makon jiya na kawo hanyoyi shida da mai karatu zai iya bi, wajen tantance kowane irin labari ne yaci karo dashi a kafafen sada zumunta.  Tabbas hanyoyi ne masu inganci.  Amma ba kowa ke da hakuri da kwarewar da zai iya bibiyarsu daga matakin farko har zuwa karshe ba.  Amma idan aka kintsa wadannan hanyoyi a cikin wata fasaha ta musamman, kamar manhajar wayar salula, ko a matsayin wani shafi na musamman da za a iya amfani dashi, hakan zai taimaka matuka.

Karantarwa a Makarantu da Jami’o’i

Hanya ta biyar ita ce shigar da wannan bangare cikin manhajin karantar da dalibai a makarantu kanana da jami’o’i, don koyar da hanyoyi nagartattu da za a iya dakile wadannan labaru cikin al’umma baki daya.  Wannan ne zai taimaka wajen samar da wata ka’idar ilmi sananniya tsakanin masana da al’umma baki daya; ta yadda duk inda aka je, zancen iri daya ne.  Hakan kuma na bukatar kwarewa a fannin sadarwa na zamani – sanin hanyoyi da na’urorin sadarwa da tasirinsu wajen samarwa, da yadawa, da kuma dakile wadannan hanyoyi, cikin sauki.

Bibiyar Kafafen Yada Labarai Sama da Daya

Daga cikin dalilan dake sa mutane suke afkawa da zarar an bijiro musu da labaran karya, shi ne killace kansu ga wata kafa ta yada labarai guda daya tak.  Idan aka yi rashin sa’a ire-iren wadannan labaru na karya na zuwa ta kafar da ita ce kadai mutane suka aminta da ita, to, barnar za ta game.  Amma idan ya zama ana surkawa, a karanta wannan, da wancan, da wadancan, to, hakan zai taimaka wajen tantance gaskiya.  Domin duk abin da ya faru a galibin lokuta, kafafen yada labarai kan ruwaito shi.  Kuma ta hanyar bibiyar kafafe daban-daban ne za a iya tantance wata gaskiyar daga wata karyar.

Wadannan, a takaice, su ne hanyoyin da za a biya, a kusa ko a nesa, wajen dakile hanyoyin da labarum karya ke tsira, da tare da girbe su, a inda aka yi rashin sa’a suka tsiro ba a lura dasu ba, kafin su zama annoba cikin jama’a.  Allah mana jagora baki daya, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.