Filin Ji-Ka-Karu (1)

Filin “Ji-Ka-Karu” fili ne da na ware shi don fa’idantar da masu karatu kan fannin Kimiyya da Kere-kere a ilimance kuma a tarihance. Zai rika zuwa lokaci-lokaci, kwatsam. Wannan shi ne kashi na daya.

277
 • Idan aka jefa katako ko bangarorin itatuwa ko kirare a cikin kogi ko teku ko duk inda ruwa yake tare, ba su lumewa zuwa karkashin ruwa, saboda a binciken kimiyya, ruwa ya fi katako ko itatuwa nauyi.

- Adv -

 • Idan aka jefa karfe cikin ruwa – kogi, ko teku, ko duk inda ruwa ke tare – ya kan lume har zuwa karkashin ruwan, saboda a binciken kimiyya, karfe ya fi ruwa nauyi.
 • Idan aka kyasta kan ashana a jikin kwalin ashanar, nan take wuta kan kama, saboda a binciken kimiyya, “gogayya tsakanin abubuwa biyu masu kaushi” (wato Friction) na haifar da zafi (wato Heat) a duk inda ya samu.
 • Launin shuke-shuke ko ciyayin da ke raye kan zama kore ne saboda samuwar sinadarin “Chlorophyll” da ke samuwa a cikin kwayoyin halittarsu. Amma idan a cikin inuwa suke, launinsa kan zama rawaya galibi, wanda kuma hakan alama ce da ke nuna yunwa a tare da su.
 • Idan aka bar kankara cikin yanayin zafin da mizaninsa ya kai sifili (0) a ma’aunin santigireti (zero centigrade), to, zai narke ya zama ruwa.
 • Ruwa na raguwa ko karuwa ne iya gwargwadon zafi ko rashinsa; idan zafinsa kadan ne, yawansa kan ragu. Amma idan zafinsa ya kai makura (Boiling Point), to, yawansa zai karu.
 • A al’ada duk abu mai nauyi da ke sama, muddin ba a rike yake ba, zai fado kasa. Haka duk abin da ka jefa sama, nan take zai fado kasa.  Me yasa?  Malaman kimiyya suka ce dalilin na samuwa ne daga wannan kasa da muke takawa.  Akwai wani karfi da ke janyo duk abin da ke samanta.  Wannan karfi, wanda suke kira “Force of Gravity” a fannin kimiyya, shi ne da alhakin wannan aiki.  Wanda ya fara bincike na musamman a wannan fanni shi ne Sir Isaac Newton, cikin littafinsa mai suna “Principia”.

- Adv -

You might also like
2 Comments
 1. hassan says

  Assalamualaikum.babansadik .Allah ya Kara basira hakika Ina karuwa sosai a wanan shafi.da fatan Allah ya Kara taimakawa

  1. Baban Sadik says

   Wa alaikumus salam, barka dai Malam Hassan. Muna godiya matuka da tsokacinka. Allah saka da alheri.

Leave A Reply

Your email address will not be published.