Sakonnin Masu Karatu (2020) (1)

Yadda Ake Filashin Wayar Salula

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 13 ga watan Maris, 2020.

67

A cikin makon da ya gabata ne (11 Maris, 2020) wasu barayi suka balle makullin mota ta a nan Abuja, inda suka dauke jakar dake dauke da kwamfuta ta, da ma’adanan bayanai manya guda 2 (external hard drives) da sauran kayayyaki da takardu masu amfani da bazan iya tantance su ba har yanzu.  Wannan yasa na rasa galibin abubuwan da nake dogaro dasu wajen gudanar da bincike kan makalolin da nake rubutawa a wannan shafi.  Don haka zan dakatar da rubutu kan “Ci Gaban Kimiyya da Kere-kere ga Al’adu da Dabi’ar Dan Adam”, wanda na farko cikin watan da ya gabata, sai nan gaba idan na gama kintsawa. 

A yau in sha Allahu zan leka taskar sakonninku ne, don amsa wasu daga cikin tambayoyi ko tsokacin da kuka yi.  A gafarceni kan wannan tsaiko da aka samu.  Ina godiya matuka da goyon bayan da nake samu daga gare ku baki daya.

———

Assalamu Alaikum Baban Sadik, barka dai.  Don Allah ina son a bambance mini tsakanin wadannan kalmomi: “Factory Reset”, da kuma “Flashing” a fannin kimiyya da fasahar wayar salula.  Da fatan zan samu gamsassun amsoshi daga gareka.  Na gode.  Aliyu Nasiru, Kano: alinasir30@gmail.com

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aliyu.  Lallai akwai bambanci tsakaninsu, kamar yadda a zahirin haruffansu ma da bambanci.  Da farko dai, zai dace Malam Aliyu yasan cewa bayan kera wayar salula, wadanda suka kera su sun san cewa a wani lokaci na rayuwarsu, muddin ana amfani dasu, to, akwai nau’ukan matsaloli ko kalubale da zasu rika cin karo dasu.  Ire-iren wadannan matsaloli na iya zuwa ta hanyar mai amfani dasu, ko ta hanyar wata wayar da suke aiwatar da sadarwa da su, ko ta kuma a ita karan kanta wayar; haka kawai tana iya haduwa da matsala, ko da babu wanda ya taba ta, muddin ana amfani da ita.   Don haka, sai suka samar da hanyoyin warware wadannan matsaloli.  Wadannan hanyoyi dai mataki-mataki ne, kamar yadda su ma matsalolin hawa-hawa ne.

Kafin bayanin dalilan da kansa wayar salula ta shiga halin da za ta bukaci wadancan hanyoyin waraka, wadanda ka zayyana biyu kadai daga cikinsu, yana da kyau mu san cewa, a duk sadda ka kunna waya, kayi amfani da ita na dan wani lokaci ko kwanaki tana kunne, akwai inda take tattara wasu bayanai na musamman wadanda idan ta tashi bukatar aiwatar da wani aiki irin wanda tayi a baya, ba sai ta maimaita matakan da ta bi ba, kawai za ta koma kan wadancan bayanai ne don aiwatar da aikin.  Wadannan bayanai su ake kira: “Cache”.  Kuma wayar salula kan taskance bayanai kan dukkan ayyukan da take aiwatarwa – daga kiran waya, zuwa hawa Intanet, da sauraron sauti ko kallon bidiyo.  Dukkan wadannan ayyuka idan kana yinsu ta hanyar wayar salula, tana aiwatar da umarnin da kake bata wajen yinsu ta hanyar komawa kan bayanan da ta taskance a baya kan aiki, ba sai ta maimaita su a aikace daga farko zuwa karshe ba.

To amma kasancewar wayar salula na’ura ce, akwai sadda wadannan bayanai da take taskancewa masu suna: “Cache” kan gurbace.  Shi yasa a wasu lokuta idan ka bukaci aiwatar da wasu abubuwan da ka saba yinsu da wayarka, sai ka samu cikas.  Musamman wadanda suke da alaka da wayar kai tsaye, ba na kira ko amsa kira ba.  Wannan yasa aka tanadi wadannan hanyoyi don magance ire-iren wadannan matsaloli.

Matsaloli

Wadannan matsaloli dai sun shafi ruhin wayar salula ne, wato babbar manhajarta ko kuma masarrafan da mai waya ke loda mata don amfanin kansa; wato: “Hardware Related Issues” kenan, kamar yadda a fannin kimiyyar sadarwa.  Ire-iren wadannan matsaloli dai sun hada da matsalar yanayin sadarwa (Network), da matsalar sauti, da matsalar bidiyo, da matsalar tes, da matsalar sarrafa bayanai, da matsalar aiwatar da kira ko amsa kira, da matsalar aika sakonnin Imel, ko hawa Intanet da dai sauransu. Alamun dake tabbatar da samuwar wadannan matsaloli a lokuta daban-daban dai su ne, kasa kira ko amsa kira, da yawan cijewar waya idan ana amfani da ita, da yawan sumewa (hanging) lokaci zuwa lokaci, da sauran alamu makamantansu.  A wasu lokuta kuma wasu kan so sanya wa wayar salula wasu siffofi da hanyoyin gudanar da abubuwa irin wadanda asalin kamfanin bai yarda a dora wa wayar ba.  Haka kuma, a wasu lokuta mutum na iya mance Kalmar sirrin wayarsa, ya kasa sarrafa ta.  Wannan kan sa dole a bi ta bayan fage don shawo kanta.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.