Shahararrun Kamfanonin Wayar Salula a Duniya (2)

Kashi na shida cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

549

Kamfanin Samsung Group

Kamfanin Samsung Group shi ne kamfani na daya a kasar Koriya ta Kudu (South Korea) wajen samar da kayayyakin lantarki da wayar salula, kuma kamfani na biyu a sahun  kamfanonin kera wayar salula da sayar dasu a duniya, bayan kamfanin Nokia Corporation, kamar yadda bayanai suka gabata.  Wannan shahararren kamfani dai ya samo asali ne a shekarar 1938, kuma mallakin wani bawan Allah ne mai suna Lee Byung-Chull, wanda a halin yanzu yana cikin shahararrun masu kudi a kasar Koriya ta Kudu.  A shekarar 1938 ne ya kafa kamfanin Samsung Trading Company, inda yake sayar da kayayyaki masarufi a wani dan kauye mai suna Daegu, kusa da birnin Seoul. 

Cikin shekarar 1953 sai ya bude wani reshe don samar da sukari.  Kafin shekarar ta kare ya sake fadada kamfanin, inda ya samar da wani reshe da ya sanya wa suna Samsung Electronics.  Wannan reshe ne ya samar da tashar rediyo da talabijin a kasar a shekarar 1970.

Da aka shiga shekarar 1982 kuma sai wannan reshe da ke samar da kayayyakin lantarki, wato Samsung Electronics ya kafa masana’antar samar da talabijin.  Wannan ya ci gaba har zuwa shekarar 1990, lokacin da ya fara mallakar kadarori a wasu kasashen duniya, ya kuma bude reshen gine-gine da ya sa wa suna Samsung Construction.  Wannan reshen ne yayi tasiri sosai a duniya, wajen samar wa kamfanin kudade fiye da shekarun baya.  Misali, shi ne ya gina dogayen hasumiyar da ke birnin Kuala Lumpur da ke kasar Malesiya wadanda ake kira Petronas Towers, masu hawa tamanin da hudu kowanne. Da kuma dogayen hasumiyar birnin Taipei da ke lardin Taiwan, wato Taipei 101, masu hawa dari da daya kowannensu.

Bayan wadannan har wa yau, kamfanin Samsung Construction ne ya gina shahararrun hasumiyoyin nan guda biyu da ke birnin Dubai masu suna Burj Dubai.  Wannan ba abin mamaki bane, domin kamfanin yayi suna a bangaren kera manyan jiragen ruwa a duniya.

Kamfanin Samsung Group dai yana kera wayoyin salula, da manyan ma’adanar kwamfuta, wato Hard Disk Drive, da kayayyakin lantarki, irinsu rediyo da talabijin na zamani kowane iri ne kuwa.  Sannan kuma ya gina wata tafkekiyar Jami’a a kasar birnin Seoul mai suna Sungkyunkan University, wacce ke yaye zaratan dalibai a fannonin ilimi dabam-daban.  Wadannan dalibai dai galibinsu kamfanin ne ke daukansu a matsayin ma’aikata.  A halin yanzu dai kamfanin na dauke ne da ma’aikata dubu dari biyu da saba’in da shida (276,000), a kididdigar shekarar 2008.  Kuma babban hedikwatansa na birnin Seoul, a wani gari da ake kira Samsung Town.  Duk mai son Karin bayani na iya ziyartar kamfanin a gidan yanar sadarwarsa da ke http://www.samsung.com.

Kamfanin Motorola Incorporated

Kamfanin Motorola Incorporated ya samo asali ne a shekarar 1928, a birnin Chicago da ke jihar Illinois a kasar Amurka.  Wadanda suka kirkiri wannan kamfani dai su ne: Paul  Galvin da kuma Joseph Galvin, kuma sunan farko da suka sanya wa kamfanin shi ne: Galvin Manufacturing Corporation.  Sai a shekarar 1930 aka canza sunan kamfanin zuwa “Motorola”, sunan da aka dauko daga kalmomi biyu: “motor” da kuma “ola”.  Manufar sanya sunan “motor” shi ne don tabbatar da kwarewar kamfanin wajen kera wayoyin tafi-da-gidanka da cikin motoci.  Kalmar “ola” kuma wata kalma ce da ta shahara a wancan lokaci, inda komai aka samu, sai a kara masa sunan “ola” a karshe.

- Adv -

Kamfanin Motorola Incorporated ne ya fara kera wayoyin Walkie Talkie a duniya, kuma shi ne ya fara kera wa Hukumar NASA na kasar Amurka kayayyakin sadarwa don sawwake tafiye-tafiyen da masana kimiyyar sararin samaniya ke yi.  A karshe ma dai, da wayar sadarwa ta rediyo da kamfanin ya kirkira ne direbobin kumbon Apollo 11 suka yi amfani don sanar da cewa sun isa lafiya, a shekarar 1969.  Kamfanin ya shahara wajen kera wayoyin salula da wayoyi na musamman da ake amfani dasu a cikin mota, da kuma kayayyakin sadarwa a tsakanin kwamfutoci, wato Networking Equipments.  Shi ne kamfanin farko da ya fara amfani da babbar manhajar wayar salula na kamfanin Google mai suna Android a wayar salularsa ta  musamman (Smartphone), inda ya fitar da wayar farko ranar 6 ga watan Nuwamba, 2009.

Kuma shi ne kamfanin wayar salula na farko da ya fara sanya wa wayarsa fasahar GPRS  a duniya.  Kamfanin Motorola Incorporated yayi fice a sahun kamfanonin sadarwar wayar salula, inda ya yi ta zama na daya a shahara da inganci, kafin kamfanin Nokia Corporation ya shallake shi a shekarar 1998.  A yanzu yana da ma’aikata guda dubu sittin da hudu (64,000), kuma ana iya samun Karin bayani a gidan yanar sadarwarsa da ke http://www.motorola.com.

 Kamfanin SonyEricsson

Wannan kamfani gamayya ne na kamfanoni guda biyu, wato kamfanin Sony da ke kasar Japan, da kuma kamfanin Ericsson da ke kasar Suwidin a nahiyar Turai.  Wannan gayamma ya samo asali ne a shekarar 2001, cikin watan Oktoba.  A halin yanzu hedikwatar na kamfanin birnin London ne da Fullham a kasar Ingila.  Amma yana da rassa inda ake bincike kan fasahar kere-kere a kasashen Japan, da Suwidin, da Sin, da Jamus, da Amurka, da Indiya, da kuma kasar Ingila.  Kamfanin SonyEricsson shi ne na hudu a sahun kamfanonin wayar salula da suka shahara wajen inganci da yawan ciniki, bayan kamfanonin Nokia Corporation, da Samsung Group, da kuma LG.  Yana kera wayoyin salula ne masu inganci, kuma masu jure tsawon lokaci wajen sauraron wakoki ko sauti.

Shahararriyar wayar salular da kamfanin yake alfahari da ita kuma ta taimaka wajen samo masa suna ita ce: K750i, wacce ya kera a shekarar 2005.  A shekarar 2008, kididdiga ya tabbatar da cewa kamfanin SonyEricsson ya sayar da wayoyin salula sama da miliyan casa’in da shida da dubu dari shida (96.6million).  Yana da ma’aikata guda dubu tara da dari hudu (9,400).  Ana iya ziyartar gidan yanar sadarwarsa da ke http://www.sonyericsson.com, don neman Karin bayani.

Kamfanin LG Group

Kamfani na karshe da zamu kawo bayani kansa shi ne kamfanin LG Group, wato kamfani na uku a sahun manyan kamfanonin kayayyakin lantarki a kasar Koriya ta Kudu.  Asalin sunan kamfanin dai shi ne: “GoldStar”, lokacin da wani bawan Allah mai suna Koo In-Hwoi ya kafa kamfanin a shekarar 1947.  Kamar kamfanin Nokia Corporation, kamfanin LG Group ya fara ne da masana’antar robobi gasassu, wato Plastics.  A shekarar 1958 kuma ya shiga harkar kayayyakin lantarki.  A shekarar 1959 kuma ya kera rediyo na farko a tarihinsa.  Haka yaci gaba da tafiyar da harkokinsa har zuwa shekarar 1995, lokacin da aka canza sunan kamfanin don samun karbuwa a duniya, daga GoldStar zuwa LG Group.  Manufar “LG”, kamar yadda tarihi ya tabbatar, shi ne “Lucky GoldStar”. 

Wannan canjin suna kuwa ya karbi kamfanin, inda ya ci gaba da fadada harkokinsa zuwa kera wayoyin salula da talabijin da rediyo da sauran kayayyakin sadarwa na zamani, kamar yadda mai karatu ke gani a halin yanzu.  Wannan tasa a karshe kamfanin ya sauya taken kamfanin daga “Lucky GoldStar”, zuwa “Life is Good”.  A halin yanzu kamfanin na dauke ne da ma’aikata dubu dari da saba’in da bakwai (177,000), Ana iya ziyartar gidan yanar sadarwarsa da ke: http://www.lg.com, don neman Karin bayani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.