Gaskiya da Gaskiya (9): Da Me Ka Fi Su?

Duk masu zagin Sahabban Manzon Allah (SAW) babu wani abu guda daya da za su iya dagawa su nuna, wanda zasu kira da suna tallafi ne ga addini, wanda yafi ko zai fi abin da Sahabbai suna yi wajen ci gaban addinin Allah. Kaskanci ya kare wa mai zagin Sahabbai. Da me ka fi su?

273

A bayyane yake cewa samuwa da habbakar hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani sun dada taimaka wa jama’a, musamman dai matasa a arewacin Najeriya wajen bayyana manufofinsu, ciki har da manufofin addini.  Daga cikin abin da yake zahiri karara, kuma yake tabbace babu coge, akwai bayyanar masu zunduma wa Sahabban Manzon Allah (SAW) zagi, da fadin duk wata kalma ta kaskanci a kansu, irin kalmomin da ko kafirai ba su gaya musu ko danganta su gare su.   Wannan lamari kan dame ni, musamman ganin cewa masu wannan dabi’a mummuna duk Hausawa ne, masu ikirarin musulunci ko “kyakkyawar tafarkin musulunci” ta hanyar danganta kansu ga Manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa.

Ba son Ahlul baity da danganta kai gare su bane damuwata, a a.  Illa rashin adalcin da ke kunshe cikin wannan ikirari.  Wannan lauje ne a cikin nadi.

Shekaranjiya nake karanta zancen wani inda yake kunduma wa Nana Aisha (RA) zagi kan cewa “Mara kunya ce ita, ba ta da mutunci.”  Nan take ya jawo hadisin Bukhari dake bayanin wani sabani da ya taba shiga tsakaninta da Mijinta, har a karshe aka kira mahaifinta yayi hukunci.  Mai wannan zance ya amince cewa lallai wannan lamari ya faru, don haka ne ma ya kira Nana Aisha “mara kunya.”  Amma abin mamaki, kwanakin baya kuma na ji shi yana cewa: “Duk hadisan da ke bayani kan falalan Aisha karya ne.”  Kuma “don me za a ce itace tafi kowace mace falala, bayan ga Nana Khadija (RA), wacce ta agaza, ta tausaya, kuma ita ce uwar ‘ya’yansa?”  Wannan tufka da warwara ne.

Me yasa ka gaskata hadisin da ke nuna “rashin kunyar Aisha” (kamar yadda kace), amma kaki amince wa hadisin dake nuna falalarta?  Sannan, ai Nana Khadiya (RA) bata yi tsawon rayuwa a musulunci ba ta rasu, in ka hada da shekarun Nana Aisha.  Nana Khadija bata riski zaman Madina ba Allah ya karbi rayuwarta, in ka hada tarin iliminta da Nana Aisha.  Kuma me yasa ka gaskata hadisin Nana Aisha kan kishin da take yi saboda ambaton Nana Khadija da Manzon Allah (SAW) keyi, amma ka kasa gaskata hadisan falalar Nana Aisha?  Me wannan ra’ayi bai yi adalci ba kowaye shi.

- Adv -

Idan muka dawo bangaren ‘ya’yan Nana Khadija, bayan Fatima (RA) akwai ‘yan uwanta.  Abin mamaki, su ba Ahlul Baiti bane?  Ina Rukayya?  Ina Ummu Kulthum?  Me yasa ba a ambatonsu?  Kuma ba a musu maulidi balle a musu addu’a?  Idan aka musu haka an yi musu adalci?  Kuma anyi wa mahaifiyarsu da ake ikirarin kaunarta adalci?

Idan muka juwo ta bangaren sauran matan Manzon Allah ma haka lamarin yake.  A yayin da wasunsu ke zabe wasu daga ciki (irin su Ummu Salama) a shafe su da mai, wasu na ganin duk “ba su da wani kima wajen Manzon Allah (SAW).”  Kwanaki uku da suka shige na hangi wani na cewa: “Wai meye abin takama wai don Manzon Allah ya auri ‘ya’yansu?” (wato Abubakar da Umar kenan).  Yaci gaba da cewa: “…bayan tallansu ma ake masa don ya aura?”  Abin da yake nufi shi ne, duk ba su da wata kima; an gaji dasu ne sannan aka tallata wa Manzon Allah ya aura.  Shin, ga mai hankali wannan ba cin mutunci bane ga Manzon Allah (SAW)? Anya da gaske muna kaunarsa kuwa?  Muna kaunar iyalan gidansa hakikatan?  Da sake.

A bangaren masu abin ma (wato Sayyidina Ali – RA), ba dukkan ‘ya’yan bane ake dauka.  A yayin da ake shafe su Nana Fatima (RA) da Husaini da mai, su Hasan da Muhammad Ibn Al-Hanafiyya ko kallonsu ba a yi, balle a dubi sauran ‘ya’yan matansa shi kanshi.  Sai ana son furofaganda sannan ake maka sunan Hasan a tuta ko logo.  Amma a tare da haka, hatta wadanda basu mutu a musulunci ba an jawo su ance Ahlul Baiti ne.  Wannan coge ne tsantsa…orijina kuwa.

DON HAKA:  Duk wanda ke zagin su Sayyidina Abubakar da Umar (RA) da sauran sahabbai, to WALLAHI yasan cewa yin hakan TUHUMA CE ga zatin Manzon Allah.  Tuhuma ce ga gamewar ilmin Allah – domin hakan na nuna cewa (kamar) Allah bai san za su zama mutanen banza bane, ya hada su zama da Manzonsa, wanda shi ne mafificin halittu baki daya.

Sannan, a karshe, a ka’idar al’ada da hankali, duk wanda ka bude baki da la’ance shi, ko ka zage shi, abin da kake nunawa karara shi ne, ka fi shi ne; ta kowane bangaren rayuwa da mutunci.  DON HAKA, KAFIN KA ZAGI KOWANE SAHABI, KA DUBI RAYUWARKA TUKUN KA GANI, SHIN, WANI CI GABA KA KAWO WA MUSULUNCI?  IDAN AKWAI, SHIN, YA KAI NA WANCAN SAHABIN?  IN EH, SANNAN KA ZAGE SHI.  IN KUWA AMSAR A A CE, TO AHIR DINKA.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.