Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (17)

Kashi na 17 cikin jerin bayanan da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Asha karatu lafiya.

159

Matashiya

Idan masu karatu n tare damu dai, mun fara bayani kan hanyoyin kariya daga masu satar zatin mutane.  Kafin wannan lokaci, mun dauko bayani tiryan-tiryan kan wannan mummunar ta’ada, inda muka fara da bayani kan ma’anar satar zati, da dalilan da suka sa barayin zati ke satar bayanan mutane, da kuma na’uka ko fuskokin da wannan nau’in ta’addanci ke dauka.   Yadda ake satar mutane a zahirin rayuwa, haka ake satar mutane a shafukan sada zumunta.  Illa dai bambancin dake tsakani shi ne:  a zahirin rayuwa ana sace mutum ne gaba dayansa, da gangar-jikinsa da ruhinsa.  Amma a shafukan sada zumunci, ganin cewa ba zahirin gangar-jiki bane ke bayyana a shafukan, ana sace zatin mai shafin ne.

Satar zati a kafashen sada zumunta na daukan fuskoki ne mabambanta.  Akwai wanda za a sace zatinsa, ana gudanar da abubuwa da sunansa, amma bai sani ba.  Haka wadanda ke mu’amala da barawon su ma baza su gane cewa ba wanda suke zato bane.  Watakila saboda bai cika mu’amala da shafin ba a-kai-a-kai.  Idan haka ta faru, barawon na iya tura wa abokan mai shafin sako cewa yana matukar bukatuwa zuwa ga kudi, su taimaka masa.  Kasancewar sun san shi, ba za suyi wani dogon bincike ba, musamman idan na kusa dasu ne.  A yanayi irin wannan barawon kan canza “Password” din mai shafin ne, don hana shi hawa, balle yaga irin wainar da yake toyawa.

Fuska ta biyu ita ce, ana iya sace zatin mai shafi amma aki canza “Password” dinsa.  Barayin dake amfani da wannan tsari suna yin haka ne don sauraro ko gani ko leken asirin mai shafin, don ji, da gani, da kuma kwasan irin bayanan da yake aikawa ko karba.  Wannan na faruwa a dandalin Facebook, da Twitter, da kuma Imel.  Barawon zai ta lura da mai shafin ne, tare da nadar irin bayanan da yake so, ba tare da mai shafin ya sani ba balle ya canza “Password” dinsa.

Fuska ta uku kuma, ana iya sace zatin mai shafi a dandalin abota ta hanyar kwafar irin bayanansa, da hotunansa, da lambar wayarsa, da sunansa, da duk wani abin da zai iya taimakawa wajen kwaikwayon rayuwarsa, sai a bude shafi makamancinsa.  Wannan shi ne mafi muni daga cikin hanyoyin satar zatin mai shafi.  Domin da wannan tsari, ana iya yaudarar mutane da dama wadanda suke aminai ne ko ‘yan uwan wanda aka saci zatinsa.  Cikin makonnin baya naga wata ‘yar uwa ta aika wa wata ko wani sako ta Inbox, tana rokonsa ko rokonshi da ya cire sunanta da hotonta da yasa a “Profile” dinsa ko dinta, sannan yaji ko taji tsoron Allah ya ko ta rufe shafin nan.  Da na duba sai na ga da irin sunanta ne aka bude shafin dashi, sannan hotonta ne sak, a dore a kan “Profile” din shafin.  Wani karin abin takaici ma shi ne, barawon dake amfani da wannan tsari yana iya tura wa abokanka sako, cewa su karbe shi a matsayin aboki, ya samu matsala ne da tsohon shafinsa.  Mai amfani da wannan fuska wajen satar zatin mutane a dandalin abota har wa yau, kan aikata badakala nau’uka daban-daban da sunan mai shafin, ta hanyar bin wadanda yake tunanin sun san mai sunan, yana zambatarsu.  Na yi rubutu a shekarar 2015 a shafina dake Facebook, don fadakar da jama’a kan wannan matsala.  Musamman dangane da mutanen dake bude shafuka da sunan manyan shugabanninmu, na da ko na yanzu – irin su Atiku Abubakar, da Shugaban Kasa mai ci, da Abdullahi Dikko Inde, da Mai martaba Sarkin Kano, Amir Muhammad Sanusi Lamido Sanusi II –  don yaudarar jama’a.  Wannan duk matashiya ce;  ina fatan wadanda ke tare damu tun farkon wannan silsila sun fahimci tsarin.

- Adv -

Kasancewar galibin dalilin dake haddasa satar zati na aukuwa ne ta hanyar “Password”, yasa muka fara da bayani kan yadda “Password” yake – ma’anarsa, da nau’ukansa, da siffofinsa, da kuma ka’idoji ko dokikin zaban “Password”.  Daga wannan mako in Allah Yaso, za mu duba sauran bangarori ko dalilan dake sawwake wa dan Dandatsa satar zatin mutane.  Wadannan jerin kasidu dai su ne bangaren karshe na wannan silsila da muka faro wajen watanni biyu ko uku da suka gabata.

Hanyoyin Kariya (2)

A baya, sadda muke bayani kan hanyoyin da ‘yan Dandatsa ke bi wajen tattaro bayanan jama’a, bayan na sata, akwai wadanda suka shafi bayanan da suke tsinta a bola, da wadanda suke tsinta a bolar Intanet, da wadanda suke tsinta a tsofaffin kayayyaki da na’urorin sadarwa – irin su Kwamfuta, da Router, da Flash, da Zip Drive da sai sauransu.  Kasancewar ire-iren wadannan hanyoyi – idan ke kebance tsofaffin kwamfutoci da mutum zai iya saya a hannun wani ko daga wata ma’aikata – basu shahara a wannan bangaren da muke rayuwa ba, ba za mu shagaltu da hanyoyin suka yadu ne kawai.  Sauran kuma a hankali idan sun fara bayyana a nan, sai mu dube su sosai.

Tsofaffin Kayayyaki da Na’urorin Sadarwa

Idan kana da tsohuwar kwamfuta da kake son sayarwa ko baiwa wani kyauta, yana da kyau ka mata wanka da Wanki.  Ba wai ina nufin ka nemo ruwa da muke sha ka wanke ta dasu ba.  Ina nufin ka kwashe duk abin da ke ciki, ka cire dukkan wata manhaja da kasan ka taba shigar da adireshinka na Imel da kuma “Password” a ciki.  Hatta manhajar lilo, wato: “Browswer”; idan baka iya share bayanan da ke kanta na shafukan Intanet din da ka hau ba, ka cire ta kawai (Uninstalling) daga kan kwamfutar.  In da hali, kawai kayi “Resetting” ko “Reformatting” kwamfutar kawai; ta koma sabuwa ta bangaren ruhi, kamar yadda ake kera ta.  Idan kuma ma’adanar Flash (Flash Drive) kake son kyautarwa, ita ma ka goge dukkan abin da ke kai.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.