Gaskiya da Gaskiya (4): Neman Zabin Allah…!

A duk abin da za kayi, wanda halal ne gareka, amma baka san yadda karshensa zai kasance ba, ka nemi zabin Ubangiji. Domin shi ne mahaliccinka, shi ya kaddara maka dukkan abin da kake a rayuwarka, don haka ya fi kowa sanin abin da yafi zama alheri gare ka.

261

Watarana daya daga cikin malamanmu ke sanar da mu muhimmancin neman zabin Ubangiji kan abin da mutum zai yi a rayuwarsa musamman a bangaren mu’amala, sai ya bamu labarin wani bawan Allah da yayi gamo da rashin sa’a. Ya Allah ka mana tsari da irin wannan gamo, amin. Ga yadda lamarin ya kasance.

Malam yace:

Akwai wani bawan Allah da yaje wajen wani malami a garin Kaduna, don neman a taya shi da addu’a don sunansa na cikin wadanda aka kai wa Gwamnan soji na wancan lokaci, za a basu mukamin Kwamishina. Malam na jin haka sai yace masa: “To, za muyi addu’a, Allah sa wannan mukami da kake nema samunsa ya zama alheri a gare ka. In ba alheri bane gare ka, Allah canza maka da mafi alheri.” Nan take sai fuskar yallabai ta murtuke. Don me za a masa irin wannan addu’a? Shi so yake a masa mai ci yanzu; ya samu, ta kowace hanya. Daga nan ya fice a fusace.

Allah mai iko, Mahaliccin kowa da komai. Shi kadai ya san wace hanya yallabai yabi a karshe aka nada shi kwamishina. Ya fara aiki ba da dadewa ba, bai fara jan zare ba, sai kwatsam shubagan kasa mai ci ya rasu! Wannan tasa gaba daya tsarin gwamnati ya ruguje, aka fara aiwatar da bincike. Ana cikin haka sai aka cafke wasu daga cikin jami’an zartarwa na gwamnati, har da yallabai daga cikinsu. Sai Legas, aka rufe su.

- Adv -

Bayan kusan shekara guda aka sake su. Iyalinsa suka zo filin jirgin sama don daukan maigidansu. Yana sauka aka masa jagora zuwa cikin mota. Yana shiga sai yace wa direba: “Gidan Malam….” Direba bai gane ba. Ya sake ce masa: “Gidan Malam…” Direba yace: “Wani Malam…?” yace mu je. Haka ya masa kwatance har suka kai gidan wancan malami na farko.

Suna isowa sai aka masa sallama da Malam. Malam na fitowa sai yallabai yace masa: “Malam ka gane ni kuwa?” Malam yace: “Ban gane ka ba, domin mutane masu zuwa wurina suna da yawa.” Yace: “Ni ne wanda ya zo wajenka kwanakin baya kan batun addu’a…” Sai Malam yace: “Af, na tuna. To yaya aka yi?” Yallabai ya labarta masa daga farko har karshe. Yana gamawa sai Malam yace: “To ai ka ga abin da nake ji maka tsoro kenan. Yanzu mu sake addu’a: Muna rokon Allah ya zaba maka duk abin da yafi zama alheri a rayuwarka.”

Yallabai, cikin babbar murya, yace: “Aaaameeennnn!!!”

Jama’a, tsakani da Allah muna neman shawarar Ubangiji a dukkan al’amuranmu musamman na bangaren mu’amala? Ko muna jiran sai irin ta Yallabai ta fado kanmu?

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    JAZAKALLAH KHAIR

Leave A Reply

Your email address will not be published.