Gaskiya da Gaskiya (3): Cin Amana!

Mafi girman cin amana shi ne ka ha’inci wanda ya fi kowa wajen amince maka. A wannan kissa mai ta da hankali, mai karatu zai ga yadda ake cin amana karara!

264

Cikin shekarar 1999 ne, a daya daga cikin sharhin da yake yi a shafinsa na musamman mai take: “Publisher’s Corner,” a Mujallarsa mai suna: “Hotline,” Alhaji Hassan Sani Kontagora (Magajin Rafi) ya hakaito wani labari mai matukar ta da hankali da tsoratarwa dangane da dabi’u da halayyar dan adam da rashin tabbas dinsa. Kada in cika ku da surutu. Ga abin da yace:

Wani bawan Allah ne mahaifiyarsa ke fama da rashin lafiya. Bayan likita ya duba ta, sai yace sai an mata tiyata don samun lafiya tabbatacce. Kudin tiyatar naira dubu talatin ne (N30,000), wanda shi kuma bai mallake su ba. Hankalinsa ya tashi matuka. A karshe dai ya yanke shawarar sayar da gidansa wanda shi da iyalinsa ke zaune a ciki. In yaso bayan ya sayar, sai ya kama gidan haya, sauran kudin kuma ya san me zai yi dasu.

Nan take ya sanar da amininsa wanda tare suke komai; ci da sha, lafiya da rashin lafiya, talauci da samu, safiya da maraice. Yace masa ya nemo wanda zai sayi gidan. Nan take aka samu mai saya, aka kuwa sayi gida naira na gugan naira har dubu dari biyu da hamsin (N250,000). A ranar da ciniki ya fada a ranar aka biya kudin baki daya. Mai gida ya karbi kudinsa, wanda ya saya kuma ya saurari ranar da za a fice don a mika masa mallaka da takardun gida.

- Adv -

A ranar da wannan bawan Allah ya karbi kudi, cikin dare sai ga baki. Ina nufin barayi kenan. Suka zo da yawa, kowa fuskarsa a rufe da dodorido (Mask). Suka tsorata shi, suka ce kudi suke bukata. Nan take ya dauko kudin ya mika musu, babu ja-in-ja. Bayan sun kama hanya za su fita, sai ya tuna tsohuwarsa dake kwance a asibiti, da cewa ya sayar da gidan ne don ya warware matsalar da ke damunta. Idan suka wuce da wadannan kudade ya yi uku-babu kenan.

Nan take yayi kukan kura ya tari gaban shugabansu, yace masa don Allah ya ceci rayuwarsa ya bashi naira dubu talatin kacal daga cikin kudin, domin ya sayar da gidan ne don ya biya kudin tiyatar da za ayi wa uwarsa. Nan take sai Allah ya jefa tausayi cikin zuciyar wannan shugaba na barayi. Ya ce masa: “Yanzu wannan kudin na gidan nan ne, don wannan daliin?” Yace masa tabbas kuwa. Daga nan sai ya jawo daya daga cikin yaransa, ya kware fuskarsa. Sai yace masa: “Ka san wannan?” Kwamfa! Dubawarsa ke da wuya sai ya ga wancan aminin nasa ne, wanda shi ya nemo wanda ya sayi gidan. Yace: “Yallabai ai wannan aminina ne, shi ya nemo wanda zai sayi gidan ma.” Nan take wannan shugaba na barayi ya harbe shi da harsashi a ka, ya kuma karbi jakar kudin gaba daya ya damka masa, sai yace: “Don Allah ka gafarce mu. Muna neman alfarman ka bamu naira dubu goma ne kacal daga cikin kudin.” Yace wannan kudin da suke so ma don su kashe wata wuta ce daga wata majiya da ta san sun shigo unguwar don yin sata. Nan take ya cire ya basu, suka ja gawar wancan mujirimi suka wuce.

Jama’a, in har amini zai wa amininsa irin wannan, don Allah ku gaya mini: wa za ka amince wa kuma a rayuwar yau?

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    Al’amuran rayuwar ta mu a wannan zamanin sai a hankali.

    Fatan Mu Allah yasa mu da ce a duk inda mu kasancr

Leave A Reply

Your email address will not be published.