Gaskiya da Gaskiya (2): Zuciya, Ma’aunin Dan Adam!

Daga cikin kyauta mafi tsada da Allah Yayi wa dan Adam akwai zuciya da ya bashi. Ita ce gabar dake gaya wa dan Adam gaskiya a kowane lokaci, sai dai yayi marsisi ya ki ji.

113

Bayan wani bincike na musamman da na gudanar mai shafuka 30, mai take: “Tsakanin Zuciya da Kwakwalwa – Wa Ke Samar da Tunani?” na dade ina ta mamaki da al’ajabi kan hikima da kudurar Ubangiji mahaliccin al’ummar farko da na karshe. Malaman kimiyyar kwakwalwar dan adam (Neuroscientists) basu yi kasa a gwiwa ba wajen binciko irin sarkakiyar da ke cikin halittar zuciya, da irin sinadaran maganadisu da take dauke dasu, masu aiwatar da sadarwa tsakanin zuciya da wata zuciyar da ke muhalli daya. Allah buwayi gagara misali.

Sun nuna cewa: yadda kowane dan adam ke aiwatar da sadarwa tsakaninsa da dan adam dan ‘uwansa, haka ma zukata ke aiwatar da sadarwa. Shi yasa ma, a cewarsu wanda bincike ya tabbatar, idan mutum daya na tsaye a wuri, ransa a bace, zuciyarsa a turnuke da kunci, duk wanda ya shigo wurin nan take zai iya gane cewa ba lafiya yake ba. Domin zuciyar ta aiwatar da sadarwa tsakaninta da na wanda ya shigo. Wannan bincike bai wuce shekaru 4 da bayyana ba, bayan shekaru sama da 50 ana ta hakilo.

- Adv -

Bayan wannan nazari ne na kara fahimtar hikimar da ke cikin jera rantsuwowi sama da 10 a cikin SURATUSH SHAMS, don tabbatar da girman tasirin zuciya wajen tasarrufin dan Adam. Malaman tafsiri suka ce babu wata sura a Kur’ani gaba daya inda Allah Ya jera rantsuwa dai-dai har goma, a jere, don tabbatar da wani abu, sai cikin Suratush Shams. Malamai suka ce daga cikin hikimar shi ne: zuciya wata mizani ce da Allah ya baiwa dan adam wajen gano gaskiya da karya, da daidai da kuskure, da mai kyau da mara kyau.

Tun sannan, a duk sadda na saba wa gaskiya sai zuciyata ta ce mini: WANNAN ABIN DA KAYI FA KUSKURE NE, BA DAIDAI BANE. Shin, ni kadai nake jin haka ko ku ma kuna ji?

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    Alhamdulillah!

    Ai malam duk wani abu da mutum zai ji ko yayi ba a rasa wani ma da yake ji ko zai yi.

    Fatan mu Allah yasa mu da ce

Leave A Reply

Your email address will not be published.