Kimiyya da Fasaha a Kasashen Musulmi (3)

Binciken Kimiyya a Kasashen Musulmi

An buga wannan makala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 26 ga watan Nuwamba, 2021.

233

Binciken Kimiyya a Kasashen Musulmi (2)

Waxannan qididdigar da ma’aunan na bayyyana qarara yadda qasashen Musulmai suke koma baya a fagen bincike da yawan buge-bugen sakamakon bincike-bincike a kimiyya da fasaha da makamantansu. Amma sai dai abun farincikin da jin daxin shine akwai zaqwaquran masana kimiyya Musulmai da suka nunawa wannan rashin katavus yatsa suka yi face a fannin su har duniya sallama mu su a fagagen nasu. Babban su kuma na farkon su shine Farfesa Muhammad Abdussalam da a ka fi sani da Abdus Salam da a ka haifa a shekarar 1926 ya rasu a shekarar 1996, xan qasar Pakistan ne da yaci alwashin kawo qarshen koma bayan da qasashen Musulmai ke ciki a vangaren kimiyya da fasaha da qirqire-qirqire a duniya a yau. Abdus Salam na daga jagorori da ‘yan sahun farko a Ilimin kimiyya a tsakiyar qarnin da ya shuxe, wato 20th century da duniyar kimiyya ta sallamawa. Yana daga mutum uku da suka kashe lambar yabo ta Nobel a Physics ta shekarar 1979 tare da sauran mutum biyu ‘yan qasar Amurka masu suna Sheldon Glashow da kuma Steven Weinberg. An ba shi kyautar Nobel xin ne sakamakon gagarumin gudunmowar da ya taka wajen samar da wata nazariyya, wato, ‘theory’ da ake kira da electroweak theory: shi wannan ‘theory’ xin na daga ‘theory’ xin da suka fi girma da qayi da qima a idanuwan masana kimiyya a yau.

- Adv -

Dalilin hakan kuwa shine, shine ‘theory’ a tarihin kimiyya da ya yi bayanin yadda quwwa (forces) wato nau’ukan qarfi nan (dake riqe da abubuwan da Allah ya halitta da ya sanya ba sa suncewa ko su wargaje, wato kamar dai maganaxiso ne) guda biyu jiga-jigai cikin guda huxu da muke da su dake a duniya da xabi’a, wato nature, ke da alaqa da juna : su waxannan forces xin su ake kira da qarfin da ya yimqe maganaxison lantarki, wato, electromagnetic force, da kuma qarfin da ake kira da weak nuclear force (An samu qarin Musulmi da ya qara samun lashe kyautar Nobel a fannin Chemistry mai suna Ahmed Zewail (1946–2016) a shekarar 1999. Har ila yau, a shekarar 2015 ma an qara samun Musulmi daga qasar Turkiyya da ya samu damar cin kyautar Nobel a fannin Chemistry shi ma dai har ila yau mai suna Aziz Sancar, shi har yanzu yana raye).

Duk da Abdus Salam Musulmi ne mai bin addinin sa sau da qafa, amma hakan bai hana qasar sa ta haihuwa ta karve shi da yin maraba da shi ba a tsakankanin shekarun 1970. Kuma wani abin sha’awa dangane da wannan bawan Allah shine, duk da rashin yabawa da korar sa da qasar sa ta haihuwa tayi, hakan bai hana shi jajircewa da yin hovvasa wajen ganin qasar sa ta Pakistan da sauran qasashen duniya na Musulmai sun kai qololuwa a fagen kimiyya da fasaha da qere-qere ba ta yadda su ma za su iya gogayya da kasar Amurka da Turai da sauran manyan qasashen duniya.

Amma sai dai kash! Har Abdus Salam ya rasu a shekarar 1996 mafarkin nasa na ganin qasashen Musulmai sun kai gaci wajen binciken kimiyya da fasaha da qere-qere bai tabbata ba duk kuwa da iya qoqarin sa da ya qarar da rayuwarsa a kan ganin hakan ya cimma gaci. Har Allah ya karvi ransa, bai daina furta cewa “Duk da cigaba da wayewar kai da a ka samu a duniya a yau, babu inda kimiyya da fasaha da bincike ke kuturwar baya kamar a qasashen Musulmai. Hakan ba qaramar illa ba ne ga tazgaro ga su Musulman, saboda ko mun qi ko mun so rayuwa da cigaban kowacce al’umma a yau sun dogara ne kacokan ga yadda suka ba wa bincike a fannin kimiyya da fasaha da qere-qere da sauran ilimai gudunmowa da Kulawa ba.”

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.