Dandatsanci: Wani Sabon Salon Yaki Tsakanin Kasashen Duniya (2)

Kashi na biyu cikin jerin kasidun dake nazari kan sabon salon yakin kutse a tsakanin kasashe. A sha karatu lafiya.

243

Ruwan Dare….

Wannan ta’addanci da kwararru kan harkar kwamfuta suka faro shi shekaru 20 da suka gabata daga sha’awa yanzu ya koma tsagwaron siyasa a tsakanin kasashe, da addinai, da kuma kungiyoyi.  Bayan bayanan da mai karatu yaci karo dasu a baya kan irin matsalolin da kasar Amurka ta yi ta cin karo dasu sanadiyyar hare-hare ta bangaren kwamfuta, sauran kasashe ma ba a barsu a baya ba.  Ba don komai ba sai don ganin wannan aika-aika a yanzu ya zama wata hanya ta musamman da wasu ke amfani da ita wajen daukan fansa kan duk abin da wata kasa ko addini, ko wata kungiya ta musu a fagen siyasa ne, ko tattalin arzikin kasa, ko kuma bangaren addini da al’ada.

Daga cikin misalai tabbatattu har wa yau akwai harin da aka kai wa gidajen yanar sadarwar kasar Isra’ila cikin shekarar 2006, daidai lokacin da take ta gwabza yaki da ‘yan Hizbulla da ke kudancin kasar, a watan Juli.  Daga baya an gano cewa wadanda suka aiwatar da wannan aiki na dandatsanci wanda ya shafi muhimman ma’adanar bayanan hukumar kasar ta Isra’ila, ‘yan Dandatsa ne kwararru masu asali daga kasar Rasha.  Nan take kasar Isra’ila tace lallai hukumomin kasashen Larabawa da ke Gabas-ta-tsakiya ne suka dauke su haya don daukar ramuwa a madadin Palastinawa.  A yayin da take can tana da fafatawa da ‘yan Hizbullah, a cikin gida kuma ana can ana ta mata ta’adi a bangaren bayanai da harkokin cikin gida.

Cikin watan Satumba na shekarar 2010 ne kasar Iran ta sanar da cewa wasu ‘yan Dandatsa sun kai wa manyan kwamfutocin da ke sarrafa cibiyar samar da makamashin lantarki na Yuraniyon da take amfani dasu.  Abin da ya faru kuwa shi ne, an harbe su ne da kwayoyin cutar kwamfuta (Computer Virus) mai suna StuxNet, wadda ta shige cikin babbar manhajar kwamfutocin don aiwatar da ta’addanci.  Nan take hukumar Iran ta zargi Gwamnatin kasar Isra’ila da wannan aika-aika. Tace ko kadan ba ta tababa cewa lallai Isra’ila ce tayi amfani da ‘yan Dandatsa wajen darkake mata kwamfutocin dake tafiyar da wannan cibiya na sarrafa makamashin Yuraniyon.  Domin, kamar yadda tace, daman kasar Isra’ila da sauran kasashen yamma na kyashin ci gaban da take samu a wannan fage, shi yasa suke ta kulle-kulle da  karairayi cewa makamashin Nukiliya ne take kerawa.

Bayan wannan takaddama tsakanin kasar Isra’ila da Iran ya sarara, sai ga sanarwa ta musamman daga bakin Babban Daraktan da ke Lura da Babbar Cibiyar Sadarwar kasar Burtaniya (Communication Headquarters), wato Ian Lobban, cewa lallai kasarsa na fuskantar barazanar sanadiyyar hare-haren aikin Dandatsanci daga wasu kasashe da ya kira “tsageru.”  Wannan sanarwa yazo ne cikin watan Oktoba na shekarar 2010, wato wata guda kenan bayan harin da aka kaiwa kwamfutocin cibiyar Nukiliyar kasar Iran.  Lobban yace a duk wata ‘yan Dandatsa na kaiwa kasarsa hari a kalla sau dubu daya.  A karshe yace lallai kasar Burtaniya na fuskantar hadari mai girman gaske!

Bayan wata guda ne har wa yau aka kai wa kwamfutocin manyan hukumomin tsaron kasar Pakistan hari, inda aka jijjirkita bayanan da ke cikinsu, da kuma sace bayanan da ke ciki.  Wadanda suka aikata wannan aiki kuwa wata kungiya ce ta ‘yan Dandatsar kasar Indiya mai suna Indian Cyber Army.  A cikin  gidajen yanar sadarwar da suka dandatse sun bar sako cewa sunyi hakan ne don daukan ramuwa kan harin bam da wasu tsagerun kasar Pakistan suka kai wani babban otal dake birnin Mumbai, aka rasa rayuwa masu dimbin yawa.  Daman lokacin da aka kai wannan hari akwai rade-radin cewa ‘yan kasar Pakistan ne suka kai, saboda takaddar da ke tsakanin kasashen biyu wanda ya shafi kan iyaka.  Wannan hari na faruwa da wata guda sai wata kungiya mai suna Pakistan Cyber Army ita kuma ta kai harin dandatsanci kan kwamfutocin manyan hukumomin gwamnatin kasar Indiya, don daukan fansa.  Wannan al’amari ya haifar da kace-nace a tsakanin kasashen biyu, inda alaka ta dada tsamari.

- Adv -

Cikin watan Yuli na shekarar 2011 kuma aka aiwatar da wani hari mai muni kan kwamfutocin kamfanonin talabijin da rediya na kasar Koriya ta Kudu (South Korea), inda komai ya tsaya cak, shafukan yanar gizonsu suka tsaya, sannan ma’aikatan kamfanonin suka kasa mu’amala da fasahar Intanet na tsawon sa’o’i.  A wannan da aka kai an sace tsagwaron bayanai masu muhimmanci sama da miliyan 35!  Nan take hukumar kasar tace makwabciyarta ne ta kai wannan hari, wato Koriya ta Arewa (North Korea), don ramuwar gayya kan rashin goyon bayan da suke basu kan matsalolin diflomasiyya da suke samu da sauran kasashen Yamma musamman.

A cikin watan Agusta ne kuma aka hankado wani barna da wasu ‘yan Dandatsa suka kwashe shekaru wajen biyar suna kaiwa (tun shekarar 2006 – 2011), tare da sace dimbin bayanan sirri a kasar Amurka.  Wannan hari, wanda yana daga cikin hare-hare mafiya muni da aka taba kaiwa, ya shafi kamfanoni da hukumomin gwamnatin Amurka kusan 72, ciki har da shahararren kamfanin samar da manhajar magance kwayoyin cutar kwamfuta mai suna McAffe Inc.  Wannan al’amari ya tayar wa hukumar Amurka hankali sosai.  Cikin watan Oktoba kuma sai wasu ‘yan Dandatsa suka kai wa kwamfutar da ke dauke da manhajar da ke sarrafa shahararren jirgin nan mai sarrafa kansa mai suna Predator da kasar Amurka ke ji dashi a fagen fama a yau, wani mummunar hari.  A yayin harin, an sace bayanan da suka kunshi yadda ake sarrafa jirgin, da manhajar da ke sarrafa shi.  Sai da kwararru a wannan fanni suka kwashe tsawon kwanaki 14 suna ta hakilon daidaita wannan manhaja, sannan aka samo kanta.

Tuhuma…

Daga cikin kasashen duniya babu kasar da ta fi kowacce yawan korafi da kukan ana tsangwamarta irin kasar Amurka.  A duk sadda aka kai mata hari ta wadannan hanyoyi na tsarin sadarwa, kasar da take fara tuhuma ita ce kasar Sin. Hatta cikin watan Maris da ya gabata an kai hari kan manyan kamfanonin sadarwa da manyan hukumomin gwamnatin kasar, da al’amura suka lafa nan take masana da kuma kwararru, har da shugaban kasa da kansa suka ce ai wannan hari daga kasar Sin ne.  Bayan kasar Sin, har wa yau gwamnatin Amurka da Burtaniya musamman suna yawan zargin kasar Rasha da ire-iren wadannan ayyuka.  Sannan ana yawan zargin kasar Koriya ta Arewa, duk da cewa kasa ce da a yau kusan an dauka su suka fi kowa talauci a duniya, wanda hakan yasa, kamar yadda kasashen Amurka da sauran kasashen Yamma ke cewa, ba kowa ke iya mallakar hanyar sadarwa ta Intanet ba.  To amma duk da haka ana zargin suna da karfin da za su iya aiwatar da ayyukan Dandatsa.  Wannan lamari ne mai cike da tufka da warwara.  Me yasa?

Babban dalili kuwa shi ne, shi aikin Dandatsanci wani abu ne mai cike da sarkakiya. A farkon lamari galibi kwararru masana harkar sadarwa ne ke aiwatar da shi a radin kansu.  Daga baya suka fara kafa kungiyoyi.  Tabbas za iya yiwuwa a dauke su haya, kamar yadda ake yi a galibin kasashen Yamma musamman Amurka, to amma tabbatar da cewa hukuma ce ke daukan nauyinsu, wani abu ne mai girman gaske.  Na biyu kuma, a wannan zamani da muke ciki da zarar wasu ‘yan Dandatsa sun kai hari, nan take sai Amurka su ayyana cewa daga kasa kaza ce, tun ba a kai ko ina wajen bincike ba.  Idan aka aiwatar da aikin Dandatsanci kan kwamfuta, gane wadanda suka yi hakan, ko daga kasar da aka yi hakan, ko daga kwamfutar da aka aikata hakan ba abu bane mai sauki, ko kadan. Hakan zai dauki tsawon lokaci kafin a gane.  Abu na uku kuma shi ne, dan Dandatsa (Hacker) na iya kasancewa a kasarsa, amma yayi amfani da wata kwamfuta da ke wata kasa don aiwatar da ta’addanci.  Duk mai bincike zai ga lambar kwamfutar da aka yi amfani da ita ne wajen kai harin, wato IP Address, wanda kuma daga nau’in jerin lambobin ne ake iya gane kasar da kwamfutar take.  To amma wanda ya aiko kwamfutar ba a kasar yake ba, daga wata kasa ya sojantar da ita.  Wannan ke sa a kasa gane hakikanin lamari, sai in kama mutum aka yi.

Abu na gaba shi ne, duk da cewa kasashen Rasha da Sin sun yi wa kasar Amurka fintinkau wajen samar da kintsattsen hanyan kariya a fannin tsarin sadarwar kwamfuta, babu wata kasa a duniya daga cikin kasashen Turai har zuwa Amurka da ba ta amfani da wadannan mutane wajen cinma burinta na siyasa ko na tsaro, a boye.  In kuwa haka ne, to don me a kullum ake yawan zargin kasar Rasha da Sin da kuma Koriya ta Arewa, ko a wasu lokuta ma, kasar Iran?  Galibin masu lura da harkokin diflomasiyya suka ce wannan bai rasa alaka da siyasa.  Musamman ganin cewa wadanan kasashe ne da a baya suke da ra’ayoyin siyasa da tattalin arzikin kasa iri daya, kuma har yanzu akwai kawance a tsaninsu.  Har wa yau, kamar yadda bayani ya gabata, kasar Rasha ta dade da bunkasa harkar sadarwar kwamfuta da kariya a kasarta. Masana suka ce tun cikin shekarar 1995 kasar Rasha take samar da masana harkar kwamfuta a hukumance, tare da horar dasu  don sanar da tsaro a bangaren kariyar bayanai a kasar.

Zuwa yanzu bayanai sun nuna cewa kasar Rasha ta horar da masana harkar kwamfuta sama da dubu goma. Wadannan wadanda hukuma ta san da zamansu kenan.  Kasar Sin ma haka, ba a barta a baya ba.  Wadannan kasashe biyu musamman sun dauki harkar sadarwar kwamfuta da muhimmanci wajen habbaka tsaron kasa, da tsaron tattalin arziki ta hanyar baiwa kamfanoni kariya da samar musu da hanyoyin habbaka hajojinsu da dai sauransu.  Daga cikin taimakon da hukumar kasar Sin ke baiwa matasa har da shirya gasa a fannin Dandatsanci, wato Hacking Competition, tsakanin daliban sakandare har zuwa jami’a.  Wadannan na daga cikin dalilan da suka sa ake yawan zargin wadannan kasashe biyu, musamman.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.