Ci Gaba A Fannin Kimiyyar Ƙere-Ƙere a Zamanin Yau

A tare da cewa an samu ci gaba a fannin ƙere-ƙere na asali, wato: “Mechanical Engineering”, sai dai, mafi girman abin da ya haifar da wannan sauyi mai ban mamaki a dukkan fannonin rayuwa – ba ma kimiyyar ƙere-ƙere kaɗai ba – shi ne ci gaban da ake kan samu a fannin kimiyyar sadarwa na zamani, wato: “Information Technology”. – Jaridar AMINIYA, ranar Jummu’a, 2 ga watan Disamba, 2022.

279

Zamanin Jiya da Shekaranjiya

Abu ne sananne cewa tsarin kimiyya da fasahar ƙere-ƙere, a yadda aka sanshi shekaru kusan ɗari da suka gabata, a yanzu ya sauya fiye da zato da tunaninmu. Wannan ƙa’ida ce ta rayuwa, kamar yadda Allah Ya ƙaddara a wannan duniya.  Idan muka dubi tsari da kintsin ƙirar motoci a ƙarnin da ya gabata, za mu ga asali tayoyi uku kawai suke dashi.  Sannan ba su da cikakken rufi, kuma injinsu ƙarami ne, idan ma akwai kenan.  Bayan haka, hatta tayoyin na ƙarfe ne, ba na dafaffen roba kamar yadda yake a yanzu ba.  Haka abin yake a ɓangaren sauran ƙerarrun abubuwa.  Misali, ƙirar akwatin rediyo a zamanin yau ya sha bamban da yadda asalin akwatin rediyo yake a baya.  A baya haƙiƙanin akwatin ne kana gani, mai ɗauke da maɓallan sarrafawa a zahiri.  Amma yanzu ba haka abin yake ba.

Idan muka koma kan sauran kayayyakin amfani a ɓangaren kiwon lafiya ma haka za mu gani.  Daga kayayyakin gwaje-gwajen lafiya a ɗakin gwaji a asibiti, zuwa na’urorin da ake iya duba mara lafiya dasu don gano bugun jininsa da bugun numfashinsa, da na’urorin tantance cuta a mahalli, duk an samu sauyi nesa ba kusa ba.  A ɓangaren kayayyakin amfanin gida ma akwai sauyi fiye da baya.  Mu ɗauki agogo misali; a baya zallan ƙarfe ne mai ɗauke da yatsu masu bugawa kana jin ƙaransu.  Idan na hannu ne ma haka ne. Bambancin kawai na girma ne da bugun sautin.  Amma tsarin aikinsu ɗaya ne.  Da rayuwa ta ƙara ci gaba musamman a ƙasashen da suka ci gaba fiye damu, an samar da na’urorin dafa abinci, da na ɗumama abinci, da kuma na’urorin wankin tufafi da na wanke kwanukan abinci.  Su ma a yanzu duk tsarinsu ya canza.

Ba wannan kaɗai ba, hatta yadda ake ƙera waɗannan kayayyaki duk an samu sauyi.  A baya mutane ake ɗauka masu ɗimbin yawa don gudanar da aikin.  A yanzu masu ayyuka a cibiyoyin ƙere-ƙere  mutane ne ‘yan ƙalilan; sai na’urorin da suke amfani dasu wajen aiwatar da ƙere-ƙeren.  To duk me ya haddasa hakan ne?

Tasirin Kimiyya da Fasahar Sadarwa

A tare da cewa an samu ci gaba a fannin ƙere-ƙere na asali, wato: “Mechanical Engineering”, sai dai, mafi girman abin da ya haifar da wannan sauyi mai ban mamaki a dukkan fannonin rayuwa – ba ma kimiyyar ƙere-ƙere kaɗai ba – shi ne ci gaban da ake kan samu a fannin kimiyyar sadarwa na zamani, wato: “Information Technology”.  Wannan fanni ne yayi ruwa yayi tsaki wajen cusa wa da dama cikin fannonin rayuwa, musamman a ɓangaren kimiyya, rai da ruhi mai tasirin gaske.  Daga fannin likitanci, da safara, da ilimi, da koyarwa, da kasuwanci, da hada-hadar kuɗaɗe, da sadarwa, duk wannan fanni ya yi uwa da makarɓiya a ciki.

Manyan ɓangarori biyu ne ke da alhakin samar da wannan sauyi a fannin kimiyyar sadarwa na zamani. Ɓangaren farko shi ne abin da ya shafi hanyar sadarwa; tsakanin sadarwar wayar-iska da sadarwa ta amfani da fasahohin blutud da infra-red da sauran na’ukan haske dake iya ɗaukan sakon sauti ko hoto mai motsi ko mara motsi.  Waɗannan hanyoyi suna da tasiri matuƙa wajen haɗa alaƙa tsakanin kayayyakin ƙere-ƙere, kamar yadda za mu gani a sashen dake tafe.

- Adv -

A ɗaya ɓangaren kuma akwai na’urorin sadarwa.  Waɗannan na’urori sun haɗa da kwamfuta, da wayar salula, da sauran nau’ukan wayoyin hannu irin su iPad, da Tabs, da kuma kwamfutoci na musamman da ake amfani dasu a cibiyoyin ƙere-ƙere.  Waɗannan kwamfutoci ko wayoyin salula suna ɗauke ne da manhajojin da ake iya tsara dukkan wani nau’in kayan ƙere-ƙere cikin sauƙi, tare da kintsa shi don aiwatar da gwaji.  Misali, duk wata mota da kake gani na zamani, ko wani jirgin sama abin al’ajabi, ko wata na’ura mai ƙayatarwa wajen aiki, to, asalin zanenta da tsarinta da yadda za ta yi aiki bayan an ƙera ta, duk da manhajar kwamfuta aka yi amfani wajen samar dasu.  A nan ne za ka ga ƙwarangwal ɗinta, daga kowane fuska ko ɓangare.

A taƙaice dai, komai a yau ya koma mahalli kimiyyar fasahar sadarwa na zamani.

Muhimman Ɓangarorin da Suka Sauya

Daga cikin misalan dake tabbatar mana da tasirin fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani kan fannin kimiyyar ƙere-ƙere a yau, akwai kayayyakin aikin da ake amfani dasu wajen ƙera motoci, da jiragen sama, da sauran ƙerarrun abubuwa na amfanin rayuwa.  A yanzu ana amfani ne da na’ura mai fasaha, wato: “AI-Controlled Robot”, wajen ƙerawa da kuma maƙala ɓangarorin mota da jiragen sama da sauran kayakkin ƙere-ƙere.  Waɗannan na’urori dai mutum-mutumi ne da aka tsofa musu tsarin tunani da hankali da kintsi, ta amfani da fasahar “Artificial Intelligence” (AI).  Kuma mutane kaɗan ke sarrafa su ta amfani da kwamfuta.  Wanda a baya ko zamunna baya, duk mutane ne ke maƙala waɗannan ɓangarori na kayayyakin da ake ƙarawa.

Haka idan muka dubi tsarin aikin abubuwan da ake ƙarawa.  A yayin da har yanzu ɗan adam ne ke hawa mota ya tuƙa ta, nan gaba lokaci na zuwa da sai dai ka hau ka zauna, motar ce za ta tuƙa ka da kanta, ta kuma kaika inda ka umarceta da zuwa.  A halin yanzu kamfanin ƙera motoci na Tesla na yin gwajin wata manhajar tuƙin mota na tuƙi-da-kanka, don ɗora wa nau’ukan motocinsa dake tafe nan gaba.  Bayan nan, kamfanin Google ma na nan yana ta aiwatar da gwaje-gwaje kan ire-iren waɗannan fasahohi na tuƙin mota. Ba wannan kaɗai ba, a halin yanzu kana iya kunna motarka, ka kuma buɗe ƙofarta kafin isowa inda take, don taƙaitawa.

A baya galibi akwatin rediyo muke saya mu riƙa kamo tashoshi don saurare.  A yanzu fasahar rediyo ta koma wayar salula da giza-gizan sadarwa ta Intanet.  Ko ba ka da akwatin rediyo yanzu kana iya sauraren shirye-shirye ta wayarka ta salula – ko ba ka ko sisi ma a kan wayar.  Ta ɓangaren agogo, bayan samuwar agogo a wayoyin salula da kwamfuta, a halin yanzu akwai agogo da muke iya ɗaurawa a hannunmu, amma masu “hankali” da “basira”.  Waɗannan su ake kira “Smart Watches”.  Suna iya ƙididdige maka takun tafiyarka wajen mota jiki.  Suna iya ƙididdige maka yawa da saurin bugun zuciyarka.  Suna iya ƙayyade maka lokuta da yanayin baccinka, har ma su baka shawara idan ba ka samun bacci yadda ya kamata.

A ɓangaren kayayyakin amfani gida, akwai na’urori ƙerarru da ake ajiye su a gidaje yanzu, masu taimakawa wajen tafiyar da gida.  Mu a nan basu yaɗu ko ba.  Amma a ƙasashen da suka ci gaba, kamfanin Amazon da Google da wasunsu, duk sun ƙera ire-iren waɗannan na’urori.  Ana kiransu: “Smart Home Assistants”.  Umarni kawai za ka basu da murya, su aiwatar.  Idan kana son a kunna fitilar gaban gida ko a kashe, kana faɗa za su kashe.  Idan kana son kunna talabijin, za su kunna maka.  Haka idan wani abu ya lalace a gidan, za su iya gaya maka.  A taƙaice dai, ire-iren waɗannan na’urori an haɗa su alaƙa ne da kowane ɓangare ko abin amfanin da ke gidan, ta amfani da tsari da hanyoyin sadarwa na zamani.

A ƙarshe dai, yana da kyau mu san irin abubuwan da ke faruwa a wannan duniya tamu, ko da kuwa bai kawo inda muke ba.  Domin a ƙarshe dai, komai tsawon zamani, watarana zai riske mu.  Sannan mu yawaita karatu da bincike.  Mu kuma sa ‘ya’yanmu su karanci fannonin ilmin da ke da alaƙa ta kai tsaye da ilmin zamani.  Wannan ne zai bamu ƙarin wayewa a rayuwa, bayan wayewa ta addini a kullum muke ƙara samu.  Allah mana jagora baki ɗaya, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. ibrahim issa says

    assalama alaikum gai suwa mai tarin yawa da fatan alheri zuwa ga wannan fasihin malami baban sadik ina jin dadin karatutukan ka saboda na koyi abu mai tarin yawa arayuwa tada lilin karatun ka da nake bibiya akai akai na gode daga naka ibrahim issa anan bababn birni niger wato niamey

Leave A Reply

Your email address will not be published.