Sakonnin Masu Karatu (2016) (5)

Cikon sakonninku. Idan za a aiko sako a rika rubuto cikakken suna da adireshi, kada a mance. A sha karatu lafiya.

122

Salaamun alaikum Baban Sadik, ina son kayi mani cikakken bayani a kan shafin  Instagram.   Daga Aliyu Kugga Dumfawa, Zamfara

Wa alaikumus salam, Malam Aliyu barka ka dai.  Instagram dai manhaja ce ta wayar salula wacce ake amfani da ita wajen daukawa da yada hotuna daskararru da masu motsi, wato bidiyo kenan.  Kana iya dora hoton bidiyo mai tsawon dakika 15 (15 seconds).  Ana kuma samun wannan manhaja ne a cibiyar manhajojin wayar salula na kamfanoni daban-daban.  Kana iya samu a Play Store na Android, ko App Store na Apple ko kuma Store na Windows Phone.  Bayan wadannan har wa yau, kana iya saukar da manhajar Instagram da wasu magina manhajar kwamfuta suka gina ta App World na wayar Blackberry.  Sannan kana iya yin rajista da mallakar shafi ta hanyar kwamfutarka a www.instagram.com.

Asalin wannan manhaja dai wasu samari ne biyu suka samar da ita; da Kevin Systrom da kuma Mike Krieger.  Hakan ya faru ne a ranar 6 ga watan Oktoba na shekarar 2010.  Amma daga baya hukumar Facebook ta yi zawarcin masu wannan kamfani da su sayar mata da kamfanin, tare da ma’aikatanta guda 13.  Ciniki ya kaya a kan Dalar Amurka biliyan daya ($1,000,000,000).  Wannan ciniki dai ya fada ne a shekarar 2012.  A halin yanzu dai kamfanin Facebook ne ke da wannan kamfani, ba ma manhajar kadai ba.  Kamar yadda kamfanin Facebook ne ya saye manhajar wayar salula mai suna: “Whatsapp.”

- Adv -

Kana iya yin rajista idan ka cika shekaru 13 da haihuwa, har ka mallaki shafi naka na kanka.  A cewar hukumar Instagram, duk abin da masu shafuka suka loda a shafinsu – na hotuna, da bidiyo, da jakunkunan bayanai – nasu ne, hakkin mallakansu ne, ba na kamfanin ba.  Wannan manhaja ta samu karin tagomashi daga shekarar 2012 zuwa 2014, inda masu ta’ammali da manhajar suka kara yawaita, hada har da inganci da yawan hotunan da ake lodawa a kan manhajar a duk dakika guda.  Daga masu rajista miliyan 150 a shekarar 2012, a halin yanzu akwai masu rajista a wannan dandali na Instagram sama da miliyan 300.  Babban dalili, a cewar daya daga cikin shugabannin wannan kamfani shi ne samuwar wayoyin salula na zamani masu na’urar kemara masu inganci.

A halin yanzu dai akwai hotuna sama da biliyan daya da mutane suka loda a wannan shafi.  Kuma, kamar sauran shafuka irin su Facebook da Twitter, shafin Instagram shi ma dandali ne na sada zumunta, amma ta hanyar hotuna da bidiyo.  Kashi 68 na masu amfani da wannan manhaja dai mata ne, a yayin da maza suka dauki kashi 32.  Bayan haka, kashi 50 na masu amfani da manhajar Instagram ta wayar salula dai su ne masu amfani da nau’in “iOS”, wato wayoyin salulan kamfanin Apple kenan.  A yayin da ragowan kashi 50 din kuma masu amfani da manhajar Android ce.

Daga cikin dokokin mu’amala da wannan manhaja dai, haramun ne a loda hotunan batsa, ko masu dauke da abubuwan dake motsa sha’awa, ko zagi ko cin mutuncin wani, ko hotuna masu nuni ko ishara ko shagube ga wata kabila ko addini ko al’adun wasu da nufin wulakanta su.  Duk da haka, daga cikin matsalolin da masu dandalin ke fama dasu akwai matsalar amfani da wannan kafa wajen tallata miyagun kwayoyi, wanda an gane galibin masu dillanci da safaran miyagun kwayoyi na kasar Amurka suna dora hotuna masu dauke da nau’ukan kwayoyi daban-daban don tallatawa ga wadanda suka san harkar.

Wannan, a takaice, shi ne abin da zan iya cewa dangane da shafi ko manhajar Instagram.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.