Alaƙar Tsarin “Cashless” Da Canjin Takardun Kuɗi

Tsarin “Cashless”, kamar yadda nayi bayani a baya, ya ƙunshi taƙaita amfani da takardun kuɗi ne a zahirin rayuwa wajen ta’ammali a tsakanin jama’a; ya Allah wajen saye da sayarwa ne, ko biyan kuɗaɗe a ma’aikatu ko kamfanoni, ko kuma aikawa da karɓan kuɗaɗe a tsakanin jama’a. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 28 ga watan Afrailu, 2023.

196

Daga cikin abin da mafi yawancin ‘yan Najeriya suka jahilta (wanda laifin bankin CBN ne), shi ne haƙiƙanin alaƙar dake tsakanin wannan tsari na “Cashless” da kuma sauya fasalin takardun kuɗi da bankin yayi a ƙarshen shekarar da ta gabata.  Kaso mafi yawa na jama’a sun ɗauka ma wannan tsari na sauya fasalin takardun kuɗi shi ne asalin tsarin “Cashless” ɗin.  Wannan ko kaɗan ba haka yake ba.  In za a bi asali ma, babu tsarin sauya fasalin takardun kuɗi a cikin tsarin “Cashless” da aka samar a shekarar 2012.

Wannan kuskurarren fahimta da jama’a suke dashi kuwa ya samo asali ne daga sakacin bankin CBN wajen wayar da kan jama’a a daidai sadda yaso ɓullo da wannan tsari na sauyin takardun kuɗi, da kuma rashin amfani da tsari mai sauƙi wanda ya ƙunshi mataki-mataki ko zango-zango, don aiwatar da wannan tsari na sauya fasalin takardun kuɗi.  Sannan a karon ƙarshe ma, sai ya alaƙanta tsarin sauya fasalin kuɗaɗen da tsarin “Cashless”, don amfani da canjin kuɗi wajen haɓaka tsarin “Cashless”.  Duk da cewa bankin ya bayyana dalilansa na yin haka a yadda ya zaɓi aiwatar dashi.

Tsarin “Cashless” Daban

Tsarin “Cashless”, kamar yadda nayi bayani a baya, ya ƙunshi taƙaita amfani da takardun kuɗi ne a zahirin rayuwa wajen ta’ammali a tsakanin jama’a; ya Allah wajen saye da sayarwa ne, ko biyan kuɗaɗe a ma’aikatu ko kamfanoni, ko kuma aikawa da karɓan kuɗaɗe a tsakanin jama’a.  Wannan tsari kuma tun shekarar 2012 aka samar dashi, kuma bankin CBN bai gushe ba tun sannan wajen samar da hanyoyi da kuma amfani da dabarun da ya tanada wajen ɗabbaƙa wannan tsari.

Sanadiyyar haka ne aka faɗaɗa nau’ukan bankuna – inda aka samar da bankunan dake ta’ammali da jama’a ta hanyoyi da kafofin sadarwa na zamani zalla, da kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe masu lasisi da sai sauransu.  Sannan aka samar da hanyoyin cira da aika kuɗaɗe, kamar yadda bayanai suka gaba a kashi na 6 da na 7 makonni uku da suka gabata.  Kuma kamar yadda muka gani a maƙalar makon jiya, samar da waɗannan hanyoyi sun taimaka matuƙa wajen rage yawan ta’ammali da takardun kuɗi a ƙasa.

- Adv -

To amma daga baya sai bankin CBN yayi la’akari da cewa duk da haka, akwai da yawa cikin mutane masu hali waɗanda basu karɓi wannan tsari ba, musamman ‘yan siyasa da wasu cikin manyan ma’aikatan gwamnati dake adana takardun kuɗaɗe a gidajensu.  Sannan da yawaitar sace-sace masu alaƙa da samuwar takardun kuɗaɗe cikin sauƙi a ƙauyuka da birane.  Hakan ya fito fili inda ya tabbatar da cewa, cikin naira tiriliyon uku dake yawo a tsakanin jama’a da bankin ya buga kuma ya tantance su, kashi 70 cikin 100 duk suna hannun mutane ne; kashi 30 ne kaɗai ke kaikomo a bankuna.  Wannan, ta la’akari a tsarin tafiyar da tattalin arziƙi, tabbas cikas ne.  Domin hukuma ba za ta iya amfani da hikimomin  gyara tattalin arziƙin ƙasa har suyi tasiri a yanayi irin wannan ba.  Shi yasa ya tsiri sauya takardun kuɗi nan take, don ƙoƙarin zuƙe waɗancan adadi ko kaso mai yawa na kuɗaɗe da mutane suka taskance a gidajensu.

Kurakuran Dake Cikin Sauya Takardun Kuɗi

Ya zuwa watan Fabrairu na wannan shekara, bankin CBN ya tabbatar da cewa ya tattaro naira tiriliyon biyu da biliyon ɗari daga hannun jama’a, sanadiyyar sauya takardun kuɗi da ƙoƙarin hana karɓan tsoffin kuɗaɗe da yayi a baya.  Ta wani ɓangare, kamar yadda na sanar a sama, hakan zai taimaka wajen bai wa hukuma damar iya juya tsare-tsaren tafiyar da tattalin arziƙi, musamman wajen abin da ya shafi matsalar hauhawan farashin kayayyaki da dai sauransu.

To amma gaggawar da bankin CBN yayi ya haifar da matsala mai girma ga al’umma a ƙasar baki ɗaya.  Sannan ga zaɓe ya zo, ta ɗaya ɓangaren kuma yace ga masu garkuwa da mutane su ma, kuma takardun kuɗi suke karɓa.  Don haka, a cewarsa, amfani da wanna salo na datse komai a lokaci guda, shi ne kaɗai zai samar da waraka.

Sai dai kuma, dambarwar da aka samu tsakanin gwamnatin tarayya da wasu gwamnoni ya yi tasiri matuƙa, inda a ƙarshe babban kotun ƙoli na ƙasa ya umarci bankin CBN da ya janye wannan doka na haramta karɓan tsofaffin takardun kuɗi, har sai ƙarshen wannan shekara.  Sai cikas na gaba da wannan tsari na bankin CBN ya haifar wanda ya ƙunshi hasarar kuɗaɗe da jama’a suka yi sanadiyyar cushewar yanayin sadarwa na bankuna, inda aka ta aika kuɗaɗe amma basa zuwa, sannan kai da ka aika an cire maka.

Abu na ƙarshe kuma mafi muni, shi ne, wannan gaggawa na bankin CBN ya haifar da rashin aminci tsakanin masu ajiya a bankuna da su kansu bankunan.  Asali ya kamata banki ya zama mai lamuni ne ga masu ajiya akan cewa duk sadda suka zo neman kuɗaɗensu za a basu ba tare da wani cikas ba, amma wannan yanayi da aka shiga ya sa jama’a sun rasa wannan aminci a zukatansu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.