Tsarin Sadarwa Tsakanin Kwamfutoci (Networking) (1)

Fasahar Intanet ta samo asali ne sanadiyyar musayar bayanai da kwamfutoci ke yi a tsakaninsu. Yau za mu dubi yadda kwamfutoci ke aiwatar da irin wannan sadarwa, wanda ya sauya duniya ta bangaren sadarwa.

218

Mukaddima

Makonni kusan hudu da suka gabata na sanar da masu karatu cewa akwai wasu tambayoyi da aka rubuto masu bukatar bincike don samun gamsassun amsoshi.  A nan take nayi alkawarin samun lokaci don fayyace mana zare da abawa kan abin da ya shafi ire-iren wadannan tambayoyi.  Cikin ire-iren tambayoyin da nake samu akwai wanda ya danganci tsarin da kwamfutoci ke “Magana” ko “mu’amala” da junansu wajen mikawa da kuma karban bayanai, musamman a gajeren zangon Intanet, wato Local Area Network (LAN), a takaice.

To, maimakon gajarta bayani kan wannan tsari, sai na ga dacewan tsawaitawa, iya gwargwadon hali da lokaci da kuma shafi, don kawo gamammen tsarin da kwamfuta (da ma sauran karikitan sadarwa) ke sadar da bayanai a tsakaninsu.  Wannan tsarin sadarwa kuma ba a kan bayanai na rubutu kawai ya tsaya ba, a a, har da abin da ya shafi sauti, da hotuna masu motsi da marasa motsi.  Sai dai kafin mu shiga wannan fage, ina son ba mai karatu hakuri, domin kuwa zai ta cin karo ne da wasu bakin kalmomi, ya Allah na turanci ne ko na Hausa, wadanda na kawo su ne don saukake masa fahimta kan sakon da nake son isarwa a wannan mako da ma makonni biyu ko uku masu zuwa.

A yau za mu yi bayani ne kan tsarin sadarwa tsakanin kwamfutoci, wanda ya shafi dukkan hanyoyin, kamar yadda mai karatu zai karanta a kasa.  A mako mai zuwa kuma mu jero bayanai kan tsarin ka’idar manhajarwasikar hanyar sadarwa wato Imel, da yadda kwamfutoci ke aikawa da kuma karban rubutattun sakonnin da muke rubutawa muna aikawa.  Sai a mako na sama kuma in muna raye, mu samu bayanai kan tsarin sadarwa a tsakanin wayoyin salula da na’urorin kamfanonin da ke sadar da masu wayoyin.  Wadannan bayanai  zasu taimaka mana gaya wajen sanin abubuwa da dama kan abin da ya shafi hanyoyin sadarwa na zamani.  A yanzu za mu shiga filin daga:

“The Black Box Theory”

Kafin mu dukufa, yana da kyau mai karatu ya san wani abu dangane da tsarin da dukkan karikitai da hanyoyin sadarwa na zamani ke gudanuwa a kai.  Wannan zai taimaka masa wajen rage yawan tambayoyin da ka iya haifuwa cikin kwakwalwan sa a yayin da yake karanta wannan bayani da ke tafe.  Domin duk yadda na kai da fayyace bayanai, zai dan yi wahala mai karatu ya samu cikakkiyar gamsuwa ko fahimta, dangane da abin da ake Magana a kai.  Don fahimta kam za a fahimta, iya gwargwado.  Dalilai biyu ne suka haddasa haka; na farko shi ne ganin cewa da harshen Hausa bayanan ke zuwa, wanda kuma ba shi bane asalin harshen da na karanto ilimin daga gareshi. Na biyu kuma, ko da ma da turancin ne, wasu abubuwa ba zasu taba bayyana maka a fili ba, ko da kuwa wadannan na’urori a gabanka suke, ina maka bayani.  Wannan yasa na kawo ka’idar “Black Box”, don rage mana wahalar neman cikakkiyar fahimta.  Kuma ga abin da wannan ka’ida ke nufi.

Na tabbata masu karatu sun taba gani ko ma sun mallaki kayayyakin sadarwa irin su Talabijin ko Radiyo ko wayar tafi-da-gidanka (wayar salula) ko wayar tangaraho (landline) ko kuma kwamfuta ma a takaice.  Idan bamu mallaki duka ba, to a takaice mun mallaki wasu ko wani daga cikinsu.  In ma bamu taba mallakan kowanne ba, to a kalla dai mun taba sarrafa wani daga ciki.  Wadannan kayayyakin sadarwa, muna sarrafa su ne ta hanyoyin da makerinsu ya tanada mana, mafi sauki; daga abin murdawa zuwa matsawa ko dannawa ko kuma turawa – sama ko kasa.  Kuma galibi bamu damu da sanin tsarin yadda injin su yake ba.  Idan ma mun sani, to bamu san me da me ke haduwa, abu kaza da kaza su kasance ba.

Da zarar kana amfani da wayar salula sai ta lalace, ba abin da ya dame ka, daukawa za ka yi zuwa wajen mai gyara.  Amma idan ba lalacewa tayi ba, ba ruwanka da cewa “me da me aka kera injin wannan na’ura dashi”; in har za ka kunna Talabijin ka ya kama Magana da nuna maka hoto, ko ka kunna rediyonka ya fara Magana har ka kama tashoshi, ko ka kunna kwamfutarka ta kama aiki, ba ruwanka da abu kaza ne ya kasantar da kaza, ko kadan.  Kuma da za ka bude injin, ba abin da za ka gani sai wayoyi da sauran karikitai.  Ba ruwanka da tambayar “ta yaya aka yi wadannan ‘yan kananan wayoyi ke jiyar da ni Magana daga wannan akwatin rediyo, ko ganar da ni hotuna daga wannan talabijin?  Wannan tunani, mai sa damuwa da zahirin fasaha ko na’ura kadai, ba tare da sanin yadda na’urar ko fasahar ke sarrafa kanta ba a fasahance, shi ake kira “The Black Box Theory”.  Kuma shi ne tunanin da ke kwakwalwan kusan dukkan mai amfani da kayayyaki ko na’urar sadarwa na zamani a yau.  Kai dai a ci baure, amma ban da tona cikinsa.  A iya tunani na, wannan shi ne Karin maganan da za a iya kwatanta shi da wannan ka’ida ta “Black Box”, a takaice.

To me yasa galibi ake da wannan irin tunani?  Saboda alaka iri biyu ce tsakanin kowace irin na’ura da mai sarrafa ta.  Alakar farko ita ce wacce ke tsakanin na’urar da karan kanta; ma’ana, tsakanin ruhin na’urar, wanda ke sarrafa gangar-jikin da mai mu’amala ke iya gani har take bashi sha’awa.  Wannan yasa dukkan iliminsa na mu’amala ya takaita a nan.  Sai alakar da ke tsakanin sa da na’urar, wanda ke nuna masa tana da lafiya ko babu.  Idan na’urar na da lafiya, wannan shi ne abin da yake so.  Amma da zarar ta fara zazzabi, to ilimin sa ya kare.  Sai dai yayi kirdajen alamun da take nuna masa.  Kuma shi ne abin da zai gaya ma mai gyara, don a binciko matsalar, don gyarawa.   To a takaice dai irin wannan boyayyar alaka da ke tsakanin na’ura da gangar-jikinta, shi ne abin da yafi wahalar fahimta ga mai amfani da na’urar, domin kuwa ba wani abu bane da zai iya gani a bayyane.  Wanda kuma kashi sittin cikin dari na alakar da ke tsakanin na’ura da ruhi ko masarrafan da ke sarrafa ta, alaka ce badiniyyah, wacce ba a iya gani.  To kuma gashi a kan wannan alaka ne za mu kawo kusan dukkan bayanan da zasu biyo baya, in Allah Ya yarda.  Wannan yasa nayi kandagarki a farko, don kada mai karatu yace ”Baban Sadiq yai mana kwange”.  Kai dai a ci baure, amma kada a tona cikin sa.

Ma’anar “Computer Network”

- Adv -

A turancin kwamfuta idan aka ce “Networking”, ana nufin tsarin sadarwa tsakanin kwamfutoci (daga biyu zuwa sama), wajen mikawa da karban bayanai, ta hanyar wasu ka’idoji da kowace kwamfutur ke iya fahimta.  Wannan tsari na daga cikin dalilan da suka haddasa ma kwamfuta shahara wajen tasirin yada ilimi da harkokin sadarwa a duniya gaba daya, ciki har da fasahar Intanet.  Samuwar wannan tsari ya sawwake daman shiga wata kwamfutar daga wata, a cikin gida ne ko a ofis ko kuma a wata jiha ce daban.  Kai a takaice dai kana iya shiga wata kwamfutar da ke wata kasar, kana zaune a dakinka ko ofishinka.  Duk ta albarkacin wannan tsari na mikawa da karban bayanai a tsakanin kwamfutoci.  Yadda kasan mutane na mu’amala a tsakaninsu, to haka ma kwamfuta ke yi.  Af, to me ye abin mamakin?  Mutum ne fa ya kirkira!  Akwai abubuwa biyu da ke haddasa mu’amala tsakanin kwamfuta da wata kwamfutar ‘yar uwanta.  Abu na farko shi ne samuwar kwamfuta a kalla biyu, masu dauke da manyan manhajojin kwamfuta, wato Operating System, irinsu Windows ko Mac da dai sauransu.  A cikin wannan babban manhaja ne ake da Jami’an Sadarwa wato Network Drivers, da kuma Katin Tsarin Sadarwa da ke cikin akwatin kwamfutar, mai suna Network Card.  Abu na biyu kuma shi ne samuwar komatsen da ke sadar da kwamfutocin, a bayyane ko kuma ta wayan iska (Wireless). 

Wadannan komatsen sun hada da wayoyin kebul irinsu Twisted Pair (RJ45), da Twisted Pair (RJ11), da Coaxial Cable da Fibre Optic Cable.  Sai kuma na’urori irinsu Wireless Frequency Radio (Wi-Fi), da Routers, da Switches da kuma Satellite Dish da dai sauran komatse.  Da wadannan ake sadar da bayanai tsakanin kwamfuta da kwamfuta, kai har ma da wayar salula da Talabijin da rediyo. Bayanan da ke fita daga wannan kwamfuta zuwa wancan na yin hakan ne ta hanyar  wutar lantarki da ke bi tsakanin waya da waya ko tsakanin na’ura da wayar iska.  Abin sai a hankali.  Wadannan su ne karikitai na zahiri da mai karatu zai iya gani a yayin da kwamfuta ko wani na’uran sadarwa ke sadar da bayanai zuwa wata ko kuma ga masu kallo ko sauraro.

Nau’uka

Tsarin sadarwa daga kwamfuta zuwa wata kwamfutar ‘yar uwan ta, na daukan nau’i uku.  Akwai tsarin sadarwa ta zahiri da ke shiga tsakanin kwamfuta da wata kwamfutar da ke cikin gida ko daki ko kuma ma’aikata daya, da ke bigire daya, ko da kuwa ba a hade ginin suke ba.  Wannan tsarin shi ake kira Local Area Network (LAN), kuma yana da hanyoyin sadar da kwamfutoci iri biyu ne; hanyar amfani da wayoyi na zahiri, musamman wayoyin Twisted Pair (RJ45) ko Fire-optic Cables, da kuma Switch, musamman idan tsakanin wani gini ne da wani.  Hanya ta biyu kuma it ace ta hanyar wayar iska, wato Wireless, wanda kuma ake iya yi ta amfani da na’urar Wireless Frequency (Wi-Fi), da sauran na’urori makamantan su.  Wannan shi ne tsarin Local Area Network, ko kuma Gajeren Zangon Intanet, a Hausance.

Nau’in sadarwa ta biyu kuma ita ce wacce ta fi wannan fadi; tsakanin gari da gari, ko jiha da jiha, ko kauye da wani kauyen.  Wannan shi ake kira Wide Area Network, wato Faffadan Zangon Sadarwa.  Galibin kamfanoni masu rassa a wasu wurare kamar jihohi ko birane, sun fi amfani da wannan tsari.  Inda za a iya sadar da bayanai tsakanin dukkan rassan, ba tare da wata matsala ba.  Wannan tsari shi galibinsa ta wayar iska ake yinsa, wato Wireless.  A kan kuma yi amfani ne da na’urar sadar da kwamfuta na dogon zango, wato Router, don sadar da bayanai kala-kala a tsakanin zangunan ma’aikatar.  Misali, idan cibiyar ma’aikata wacce ke wani gari, na da iyayen garke biyu; daya na sadarwan Intanet (Internet Server), dayan kuma na rumbun bayanai (Database Server), sai ayi amfani da na’urar Router da kuma tauraron dan Adam wato Mast, don banbance iyayen garken biyu.  Wannan zai ba duk mai son shiga Intanet, da mai son amfani da bayanan da ke tsibe cikin uwar garken ma’aikatan daman yin hakan, ba tare da samun wata matsala ba.

Sai nau’in sadarwa na uku, wanda ya fi kowanne fadi da ban mamaki, wato Intanet.  Sadarwa ne tsakanin kwamfutoci da ke duniya gaba daya, ba ma wani bigire takaitacce ba.  A tsarin Intanet, kwamfuta ce za ta nemo bayanai daga wata kwamfutar da ke uwa duniya.  Watakil shi kanshi mai nemo bayanan ma bai san inda uwar garken take ba, a a, adireshin kadai ya sani.  Wannan hanyar sadarwa na yiwuwa ne ta hanyar wayar iska mafi girma, wanda ke samuwa ta hanyar tauraron dan Adam mai suna Earthlink a turance.  Na tabbata mai karatu ya ma san wannan tsari tuni, don haka ba a bukatar tsawaita bayani a nan.  Sai abu na gaba.

Tsarin Mikowa da Karban Bayanai

A kowane hali ya kasance, a kan tsamu bangare biyu ne wajen gudanar da wannan alaka ta mikawa da karban bayanai tsakanin kwamfutoci; a gari daya suke ko a garuruwa daban-daban; a jiha daya suke ko a jihohi daban-daban; a kasa daya suke ko a kasashe daban-daban, duk tsarin daya ne.  Wannan bangaren shi ne bangaren da ke mika bayanan, wanda ake kira Host ko Server, ko Terminal, a turancin kwamfuta, ko kace Uwar Garke kawai ka huta.  Wannan kwamfuta guda daya ce tinkwal, kuma aikinta shi ne mika bayanai da zarar wata kwamfuta ta bukaci tayi hakan, ta hanyar da ya dace.  Ita wannan kwamfuta har wa yau, tana da manhajarda ke taimaka mata yin haka, ba wai kwamfuta ce irin kowace kwamfuta ba.  A bangare daya kuma, sai wanda ke bukatar bayanan, wanda a turancin kwamfuta ake kira Client.  Da zarar Client ta turo bukatun neman bayanai, sai Host ko Server ta duba dacewan hanyoyin da wannan bukata ya zo.  Idan ingantacce ne, sai ta mika ta hanyar da aka biyo mata.  Idan ba ingantacciyar bukata bace, ba ma za ta iso gareta ba.

Kammalawa

Na tabbata har zuwa yanzu mai karatu na dai ji na ne kawai, ba tare da wata cikakkiyar fahimtar almaran da nake cusa masa a kwakwalwa ba.  Kada ka damu, zuwa mako mai zuwa abubuwa zasu fara budo maka.  Shi yasa nayi kandagarki a farkon makalar, don kada a zarge ni.  A mako mai zuwa, za mu yi bayani ne kan ka’idar da kwamfutoci ke dashi wajen sadarwa a tsakaninsu.  A nan ne kuma za mu san matakai ko masaukai guda bakwai da kowace kwamfuta ke da su, don sadarwa a tsakaninta da ‘yar uwanta.  Wadannan matakai ko masaukai ne ke tattare da ka’idojin mika bayanai.  Idan mai karatu bai sani ba, kwamfuta tafi kowane halitta tsaban kishi da bin ka’ida.  Idan baka bi ka’idarta ba, to kai da samun abin da kake so har abada.  Ba kamar mutum bane, wanda za ka yi ta masa magiya don yayi la’akari da uzurorika.  A duniyar kwamfuta, sai ka bushe a wurin.

A biyo mu mako mai zuwa don samun karashen wannan makala.  A karshe ina mika gaisuwata ga dukkan masu karatu.  Ina nan tafe mako mai zuwa in Allah Ya yarda.  A ci gaba da kasancewa tare damu!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.