Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (16)

Kashi na 16 cikin jerin kasidun da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Asha karatu lafiya.

130

Hanyoyin Magance Satar Zati

Daga bayanan da suka gabata, mai karatu ya fahimci abubuwa da dama da suka shafi wannan tsari na ta’addanci.  Musamman tun daga ma’anar wannan ta’ada, da nau’ukansa, da kuma hanyoyin da masu aiwatarwa ke bi wajen aiwatar da aika-aikansu, har zuwa alamomin dake nuna an sace wa mutum zatinsa sanadiyyar sace bayanansa da aka yi.  Wadannan bayanai manuni ne kan cewa kafin masu wannan al’ada mummuna suci galaba kan mai bayanan, sai da shi kanshi yayi sakaci dasu, ko wadanda ke rike da bayanan nasa suka yi sakaci dasu.  Wannan ke nuna akwai bangarori biyu muhimmai da ‘yan dandatsa ke bi wajen samun wadannan bayanai.

Bangaren farko shi ne ta hanyar mai asalin bayanan.  Misali, ace an sace shafinka na Facebook, ana hawa kai tsaye, ana rubuta shegantaka iri-iri ba tare da sani da kuma amincewarka ba. Zai iya yiwuwa daga sakacinka ne aka samu kalmar izinin shiganka, wato: “Password”, ko kuma an yi kirdado har aka dace da kalmar da kake amfani da ita a matsayin mabudi.  Wannan bangaren farko kenan.  Bangare na biyu shi ne, ta hanyar wanda aka baiwa bayanan ajiya, sanadiyyar huldar kasuwanci, ko aikin gwamnati, ko wata mu’amala ta musayar bayanai.  Misalin wannan shi ne ace kana da akwatin Imel na kamfanin Google (Gmail) ko Microsoft (Hotmail), sai wasu ‘yan Dandatsa suka barko cikin rumbun adana bayan kamfanin Google ko Microsoft, suka kwashe bayanan mutane kai tsaye; adireshin Imel dinsu da kalmomin iznin shigansu baki daya.  Ko kuma ace kana aiki da wata ma’aikata ta gwamnati ko kamfani, kuma sun karbi bayananku sun zuba a runbum adana bayanansu dake kamfanin ko gidan yanar sadarwarsu, sai ‘yan Dandatsa suka barko cikin kwamfutocinsu, suka kwashe wadannan bayanai kai tsaye.  Wannan ita ce hanya ta biyu.

Ko ma ta wace hanya ce, akwai dayan dalilai biyu dake faruwa har haka ta kasance.  Ko dai ya zama sakaci ne daga mai asalin bayanan ko kuma daga hukuma ko kamfanin dake adana bayanansa. Ko kuma tsantsar kwarewar ‘yan Dandatsan ne, da kuma kaddarar Ubangiji, wacce ta riga fata.  Dalili na biyu ba mu iya komai a kanta, domin duk dabararka, mai son kayanka ya shallake ka.  Amma dalilin farko kan wajibi ne mu dube ta. Ta wace hanya mai karatu zai iya tsare bayanansa ba tare da wani dan Dandatsa ya samu kaiwa gare su cikin sauki ba?

- Adv -

Sannan idan har aka samu kaiwa ga bayananka har aka aikata ta’addanci dasu, wace hanya za ka bi wajen kare kanka, musamman mu da muke nan Najeriya?  A kasashe irin Amurka inda suna da tsari na musamman ga mutanen da aka musu irin wannan ta’addanci, matsalarsu kadan ce.  Amma a Najeriya, babu wani tsari na musamman da hukuma ta tanada ga wadanda aka sace bayanansu har aka aikata ta’addanci dasu.  Dole ne ka san hanyar da za ka bi wajen ganin ka baiwa kanka kariya da kariyar Ubangiji, gabanin mummunar sakamakon abin da aka aikata ya tinkareka.

Kariya Gabanin Aukuwar Matsala

A matsatinka na wanda ke da bayanai a wasu gidajen yanar sadarwa na zamani, inda ake baka daman isa gare su don wata maslaha ta rayuwarka, dole ne ka tanadi hanyar kariya ga wadannan bayanai.  Haka idan hukuma ce ko wata ma’aikata, dole ne ta tanadi na’urori da manhajojin da zasu baiwa bayanan jama’a kariya.  Domin wannan zai taimaka wajen kare mutumcin ma’aikatar da kuma kimar ma’aikatanta.  Idan bayanan suna adane a kwamfutocin dake ma’aikatar ne, dole ne a tanadi na’urorin kariyar bayanai.  A baiwa kwamfutocin dake dauke dasu kariya na zahiri.  Da kuma kariya ta ma’ana.  Har wa yau, hatta harabar hukuma ko ma’aikatar, dole ne a sanya kariya.  A lika na’urorin daukan bidiyo na dukkan abin da ke gilmawa daga waje zuwa cikin ma’aikatar a kowane lokaci.  Sannan a cikin ginin aikatar ma inda sauran ofisoshi suke, dole ne a tanadi irin wannan na’urori na daukan hoto.  Sannan a tsakanin kwamfutocin dake dauke da bayanan da kuma sauran kwamfutoci, su ma dole ne a tanadi na’urar da za ta rika lura da nau’in sadarwar dake aukuwa tsakanin kwamfutar da sauran kwamfutocin ma’aika.  Musamman na’urar da ake kira: “Intrusion Detection System” ko “IDS” a gajarce.  Na’ura ce, kuma manhaja ce dake gane kowane irin kutse da ka iya aukuwa tsakanin ma’adanar bayanai da mai son isa gare su.

Idan bayanan ba ma’aikatar suke ajiye ba, suna dauke ne a gidan yanar sadarwa, nan kuma dole na farko ya zama kamfanin da zai gina shafin amintacce ne.  Haka kuma, a samu tsarin kariya a shafin gidan yanar sadarwar, don hana masu yunkurin isa ga bayanan dake ciki isa gare su.  Akwai tsarin kwakulo bayanan dake rumbun adana bayanai a gidan yanar sadarwa da karfin tsiya mai suna: “SQL Injection.”  Da yawa cikin ‘yan Dandatsa kan yi amfani da wannan hanya wajen sinsinowa da kuma kwakulo bayanai ta hanyar fom din ake tanadawa don karban bayanan mutane.  Hanyar mai sarkakiya kuma mai hadari.

A banganrenmu na daidaikun jama’a kuma, hanyoyin da za mu iya baiwa bayananmu kariya dai bai wuce ta zaban kalmar sirri ko “Password” nagartacce.  To amma tsarin Satar Zati bai takaitu ga “Password” kadai ba.  Suna bibiyar “Password” ne don ita ce kofar isa ga bayanan.  Hakikanin manufar ita samun daman isa ga bayanan.  Sauran dalilan sun shafi yadda muke mu’amala da jama’a shafukan sada zumunta, da yadda muke yada bayanmu, da irin mutanen da muke karba abota da dai sauransu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.