Sakonnin Masu Karatu (2022) (3)

Hanyoyin Inganta Shafukan Facebook (Facebook Page)

A duk sadda ka matsa alamar “Like” dake wani shafi (Page), ko karkashin wani rubutaccen sako (Text Post), ko hoto (Image Post), ko bidiyo (Video Post), za a wallafa sunanka a jerin wadanda suka ga wannan sako, kuma suka nuna sha’awarsu gareshi.  Sannan wannan zai sa injin Facebook ya yi hasashen nuna maka wasu sakonni masu alaka da wanda ka kaunata.  Wannan ke tabbatar da tasirin wannan alama ta “Like”! – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 29 ga watan Afrailu, 2022.

213

Ga ci gaban amsar tambayar makon shekaranjiya.  A yau mun ci gaba da bayani ne kan hanyoyin da masu shafukan Facebook (Facebook Page) za su bi wajen inganta shafukansu da habaka su don samun mabiya.  Ina taya mu murnar samun gama azumin wannan shekara lafiya. Allah karbi ayyukanmu baki daya.  Barka da sallah. Allah maimaita mana.

——————

Hanyoyin Inganta Shafukan Facebook (FB Page)

Alama ko tambarin “Like” a Facebook hanya ce da aka tanadar wa masu ta’ammali da bayanai a Dandalin don nuna gamsuwarsu da labarai ko hotuna ko bidiyo da mutane ke wallafawa a shafukansu na kansu (Facebook Account) ko shafukansu na kasuwanci (Facebook Page), ko kuma zaurukan Facebook (Facebook Groups) da sauran wurare.

A duk sadda ka matsa alamar “Like” dake wani shafi (Page), ko karkashin wani rubutaccen sako (Text Post), ko hoto (Image Post), ko bidiyo (Video Post), za a wallafa sunanka a jerin wadanda suka ga wannan sako, kuma suka nuna sha’awarsu gareshi.  Sannan wannan zai sa injin Facebook ya yi hasashen nuna maka wasu sakonni masu alaka da wanda ka kaunata.  Wannan ke tabbatar da tasirin wannan alama ta “Like”!

Don haka, idan har ka lura da cewa adadin masu “Like” a shafinka suna raguwa a kowace rana ko wata, na farko dai ka ji bayani kan mahimman dalilan da na zayyana a makon jiya.  Na biyu kuma, wannan tankade da rairaya da injin Facebook (Feed Filtering) na tace maka adadin “Like” dake shafinka ne, don kawar da na bogi, da barin gangariya.  Hausawa na cewa: “Da haihuwan yuyuyu, gwamma d’a daya kwakkwara.”  A yanzu dai ga hanyoyin da zaka bi wajen dada inganta shafinka don ci gaba da samun karuwar “Like” cikin sauki kuma masu inganci:

Wallafa Sakonni Akai-Akai

Babu abin da dandalin Facebook yafi sha’awa irin wallafa sakonni a shafuka akaia-aki.  Wannan shi ne sinadarin jawo hankulan jama’a zuwa shafuka, musamman na kasuwanci.  Don haka, idan kasuwanci kake, ya zama a kullum kana rubuta sakonni komai gajartan sakon.  Sannan a rika nau’anta wadannan sakonni. Ma’ana a rika sirka su; idan an wallafa sako ya zama akwai hotuna ko hoto a kasansa, ko kuma sakon bidiyo.  Ko kuma a wallafa sakon hoto mai dauke da sakon da ake son isarwa.  Ko sakon bidiyo (hoto mai motsi).  Bincike ya tabbatar da cewa mutane sun fi sha’awa sakonnin dake dauke cikin hotuna da na bidiyo.  Ire-iren wadannan sakonni kan jayo hankalin masu karatu har adadin “Like” dinka su karu a shafinka.

- Adv -

Ingancin Sakonni

Dole ne sakonnin su zama masu inganci, wadanda ke da alaka da manufar shafin, ko da na kasuwanci ne.  Idan sakonnin ba su da alaka da shafin, injin Facebook ba zai basu mahimmanci wajen tallata su ba. Duk abin da za wallafa ya zama mai inganci.  Sannan kada ya saba wa ka’idojin wallafa bayanai a dandalin.  Idan haka ya faru da yawa cikin mutane zasu kai karan sakon.  Hakan kuma na iya sa ko dai cire sakon gaba daya, ko kuma a killace shi ga ganin wadanda ba sa son ganinsa.  Wannan zai rage ma sakon damar samun Karin “Like”.

Tallata Shafin a Wurare Daban-Daban

Kana iya tallata shafinka ta hanyar watsa sakonnin da kake wallafawa ga abokanka ta shafinka na kashin kanka.  Ko ka gayyaci abokanka don suje suyi “Like” a shafin kai tsaye.  Wannan na cikin hanyoyi mafi sauki da shafinka zai samu Karin “Like” ba da tare da wata wahala ba.  Hakanan kana iya raba sakonnin da kake wallafawa a zaurukan Facebook (Facebook Groups) ko WhatsApp, ko Instagram, don samun karuwan mabiya da karuwan adadin “Like”.

Bai wa Facebook Tallar Shafinka

Idan kasuwanci kake da kake cin riba kuma kana son kara fadada abokan hulda ta hanyar shafinka na Facebook, kana iya baiwa Facebook tallar shafin, su tallata maka shi cikin farashi kalilan.  Daga naira 700 kana iya dora tallar shafinka ko manufar da kake son tallatawa, kuma zai isa ga dimbin masu ta’ammali da wannan Dandali a wuraren da kake son ya isa.  Abin da za ka iya tallatawa sun hada da shafin baki daya, da sako na musamman da ka rubuta, ko wani sakon bidiyo, ko wani sako dake dauka kan hotuna, ko kuma idan kana shafin Intanet (Website), kana iya tallata shi.  Tsarin yana da sauki kwarai.

Ganawa ta Hanyar “Facebook Live”

Facebook Live tsari ne dake dandalin Facebook wanda ke baka damar gabatar da jawabai na ilmantarwa, ko sanarwa, ko aiwatar da taro ta amfani da bidiyo kai-tsare.  Kana iya sa lokaci don ganawa da wadanda suke bibiyarka a shafinka, wannan zai taimaka wajen yada shafin, da nuna shi ga abokan masu bibiyarka, sannan kuma a duk sadda aka ziyarci shafin, za a ga wannan bidiyo don sake kallonsa.

Wadannan, a takaice, su ne hanyoyin da za ka iya bi wajen kara yawan masu “Like” a shafinka dake Facebook.  Da fatan an gamsu.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.