Dan Dandatsan (Hacker) Da Yayi Kutse Cikin Cibiyar Hada-Hadar Kudaden Kirifto Ta “Poly Network”, Kuma Yayi Awon Gaba Da Dala Miliyan 610 ($610M), Ya Fara Dawo Da Kudaden Da Ya Wawashe (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 27 ga watan Agusta, 2021.

656

Bayan ingizo nau’ukan kudaden kirifto da kimarsu ta kai dala miliyan 325 ($325 mil), sai salon wannan dan Dandatsa ya canza; inda ya fara jan kafa.  Ya daina aiko kudaden a kan lokaci.  Wannan yasa kamfanin Poly Network ya kwadaitar dashi cewa, muddin ya taimaka ya dawo da dukkan kudaden kamar yadda ya alkawarta a farko, zasu bashi “Kyautar gano kuskuren manhaja”, wato: “Exploit Bounty” na dala dubu dari biyar ($500 mil), kwatankwacin naira milyan 252 (N252 mil) kenan.  Wannan, a cewar kamfanin, don girmamawa ne, ba wai saka masa ba.  Domin abin da yayi, babu mai iya saka masa.  Sai ya amince yaci gaba da ingizo kudaden, kadan kadan, kamar yadda ya saba.  Amma sai yaki aiko da makullan da za a yi amfani dasu wajen bude asusun, don daukan kudaden da ya aiko.

A sako na karshe da ya aiko a ranar laraba sai ya sake canza salo kuma.  Yace zai karbi kudin da aka masa tayi ne kawai ba don ya rike ba, sai don ya baiwa wasu hazikai a fannin kutse, da cewa, muddin suka yi nasarar kutsawa cikin magudanar kamfanin, zai mallaka musu kudin.  Yace shi mawadaci ne, kuma wannan kudin bazai rude shi ba.  Yaci gaba da nanata cewa, ba yayi wannan kutse bane don ya mallake kudaden da ya sata ba, sai don ya jawo hankalin masu kamfanin kan kafofin dake manhajarsu, wanda wasu na iya amfani da su wajen sace kudaden mutane ba tare da an sani ba, lokaci zuwa lokaci.

Tun bayan aiko wannan sako, ba a kara jinsa ba har zuwa sadda nake tattara wadannan bayanai (Talata, 17 ga watan Agusta, 2021).  Sannan, ragowan kudaden da ya aiko, wadanda sune za su cike adadin kudin da ya wawashe (ban da dala miliyan 30 da wani kamfani ya dakile su, ta hanyar hana karbarsu a ko ina), har yanzu ya ki aiko makullan da za ayi amfani dasu wajen fitar da kudaden don mika su ga masu su.  Ana nan dai ana ta tsumayarsa.

Almara Ko Hakika?

- Adv -

Masana harkar hada-hadar kudaden kirifto a duniya dai basu gushe ba wajen yin sharhi kan wannan lamari mai daure kai matuka.  A yayin da dan Dandatsar ke kokarin nuna cewa shi mutumin kirki ne, wato: ‘Dan ‘Dandatsa mai lasisi (“Ethical Hacker”, ko “White Hat Hacker”), ta hanyar nuna cewa bai yi wannan ta’asa don ya mallake kudaden ba, sai don ya jawo hankalin kamfanin Poly Network kan raunin da magudanar kasuwancinsu ke dauke dashi, a daya bangaren wasu masana na ganin wanann kawai yaudara ce.  Domin a ka’idar jawo hankali kan kuskure irin wannan, ba a gudanar dashi a bainar jama’a kamar yadda yayi.

A a, idan kai kwararre ne mai kyakkyawar nufi, kuma ka hango wata matsala da za ta iya jawo hasara ga al’umma ta hanyar na’urorin sadarwar wani kamfani, to, a boye z aka gudanar da bincikenka, bayan ka ci nasarar isa ga abin da bai kamata a ce wani daga waje ya isa gare shi ba na bayanai, sai ka tuntubi kamfanin a boye, daga kai sai su, don sanar dani, da kuma hanyoyin da kayi amfani dasu wajen isa ga bayanan.  Amma a tsarin da wannan dan Dandatsa yabi wajen wawashe wadannan kudade, a cewar masana, sam ko kadan bai yi kama da wanda yayi don fadakarwa ba.

A daya bangaren kuma, wasu na ganin da hadin bakin wasu cibiyoyin hada-hadar kudade aka yi wannan badakala, wanda a cewar masana ya dauki tsawon lokaci ana tsara shi.  Ba abu bane da lokaci daya aka kudure shi tare da zartar dashi ba.  Masu wannan ra’ayi dai na ganin cewa, da ace ba da hadin bakin wasu cibiyoyin hada-hadar bane, da tuni sun dakile kudaden; wannan dan Dandatsan ma bazai iya samun damar sarrafa su ba; sai dai su rube a taskar da ya zuba su.

Ko ma dai mene ne, wannan ke nuna mana cewa akwai sauran aiki a gaban kamfanonin hada-hadar kudaden kirifto dake Intanet, musamman wajen bai wa dukiyar masu aiwatar da cinikayyar kudi a magudanarsu kariya daga ire-iren wadannan matsaloli dake aukuwa lokaci zuwa lokaci.  A cikin makalarmu kashi 12 da ke bayani kan wannan nau’in fasaha na kudaden zamani dake Intanet, wato “Cryptocurrency”, na sanar da cewa a shekarar 2019 kadai, kamfanoni da cibiyoyin hada-hadar kudaden kirifto na Intanet sunyi hasarar kudade sama da dala biliyan 7; tsakanin hare-haren ‘yan dan Dandatsa da dabi’ar mantuwa dake riskar wasu har su mance Kalmar sirrinsu na shiga taskarsu.  Wanda idan hakan ya faru, babu wani da zai iya baka damar canzawa.  Ba kamar banki bane da muke dasu, wadanda dukkan kudaden da ka basu ajiya yana hannunsu ne, idan suka sake kudaden suka salwanta, to, dole su biya ka.  Shi yasa ma dukkan bankuna suna da inshora na iya yawan kudaden dake karkashin kulawarsu.  A tsarin fasahar kirifto, ko nawa ka adana a taskarka, idan aka sace ko ka mance Kalmar sirrinka, babu wanda zai dawo maka dasu, sai tsananin rabo.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.