Sakonnin Masu Karatu (2014) (7)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

67

Assalamu alaikum Baban Sadik, na kasance kasance masoyinka, duk da cewa babu wata alaka da ta taba hada mu, amma ina bibiyar dukkan rubuce-rubucenka da shirye-shiryenka a jaridar AMINIYA da Sunnah TV. To amma wani abin da ke bani mamaki shi ne, a duk sadda na mika tambayata ba ka bani amsa gaba daya, alhali ina ganin yadda kake amsa tambayoyin mutane da dama.  Duk da  haka bazan gaji ba, ga wata tambayar, kila ko na dace a amsa mini ita.  Kamar yadda kayi bayanin yadda ake saukar da manhajar Bluestacks a kan kwamfutar tafi-da-gidanka, to lalle na jarraba, kuma an nuna mini nau’in Widnows na zaba, wato Windows 8 kenan, domin ita ce wacce nake amfani da ita.  Sai aka nuna mini “Download”, na matsa, ta fara, aka nuno mini: “Copying files” tare da layi mai launin  kore, na matsa, ya ci gaba.  Sai da ya kusa karewa sai ya tike; ya kasa gaba ko baya, sama da awa guda, kuma na tabbata ba matsalar tsarin sadarwar intanet bane.  To don Allah meye mafita?  –  Mai kaunarka; Baba Isa, Damaturu, Yobe

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Baba Isa.  Ina godiya da uzuri da ka mini, Allah saka da alheri.  Sabanin yadda ka fahimta, a gaskiya ban ci karo da tambayarka ba.  Akwai hanyoyi guda uku ko hudu da ake aiko mini tambayoyi.  Hanya ta farko ita ce ta hanyar lambar wayar salula da ake bugawa a shafina da ke jaridar AMINIYA.  Hanya ta biyu ita ce ta hanyar adireshin Imel da ke shafina da ke AMINIYA.  Hanya ta uku ta shafina da ke Dandalin Facebook, kana iya aiko mini ta manhajar sako, wato “Message” kenan.  Hanya ta karshe kuma ta hanyar Dandalin Kimiyya da Fasahar Sadarwa da ke facebook.  Kuskuren da wasu ke yi shi ne, sukan bari sai na sanya kasida a shafina, a karkashin kasidar wajen yin tsokaci, sai su rubuta tambayarsu.  Wannan kuskure ne. 

Ba ka rubuto sako a mahallin da aka tanada don yin tsokaci, domin ba dukkan lokuta nake samun karanta dukkan tsokacin da jama’a ke yi a shafina ba.  Domin akwai wadanda ba su samun damar yin tsokaci sai bayan wata guda ko biyu idan sun ga kasidar.  Yanzu idan suka yi, wanda kuma ni hankalina ya koma kan kasidun da na sanya a halin da ake ciki ne, ta yaya za ayi in iya tattara dukkan wadannan tambayoyi da aka yi ta hanyar da ba na tsammani kuma ban ce a rika amfani da hanyar ba?  A min uzuri kan haka. Wadannan hanyoyi guda hudu da na zayyana su ne hanyoyin da nake so a rika amfani dasu wajen aiko mini tambayoyi ko bukatar neman karin bayani.  Domin su ne nake la’akari dasu a yayin da nake tattaro tambayoyin masu karatu a duk sadda na tashi tattara su.

Dandgane da tambayarka, ina kyautata zaton akwai matsalar sadarwa a kwamfutarka.  Domin na yi amfani da wannan manhaja, kuma kafin nan na saukar da manhajar, na loda wa kwamfuta ta, kamar dai yadda kaji na yi bayani a baya.  A halin yanzu ina amfani da Windows 8 ce a kwamfuta ta, kuma na loda manhajar babu matsala.  Don haka ina kyautata zaton akwai matsala ko dai kan yanayin sadarwar Intanet, ko kuma matsala a shafin.  Idan ta sake kasancewa, kana iya kashe tsarin (Cancel), ka sake loda (Install) mata a karo na biyu.  Idan har ta ci gaba da nuna maka haka.  Ka bar wancan ka sake saukar (Download) da wata manhajar daban.   Ta yiwu sadda kake saukar da manhajar an samu dan yankewar yanayin sadarwar Intanet, wannan ya raunata ta, aka samu yankewa (Broken Link) a titin da kwamfutar take bi wajen saukarwa.  Wannan na iya sa manhajar ta zama gurguwa (Corrupt).  Idan ka sake saukar da wata manhajar lafiya lau, sai ka loda (Install) mata.  Da yardar Allah zai yi.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakaatuhu, da fatan an yi sallah lafiya. Ina mika godiya ta saboda ilimantar da mu da kake yi ta wannan dandali mai albarka.  Misali, idan mutum yana da shafi a Dandalin Facebook sai Allah ya karbi rayuwarsa, a matsayina na amininsa, zan iya rufe shafin nasa gaba daya? – Auwal Ahmad Abba

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Auwal.  Lallai kana iya rufe shafin idan har kana da suna da kalmar iznin shigarsa, wato “Username” da kuma “Password” kenan.  Amma idan ba ka da wadannan bayanai, babu yadda za ayi ka iya rufe shafin.  Sai dai ka barshi hakan kawai, illa maa shaa Allahu.  Amma kana iya rubuta sako a shafin cewa mai shafin fa ya rasu.  Don duk wanda zai tura masa sako zai fahimci hakikanin lamari.  Allah sa mu cika da imani, amin.


Assalamu alaikum, wasu sun ce wayar salula ba ta da amfani ga al’umma domin tana  kashe aure, kuma tana sa mutane su kasance makaryata.  Wai shin haka ne?  –  Bala Shamsiddeen Tari

Wa alaikumus, barka ka dai Malam Bala.  Wannan zance ne da idan ka dubi rayuwar al’umma za ka ga haka ne.  Amma a tare da haka, ba na tunanin shawarar da ake bayarwa shawara ce mai kyau, saboda akwai maslaha mai dimbin yawa cikin amfani da wannan na’ura ta sadarwa.  Tabbas wayar salula ta sha zama dalili na kashe aure, sannan jama’a da yawa suna yin amfani da wannan na’ura wajen zurfafa karerayin da suka saba yi ko da babu wayar salula a tare dasu.  Wadannan dabi’u da ka zayyana guda biyu suna daga cikin miyagun dabi’un mutane wajen mu’amala da wayar salula.  Idan muka fahimci haka, sai mu ga cewa ashe ba wayar salular bace ke da matsala, a a, mutanen da ke amfani da ita ne masu matsalar.

A ka’ida ta shari’ar Musulunci, duk wani abin mu’amala asalin hukuncin amfani dashi shi ne halacci, ba haramci ba.  Tana iya yiwuwa kace to ai a Mazhabar Malikiyya ana karfafa amfani da ka’idar “Toshe kafar hana barna” wato “Sadduz zaree’ah,” wanda kuma wannan ka’ida ita ce a kunshe cikin kusan kashi sittin cikin dari (60%) na ayoyin dake dauke da hukunce-hukuncen hani a cikin Kur’ani.  Wannan haka ne, amma kafin wannan ka’ida tayi tasiri sai an lura da maslaha ko rashinsa.  Amfani da wayar salula na tattare da maslaha mai dimbin yawa da a wasu lokuta ma yana iya zama wajibi amfani da ita.  Fa’idojin amfani da wayar salula ba za su kirgu ba, amma munanan ayyukan da ake yi da wayar salula ana iya kididdige su, ko da ta hanyar hasashe ne.

A karshe dai, don wasu na amfani da wayar salula wajen aikata munanan ayyuka, ba dalili bane cewa a daina amfani da na’urar.  Kamar yadda wasu ke amfani da mota wajen aikata fashi da makami, da daukan barasa, da zuwa wajen karuwai ko daukansu, da duk wata ta’asa da shari’a ta haramta, bazai zama dalili na haramta amfani da mota ba, ko kadan.  Don haka, idan kai ka zabi ka daina amfani da wayar salula sanadiyyar wadannan dabi’u ko don tsoron kauce ma aukuwarsu a gare ka, wannan zabi ne irin naka, kuma kada ka haramta wa kanka balle sauran mutane. Yin hakan wani babban laifi ne a shari’ar musulunci.  A al’adance ma bazai karbu ba balle a shari’a. Da fatan ka gamsu da wannan gajeren tsokaci. Allah sa mu dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.