Yadda Aka Gina Manhaja da Shafukan Facebook (3)

Ga kashi na uku cikin jerin kasidun dake mana bayanin tsari da yadda aka gina manhaja da shafukan Dandalin Facebook. A sha karatu lafiya.

269

Da Me Aka Gina Shafukan Facebook?

Dandalin facebook na dauke ne da wani tsari mai ban mamaki, mai ban al’ajabi, mai kayatarwa, amma ga wanda ya san tsarin sadarwar zamani da yadda yake aiki a yau.  Amma ga wanda bai sani ba, sai an masa kwatance mai saukin saukakewa, mai saukin fahimta.  Muna iya fahimtar wannan sarkakiya ne daga irin alkaluman bayanai da ke fitowa daga masana kan yadda wannan dandali ke aiki, kamar yadda muka karanta a makonnin baya.  Uku daga cikin manyan kalubale da ke fuskantar hukumar gudanarwar dandalin facebook dai su ne: dandazon sarkakiyar da ke cikin bukatar bayanai daga masu mu’amala a shafin a kowane dakika guda, da tarin yawan bayanai da ke taruwa tuli-tuli, a duk dakika guda, da kuma sarkakiyar da suke fuskanta wajen jera bayanai ta la’akari da mahimmancinsu wajen masu bukata a kowane lokaci.

Kada mai karatu ya rikice.  Duk da wannan sarkakiya da yake jin ina ambato, abin mai sauki ne a misalin yau da kullum.  Na yi bayani a baya cewa dandalin facebook na dauke da manyan bangarori uku ne.  Akwai bangaren farko, wanda shi ne kamar idon-gari; in da duk masu mu’amala da shafin ke mu’amala da shi.  Wannan bangare ne ke karbar sakonka –  na bukatar neman aboki, ko neman wani shafi, ko tura sakon ta’aliki, ko wata bukata dai a takaice  – kuma shi ne mai maido maka da jawabi – kan abin da ka bukata!  Wannan a fili kenan; abin da kuma kake gani kenan.  Amma ba shi ne mai hakikanin aikin ba.  Shi dan sako ne.  Wannan bangare shi suke kira “Front-End” a turancin kimiyyar sadarwa na zamani.

Sai bangare na uku, wanda ke dauke da dukkan bayanan da muke mu’amala da dasu a makare.  Wannan bangare shi ne bangaren ma’adanar kwamfuta mai dauke da babbar manhajar taskance bayanai da aka fi sani da “Database Servers” a turance.  Wannan bangare ne ke rike da dukkan bayanan da suka shafi dukkan masu shafi a dandalin facebook, a ajiye.  A turancin kimiyyar sadarwar zamani ana kiran wannan bangare da suna: “Back-End,” ko bayan gida.

Sai bangare na biyu wanda ke tsakanin bangaren farko da bangare na uku.  Aikin wannan bangare shi ne kwafo shafukan da masu mu’amala da dandalin facebook suka fi bukata a dukkan lokuta.  Idan ka shiga shafinka a karon farko, wannan bangare zai taskance shafin a ma’adanarsa.  Da zarar ka sake shiga shafinka sai wannan bangare ya gano cewa ai ka shigo dazu, kuma akwai makwafin shafin da ka bukata a baya, sai kawai ya baka shafin nan take, ba sai ya koma asalin ma’adanar da ke bangare na biyu da bayaninsa ya gabata ba.  Wannan bangare shi ake kira “Caching System.”  Amfanin samar da wannan bangare shi ne don rage saibi ko nawa wajen dauko bayanan da ka bukata dake makare a wancan ma’adana dake bayan fage, ko “Back-End.”   Watakila sai na kawo misali da tsarin banki sannan mai karatu zai fahimta.

A tsarin banki, idan ka kawo musu kudi ajiya, za a karba a jiye a taskar bankin, wanda ke babban bankin Najeriya.  Idan ka bukata ma za a je babban banki ne a dauko kudin, sai a biya ka.  To amma ganin cewa kafin a je a dauko maka wani ma yazo bukata, wanda hakan zai kawo tsaiko wajen kaikomo tsakanin bankinka da babban bankin Najeriya, sai kawai aka samar da wata ‘yar karamar ma’adana ta wucin-gadi a cikin bankin.  Wannan ma’adana ita ake kira “Strong Room.”  Maimakon ace duk sadda ka bukaci kudinka aje babban bankin Najeriya a dauko a biya ka, sai aje cikin wannan ma’adana ta “Strong Room” a dauko wadanda aka karba na wasu, a baka.  Idan kuma har lokacin tashi yayi ba a samu masu bukatar karba ba, sai a koma dasu taskar bankin da ke babban bankin Najeriya.  To haka tsarin karba da mika bayanai yake a dandalin facebook.

Kada mai karatu dai ya mance cewa muna kan bayani ne kan: “Da wani irin kayan aiki aka gina shafukan dandalin facebook?”  To ga bayani nan dalla-dalla, filla-filla, sanka-sanka!

Bangaren “Idon-gari”

Bayan dukkan tanade-tanaden da hukumar Facebook suka yi wajen inganta ma’adanarsu da shafukan da masu mu’amala ke mu’amala dasu a dukkan lokuta ta bangaren kwamfutoci masu babban mizani da kuma karfin masarrafar sarrafa bayanai, har wa yau akwai wasu tanade-tanade da suka yi wajen inganta shafukan ta bangaren masarrafa ko manhajar da ke agaza wa masu shiga wannan dandali a kullum.

Shafukan facebook dai an gina su ne ta amfani da wasu dabarun gina manhajar kwamfuta na zamani, kuma masu kayatarwa.  Wadannan dabarun gina manhajar kwamfuta dai suna taimakawa ne wajen gina shafuka masu kayatarwa, masu iya mu’amala da mai ziyara, masu iya “fahimtar” jujjuyawar mai ziyara daga shafi zuwa shafi, masu kuma taskance dukkan bayanan da mai ziyara ke zubawa a shafinsa, da wadanda yake nema daga wasu shafuka, da kuma wadanda yake aikawa zuwa wasu shafukan da ba nasa ba. Akwai jerin dabarun alkinta bayanai da gina shafukan intanet da ake wa lakabi da LAMP, wato: LINUX, da APACHE, da MYSQL, da kuma PHP.  Ga takaitattun bayanai nan kan kowanne.

- Adv -

LINUX

Wannan ita ce babbar manhajar da kwamfutocin hukumar Facebook ke dauke dasu. Kwamfutocinsu ba sa amfani da babbar manhajar Windows, saboda dalilai na tsaro da kariyan bayanan mutane. Babbar manhajar LINUX manhaja ce ta kwamfuta, wato Operating System da wani bawan Allah dan kasar Finland mai suna Linus Torvals ya gina shekaru sama da 20 da suka gabata. A halin yanzu an inganta wannan babbar manhaja, kuma galibin manyan kamfanonin duniya – tsakanin na kwamfuta da kamfanonin kasuwanci da hukumomin manyan kasashen duniya – na amfani da wannan babbar manhaja ne.  Tana da inganci wajen kariya, da inganci wajen tsaro, da inganci wajen sarrafa bayanai (Data Processing) cikin sauki.  Akwai kamfanonin da suka gina kwamfuta ta musamman mai dauke da wannan babbar manhaja, sannan akwai inda ake bayar da wannan babbar manhaja tsuranta, kyauta.  Akwai nau’ukan babbar manhajar LINUX da yawa da aka samar, galibinsu kyauta ne. Daga cikinsu akwai babbar manhajar Ubuntu, da Kubuntu, da kuma Lubuntu. Dukkansu kyauta ne. A baya ba kowa ke iya mu’amala da wannan babbar manhaja ba, saboda wahala da rashin hanyoyin mu’amala da mai mu’amala cikin sauki, wato Graphical User Interface (GUI). Wannan yasa sai wane da wane daga cikin kwararru a fannin ilmin kwamfuta ke iya sarrafa ta. Amma daga baya an samar da wadannan hanyoyi masu sauki irin wadanda ke dauke cikin babbar manhajar Windows na kamfanin Microsoft.

Daga nan za mu fahimci dalilan da suka sa hukumar facebook amfani da wannan babbar manhaja ta LINUX. Domin suna mu’amala ne da bayanai masu dimbin yawa, masu samuwa a lokaci guda, kuma nau’uka daban-daban, a yanayi daban-daban. Sannan a kowane lokaci akwai masu bukatar wadannan bayanai.

APACHE

Manhajar APACHE kuma ana amfani ne da ita wajen aiwatar da sadarwa a ka’idar mu’amala da fasahar Intanet. Manhaja ce mai dauke da titi, ko hanya, da kuma ka’idar da ke sawwake wa titin isar da sako daga kwamfuta zuwa kwamfuta. A takaice dai, masarrafar ka’idar sadarwar Intanet ce (Web Server), kuma kyauta ake samunta, kamar yadda ake samun wasu daga cikin nau’ukan babbar manhajar LINUX kyauta. Kamfani ko hukumar Facebook sun zabi yin amfani da manhajar APACHE ne don ita ce tafi dacewa da babbar manhajar LINUX wajen adanawa da kuma sarrafa bayanai.  A takaice dai, ita ce manhajar da tafi alakantuwa da babbar manhajar LINUX wajen samun ka’idar sadarwa ta Intanet, kamar yadda babbar manhajar Windows tafi dangantuwa ga ka’idar sadarwar Intanet mai suna Internet Information System, wato: IIS na kamfanin Microsoft kuma wanda ke dauke da’iman cikin babbar manhajar Windows.

MYSQL

Manhajar MYSQL kuma shahararriyar manhajar rumbun adana bayanai ne na Intanet.  Babban aikinta shi ne adana bayanai da ake shigarwa cikinta, ta hanyar jera su dabaka-dabaka, cikin tsari, da kuma sawwake hanyoyin nemansu ko samunsu a duk sadda ake bukata, cikin sauki. Cikakkiyar lafazin SQL shi ne: Structured Query Language, kuma daga cikin suka suka inganta tare da samar da wannan tsari na neman bayanai a rumbun adana bayanai cikin sauki akwai kamfanin Microsoft.  Asalinta dai dabaru ne na sarrafa bayanai, wato Script.  Wannan manhaja ta MYSQL tana dauke ne da wannan ginannen tsarin nemo bayanai mai suna SQL, kamar yadda bayanai suka gabata a baya.  Ta amfani da wannan manhaja ne hukumar Facebook ke taskance bayanan masu shafuka, da kuma taimaka musu nemo bayanai cikin sauki da tsari ba tare da wahala ba; a waya ne, ko a kwamfuta.

PHP

Cikakkan lafazin PHP shi ne: Hypertext Preprocessor, kuma daya ne daga cikin dabarun gina shafukan Intanet masu sauki da inganci.  Duk wanda ya saba mu’amala da fasahar Intanet shekaru masu yawa, zai ga da bambanci tsakanin shafukan Intanet da ya saba gani da kuma shafukan Facebook da yake mu’amala da su a kullum.  Domin shafukan Facebook suna da dabi’u masu dimbin yawa na iya mu’amala da mai ziyara a shafin. Idan baka sani ba sai ka dauka kamar wani ne ke zaune musamman don yin mu’amala da masu ziyara a shafin facebook, a duk sadda suka nemi bayanai, ko suka bukaci shiga ko fita daga shafinsu.  Domin shafukan Facebook suna sauyawa a dukkan kowane dakika guda, muddin wani canji ko sauyi ya samu a cikinsu, ba sa jiran sai wani mutum ya sarrafa su kafin su sauya. Kamar yadda suke iya fahimtar da wace irin na’urar kake shiga shafinka, ko a ina kake, ko kuma da wani lokaci kake shiga; duk shafukan facebook na lura da kai ta hanyar dabarun da ke dauke a cikinsu.  Haka idan kana da wata dabi’a ta musamman wajen mu’amala da mutane, misali kana yawan aika musu sakonni, ko kana yawan neman abokai barkatai ba tare da ka’ida ba, ko kana yawan shiga shafukan mutane da leke-leke, duk suna lura da kai, kuma suna aikawa da bayanai gamsassu kan dabi’unka.  Daga lokacin da suka fahimci ka cika wasu sharudda na mutumin da aka ce musu su tuhume shi, to nan take sai su hana ka shiga sai ka gaya musu waye kai.  Ire-iren wadannan abubuwa ba wani bane ke zaune yake yinsu, a a, shafukan ne ke aiwatar da su, sanadiyyar tsarin gini da aka musu.  To, wannan gini kuwa ya samu ne ta sanadiyyar dabarun gina shafukan Intanet mai suna PHP.

Wadannan su ne muhimman manhajoji ko masarrafai da hukumar Facebook ta fara amfani dasu a karon farko wajen alkinta bayanan masu ziyara da masu shafuka a dandalinsu.  To amma kamar yadda bayanai suka gabata a baya, a yanzu an samu ci gaba wajen yawa da tsari da kuma hanyoyin da masu ziyara ke bi wajen ziyarta ko mu’amala da juna a wannan dandali nasu.  Samuwar haka ne ya sake samar da wani yanayi mai cike da kalubale ga hukumar wannan dandali.  Saboda yawaitar masu ziyara, da yawaitar masu bude shafi a dukkan dakika ko minti na duniya, da kuma yawaitar masu neman bayanai a wannan dandali.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.