Sakonnin Masu Karatu (2022) (2)

Raguwan Adadin Likes a Shafin Facebook

Dandalin Facebook ya samar da wani tsari da ke baiwa mutane damar rufe shafinsu da zarar sun rasu.  Galibi an fi amfani da wannan tsari a kasashen da suka ci gaba.  Dangane da haka, da zarar wani ya mutu, kuma ‘yan uwansa suka sanar da hukumar Facebook, nan take za a cire shi daga adadin wadanda suke bibiyar kowane irin shafi ne ko dandali.  – Jaridar AMINIYA ta ranar 22 ga watan Afrailu, 2022.

174

Ga ci gaban amsar tambayar makon jiya.  A yau mun ci gaba da bayani ne kan dalilan dake sa adadin mabiyan shafukan Facebook (Facebook Page) ke raguwa.  A makon gobe in Allah Yaso za mu Karkare, inda zanyi bayanin hanyoyin kariya da yadda mai shafi zai habaka shafinsa don samun mabiya masu inganci.

——————

Dalilan Raguwan Adadin “Likes”

Shafukan da aka Rufe: Cikin wadanda suka bibiyeka a baya, ana samun wadanda shafinsu ke samun matsala sai hukumar Facebook tarufe account din, wannan zai sa duk wani shafi da suke bi ya ragu da iya adadin wadanda aka rufe shafukansu ta wannan dalili.  Idan mutane 100 suna cikin wadanda suka yi “Like” din shafinka, adadin mabiyanka za su ragu da wannan adadi.

Wadanda Suka Rufe Shafinsu da kansu:  akwai kuma wadanda ke rufe shafukansu da kansu don rabuwa da dandalin, ko rufewa ta wucin-gadi (Deactivating) ko kuma goge shafin ma baki daya (Deleting).  A duk sadda wani ya rufe shafinsa don radin kansa, injin Facebook zai cire shi daga cikin dukkan wata alaka da yake da ita a dandalin.  Misali, idan ya matsa “Like” a shafinka na kasuwanci, za a cire shi daga cikin adadin dake shafinka.  Wannan zai sa kaga adadin masu “Like” a shafinka ya ragu nan take.

Shafukan Wadanda Suka Mutu:  Dandalin Facebook ya samar da wani tsari da ke baiwa mutane damar rufe shafinsu da zarar sun rasu.  Galibi an fi amfani da wannan tsari a kasashen da suka ci gaba.  Dangane da haka, da zarar wani ya mutu, kuma ‘yan uwansa suka sanar da hukumar Facebook, nan take za a cire shi daga adadin wadanda suke bibiyar kowane irin shafi ne ko dandali.

- Adv -

A cikin shekarar 2015 hukumar Facebook ta sanar da wadannan dalilai uku da suka gabata a sama.  Tana mai fadakar da masu shafukan kasuwanci a Dandalin cewa idan sun ga raguwa daga adadin “Likes” din shafukansu, to, saboda ta fara yin tankade ne da rairaya kan wadanda ta rufe shafukansu, ko suka rufe shafukan da kansu ko kuma wadanda suka rasu aka rufe shafukansu.  Ta ce wannan zai duk wanda ke cikin wadannan dalilai da ta zayyana, zai shafi shafukan kasuwanci.  Sannan ta tabbatar da cewa, da wadanda suke da matsala da shafukansu, da zarar shafun sun dawo, za a mayar da alakar da suke dashi da kowane shafi ne.  Misali, idan mutum ya rufe shafinsa da kansa na wani dan lokaci, sai daga baya ya sake budo shi, to, za a mayar da shi sahun wadanda suke da rajista da kowane shafi ne ma.  Sai dalilai na gaba.

Manhajar “Likes” Na Jabu:  Akwai kuma wadanda ke amfani da manhaja (application) wajen bibiyar mutane don manufar kasuwanci. Wannan su suka fi yawa. A duk sadda facebook suka yi tankade da rairaya, nan take suke tsame su daga dukkan wani shafi da suke bi ko suka yi like.  Wannan zai sa idan kana da irin wadannan nau’ukan “Likes” din na jabu a shafinka, za ka ga ragowa daga adadin abin da kake dashi a baya.  Wannan tankade da rairaya da hukumar Facebook ke yi, kusan kullum ne.  Kamar lokaci na musamman suka ajiye don gudanar da manhajar da ke yin tankade da rairayar.

Manhajojin “Facebook Auto Liker”:  Idan kana yawan amfani da manhajojin wasa (Games apps) dake Facebook ko Instagram misali, za a bukaci ka baiwa app din dama yaga dukkan bayananka.  Akwai apps din da ke amfani da wannan dama su rika yin likes a shafukan mutane da kamfanoni don manufofin kasuwanci.  Wadannan su ake kira: “auto liker”. Cikin dan kankanin lokaci suna iya yin “Like” sama da miliyan a shafukan mutane ba tare da bata lokaci ba.  Wadannan jabun “Likes” ne, kuma hukumar Facebook tana da wata manhaja ta musamman da take amfani da ita wajen gano ire-iren wadannan nau’ukan “Likes”.  Shi yasa take cire us kai tsaye.

Don haka, idan kayi rashin sa’a ire-iren wadannan manhajoji suka shige “Profile” dinka kuma suka rika yin “Like” a shafinka, da zarar hukumar Facebook ta yi tankade da rairaya, nan take zata zagwanyar da adadin “Likes” din dake shafin.  Sai dai kuma, ta wani bangare, rage wadannan jabun “Likes” din alheri ne. Domin tace su ake yi don samar maka da asalin mutane ba manjaha ba.  Don haka, idan kasuwanci kake yi, sai ya zama duk wadanda ke ganin sakonninka da hajojinka za su zama mutane ne zalla ba manhajoji ba, wadanda ba su da hankali, balle ma su iya aiwatar da wata alaka ta kasuwanci tsakaninka da su.

Mako mai zuwa in Allah Ya kai mu, zan yi bayani kan hanyoyin da za ka iya bi wajen habaka shafinka, da inganta adadin masu “Likes” da kuma samar da bayanan da za su jawo maka jama’a cikin sauki.

A ci gaba da kasancewa tare da mu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.