Sakonnin Masu Karatu (2012) (4)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

138

Salaamun Alaikum Baban Sadik, da fatan alheri gare ka. Shin, wadanne abubuwa ne ake ce musu “The Seven Wonders of the World?”  Sannan kwanakin baya ka yi bayani kan fasahar Bluetooth, kace akwai tabarau mai dauke da wannan fasaha.  Don Allah ina son karin bayani.  Daga Ummu Haidar, Gombe.

Wa alaikumus salam, dubun gaisuwa da fatan alheri ga Maman Haidar, Allah saka da alheri, amin.  Wadannan abubuwa da ake kira “The Seven Wonders of the World” wato abubuwa bakwai masu ban mamaki a duniya, wasu al’amura ne ko wurare, ko wasu nau’ukan fasaha/ilimi da aka gano tasirinsu a duniya a wani lokaci na musamman.  Shi yasa tantance su ma yake da wahala. Domin abubuwa ne ko wurare ne da suka shafi zamunna daban-daban, da kasashe daban-daban.  Don haka, cewa ga wadannan abubuwa da a duniya su kadai ake kira da wannan lakabi su kadai, ba abu bane mai yiwuwa.  Akwai abubuwa guda bakwai masu ban mamaki da suka shafi ilimin sararin samaniya kadai, wato: Seven Wonders of the Solar System. 

Akwai wadanda suka shafi karkashin teku, akwai wadanda suka shafi fannin kere-kere, akwai wadanda suka shafi wasu kasashe kadai, akwai wadanda kuma wasu mujallun kasar Amurka da suka tantance a matsayin su ne abubuwa bakwai masu ban mamaki a duniya.  Don haka, idan aka ce za a yi magana kan abubuwa bakwai masu ban mamaki a duniya, to dole ne a tsawaita bayani, don tantance su, da tsari ko yanayin da aka yi la’akari da shi/su, da daida sauransu.  Amsa tambaya irin wannan mai harshen damo kuwa, ba abu bane da zai iya samar da amsa ta kai tsaye.

Bangaren tambayarki na biyu kuma kamar yadda kika ce, na yi bayani kan samuwar nau’in fasahar Bluetooth da ke lake a jikin tabarau. Wannan tabbas yana nan, kuma amfaninsa shi ne aiwatar da tsarin sadarwa tsakanin wayar salularka ko kwamfutar da kake amfani da ita mai dauke da wakokin da kake son sauraro ta amfani da lasifikan wannan tabarau, don sauraro kai tsaye ba tare da wata matsala ba.  Ba wannan kadai ba, akwai na’urar sauraren wake na jikin mota mai dauke da fasahar Bluetooth, akwai talabijin mai dauke da fasahar Bluetooth, da dai sauran kayayyaki/na’urori/fasahar sadarwa na zamani.  Da fatan kin gamsu.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki, yaya jama’a, kuma yaya su Sadik? Ina maka fatan alheri. Ka kasance cikin koshin lafiya.  Sako daga masoyinka: Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Tunshama Quarters, Ketare, Kano: 08095588320

Wa alaikumus salam, ina matukar godiya sosai Malam Yahuza, Allah saka maka da alheri, amin.  Hakika kana matukar karfafa mini gwiwa da sauran masu aiko sakonni makamantan wannan.  Allah sa mu cika da imani, amin.


Assalaamu alaikum, ina son Baban Sadik ya kara mini fashin baki kan yadda ake tsara Mudawwana, wato Blog.  Ta yaya zan sa murya, da kuma shafin Youtube?  Na gode.  Daga Aliyu M. Sadisu, Minna: aliyusadis@gmail.com, http://mumbarin-musulunci.blogspot.com

- Adv -

Wa alaikumus salaam, Malam Aliyu ai wannan bai da wahala ko kadan. Tunda kana amfani da masarrafar Blogger ne, idan ka shiga shafinka, sai ka matsa Sign In daga can sama a hannun dama, kana gama shigar da bayananka, za a kaika inda tsare-tsaren shafinka yake ne, kai tsaye, wato: DashBoard.  Daga nan sai ka je LayOut, inda ake canza wa shafi kamanni da kintsi.  Idan ka samu kanka a can, sai ka matsa alamar Add a Gadget dake sama daga hannun dama.  Shafi zai budo mai dauke da nau’ukan masarrafai masu fa’idantarwa da za ka iya kara wa shafinka. Sai ka zabi wanda kake so.  Idan ma baka ga abin da kake so ba, duk bai baci ba.  Daga hannun hagu can kasa za ka ga inda aka rubuta: Add Your Own, sai ka matsa, ka shigar da adireshin shafin da kake son karawa, ka matsa Add URL. Ka gama kenan.  Da fatan ka gamsu.


Allah ya saka da alheri, ya kara imani. Daga: 08064022965

Amin summa amin, ina godiya matuka da addu’o’inku. Na gode


Salaamun alaikum Baban Sadik, don Allah wace waya ce tafi shahara a duniya yanzu?  A gaya min sunanta da lambarta, da wanda ke bi mata.  Daga: Salisu Samaila Zaria: 08065165819

Wa alaikumus salam, tirkashi!  Malam Salisu ya shirya kenan.  Akwai su da yawa.  Akwai Z10 na kamfanin Research in Motion masu yin wayoyin Blackberry, duk bata wuce naira dubu dari da goma ba.  Akwai Samsung Galaxy S4, wacce ke iya lura da yanayin fuskarka da murya a duk sadda kake amfani da ita.  Idan kana karanta wani abu a shafin wayar, tana iya sinsino yanayin fuskarka, da zarar ka kawar da kai, za ta rage hasken shafin don manejin sinadaran batir.  Idan kana karanta rubutun da ke shafin, da zarar ka zo harafin karshe, nan take shafin gaba zai budo da kanshi ba sai ka bude ba.  Don a nuna maka cewa lallai ana amfani da yanayin jikinka ne.  Duk kudinta bai wuce naira dubu dari da talatin da biyar ba. Ba tsada.

Akwai kuma na ya-ku-bayi, irin su Nokia Asha 501 wacce ke gab da fitowa.  Mai shafaffen fuska ne, ba ta da allon shigar da bayanai irin na al’ada, sai wanda ke ciki. Komai dinta latse-latse ne. Idan har ta fito, ba a zaton za ta wuce dubu goma shatara.  Wadannan kadan ne cikin wadanda za iya tunawa.  Allah sa a dace, amin.


Assalaamu Alaikum Baban Sadik, Allah kara hikima da basira, amin.  Don Allah ina son ka turo mini kasidar nan wacce kayi kan haske, wato: Light.  Ga adireshin Imel di na: yahuza@mail.com.  Ka kasance cikin koshin lafiya, sako daga: Yahuza Idris Hotoron Arewa, Tunshama, Ketare, Kano: 08095588320

Wa alaikumus salam, Malam Yahuza ina godiya matuka. Na kuma cillo maka kasidar, amma makalawa nayi a jikin sakon, don haka sai ka saukar (Download) kafin ka iya budewa. Har wa yau, idan wayarka ba ta iya bude bayanai da aka taskance da masarrafar Microsoft Word, to dole sai ka je mashakatar lilo (Cyber Cafe) ka ciro.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.