Sakonnin Masu Karatu (2022) (1)

Raguwan Adadin "Likes" a Facebook Page

Da farko dai, su shafukan Facebook (Facebook Page) an kirkiresu ne don baiwa mutane shahararru da kamfanoni da kungiyoyin da kuma kasashe ko hukumomin dake son tallata manufofi ko hajojinsu da ra’ayoyinsu ko kuma, a wani lokacin ma, don basu damar fadakar da mutane kan wasu al’amuran rayuwa. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 15 ga watan Afrailu, 2022.

129

Kamar yadda muka saba lokaci zuwa lokaci, daga wannan mako zuwa makonni biyu dake tafe za mu amsa wasu daga cikin tambayoyinku ne.  Bayan an sha ruwa kuma sai mu ci gaba da bayani kan siffofin Web 3.0, kamar yadda muka fara  a makonni ko watannin baya.  Allah karbi azuminmu da sauran ibadojin da muke gabatarwa a wannan wata mai albarka, amin.

———————–

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka. Yaya ibada?  Kuma yaya iyali?  Da fatan kowa lafiya.  Muna godiya matuka da yadda ake wayar mana da kai dangane da wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa na zamani.  Tambaya a nan ita ce: wai me yasa ne nake ganin adadin mutanen da suka yi “Like” din shafina a Facebook yake raguwa?  Misali, ina da mabiya gudan 20,000 da doriya, amma sai inga adadinsu na raguwa, alhali kullum sai na ga mutane suna “like” din page din?  Wace hanya kuma zan bi don magance wannan matsalar?  Na gode matuka, Allah saka da alheri.  – Dahiru Isa, Numan, Adamawa, ddisa20@gmail.com.

Wa alaikumus salam Malam Dahiru, barka dai.  Ina godiya matuka da addu’o’inku.  Allah karbi ibadarmu baki daya, amin.  Dangane da tambayarka kan dalilin raguwan adadin wadanda suka yi “Like” din shafinka a Facebook, amsar hakan na bukatar Karin bayani don fahimtar yadda tsarin “Facebook Like” yake ga shafukan dake dandalin.

Da farko dai, su shafukan Facebook (Facebook Page) an kirkiresu ne don baiwa mutane  shahararru da kamfanoni da kungiyoyin da kuma kasashe ko hukumomin dake son tallata manufofi ko hajojinsu da ra’ayoyinsu ko kuma, a wani lokacin ma, don basu damar fadakar da mutane kan wasu al’amuran rayuwa.  Idan ka bude shafi a Facebook, akwai wasu siffofi da shafin ke dauke da su, wadanda kuma dasu ne Injin Facebook ke amfani wajen kururuta shafinka ga masu ta’ammali a dandalin don su ganshi kuma suyi ta’ammali dashi.

Na farko, kafin mutane su iya amfana da shafinka sai sun matsa alamar “Like” dake shafin.  Wannan zai basu damar iya gani da kuma karantu dukkan sakonnin da kake wallafawa a shafin.  Kuma iya adadin wadanda suka matsa “Like” iya adadin shahara da sakonninka zasu samu cikin sauki.  Yawan “Likes” ne ke tabbatar da farin jinin shafi, da kuma ingancin sakonnin dake wallafe a ciki, da kuma cewa lallai shafi ne ingantacce ba wai an bude shi bane don zambatar mutane.  Wannan za sa a duk sadda ka wallafa sakonni, nan take injin Facebook zai nuna wa wadanda suka yi rajista da shafin kai tsaye.  Idan sun hau shafinsu za su rika ganin sakon.

- Adv -

Na biyu, ma’amalar da mutane ke yi da sakonninka shi ake kira: “Engagement”, kuma shi ma yana taimakawa wajen kara farin jinin sakonnin dake shafin.  Wannan ya hada da matsa “Like” dake karkashin sakon da ka rubuta.  Ko yada shi zuwa shafukansu “Share”, ko kuma matsa alamar gamsuwa ko rashin gamsuwa dake dauke a emoji da dai sauransu.  Mafi tasiri cikin tsarin ta’ammali da sakonni a shafi shi ne yin ta’aliki (Comments).  Dukkan wadannan ana kiransu “Engagements”.  Habakar wannan tsari na ta’ammali da shafi a Facebook, wato: “Engagements”, yana dogaro ne kacokam ga tsarin “Likes”.

Tsarin “Facebook Page Like”

Shi “Likes” ko matsa alamar “Like” a shafin Facebook, daidai yake da yin rajista da gidan yanar sadarwa a Intanet, wato “Website”.  Idan ka yi “Like” din wani shafi, to, ka zama mamba din shafin baki daya.  Komai aka wallafa, kai tsaye za ka gani a dandalin labarunka na Facebook (News Feed), a duk sadda ka hau.

A daya bangaren kuma, idan kaci gaba da tallata shafinka a kafafen sadarwa daban-daban, za ka rika samun karuwar “Likes” a duk sadda mutane suka ci karo shafinka, musamman idan sun gamsu da irin sakonnin da kake wallafawa.  Haka idan suna da abokai, za su iya ganin sako daga Facebook cewa: “Wane ya yi rajista da shafi kaza…”, misali.  Wannan zai sa su ma su bibiyi shafin don matsa “Likes”, iya gwargwadon yadda alakar kusanci take tsakaninsu.

Sai dai kamar yadda ka tambaya, a wasu lokuta muddin kana la’akari da adadin masu “Likes” a shafin, za ka rika ganin yawa ko adadinsu na sauka; wato yana raguwa.  Ga galibin masu shafuka, wannnan abin damuwa ne sosai.  Na sha samun tambayoyi irin wannan a dandalin Facebook ta hanyar Messenger, kuma na fadakar dasu kan dalilan.  Amma tunda tambayar ta kara maimaituwa a nan, zan jero dalilan gaba daya, da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance hakan.  Duk da cewa a daya bangaren kuma, raguwan adadin masu “Likes” a shafinka na iya zama alheri ta wani bangaren.  Zan yi bayani a takaice a karshe.  Bayani kan manyan dalilan dake sa adadin masu “Likes” a shafin Facebook (Facebook Page) ke raguwa, shi ne abin da ke tafe a mako mai zuwa.

A ci gaba da kasancewa tare damu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.