Ziyarar Gidajen Yanar Sadarwa (1)

Daga wannan mako za mu fara kai ziyara ne zuwa wasu gidajen yanar sadarwa na harshen Hausa, don baiwa masu karatu daman ganin yadda suke, da irin tsarin dake cikinsu, da kuma fa’idar dake tattare da ire-iren wadannan shafuka.

353

Makon Jiya

Ga dukkan alamu kasidar makon da ya gabata tayi tasiri matuka, kamar kasidun sauran makonni.  Na gane hakan ne daga yanayin sakonnin waya da Imel da kuma kira da wasu daga cikin masu karatu suka yi ta yi.  Hakan har wa yau na dauke ne da bukatun neman Karin bayani ko godiya, kamar dai yadda aka saba.  Don  haka na ce bari mu dan killace rabin shafi don jawabi kan biyu rak daga cikin wadannan bukatu, kafin mu shiga sabon babin wannan mako.

Yanayin Girman Wayar Salula

Da akwai tambaya kan ko zai iya yiwuwa mutum ya aika da jakan sako (attached file) daga akwatin Imel dinsa, ta hanyar wayar salula?  Wannan, kamar yadda na shaida ma mai neman Karin bayani, ya danganta ne kacokan da irin girman mizanin wayar salular.  Sai kuma girman sakon da za a aika.  Da farko dai abin da za mu lura da shi shine, wayar salula ta sha banban da kwamfuta, wajen girman mizani da yawan karikitan da ke taimaka mata sadar da sako.  Don haka idan kana son wayar da za ta rika taimaka maka wajen aikawa da jakunkunan bayanai ta hanyar Imel, idan ka tashi saya sai ka yi ma masu sayarwa bayanin irin abin da kake bukata.  Wayoyi irin wadannan na da matukar tsada, kuma za ka samu suna da girman jiki.

 Tafi Sannu Kwana Nesa

Idan ka fara amfani da fasahar Intanet da hanyar wayar salularka, za ka ga banbanci wajen budowan shafi da rufewa da dai sauransu, kasa da yadda ka saba gani idan a kan kwamfuta kake lilo.  Wannan na faruwa ne saboda mizanin wayar ba daya yake da na kwamfuta ba.  Sannan ka tuna cewa kana amfani da wayarka ne a matsayin makalutun sadarwa (modem), wanda ke zuko sigina daga jikin Uwar Garke (Server), don shigar maka da shi a matsayin harrufa da hotuna ko makamantansu.  Don haka dole ne a samu tsaiko.  Amma a galibin lokuta, za ka samu masu mashakatar tsallake-tsallake (cyber café) na samun sigina ne daga tauraron dan Adam ko kuma Broadband, a takaice.  Wanda shi ya fi sauri da hanzari wajen zuko sigina.  Don haka sai a yi hakuri.

………………………………………………………………………………………………..

 GAMJI.COM (http://www.gamji.com)

A wannan mako za mu fara kai ziyara ne zuwa wasu gidajen yanar sadarwa a giza-gizan sadarwa ta duniya, don samun wuraren yawo da kuma sawwake ma kawunanmu jigilar neman gurabun shakatawa ba tare da dogon yawo maras ma’ana ba.  Idan mai karatu bai mance ba, a kasidar Waiwaye Adon Tafiya, mun nuna muhimmancin sanin wuri da abin da mutum yaje yi a duniyar gizo.  Domin wuri ne mai matukar fadi, cike da abubuwa masu kama da juna amma asalinsu da nau’in dabi’arsu ta sha banban.  In kuwa haka ne, kenan akwai bukatar sanin inda mutum zai je, me zai yi, kuma me yake ko yaje nema, don guje ma bacewa ko walagigi.  Wannan tasa za mu samu makonni uku nan gaba, don kawo bayanai da samfurin wasu gidajen yanar sadarwa da mai karatu zai so a ce can yake kashe dare ko rana, wajen amfanin kudinshi da lokacinshi.  A yau za mu fara da gidan yanar sadarwan GAMJI.COM, in Allah Ya yarda.

Gidan Yanar, Kacokan

 

 

- Adv -

Wannan gidan yanar sadarwa ginanne ne, kayatacce, wanda kuma aka gina da kwarewa irin ta ilimin manhajar kwamfuta, wato Computer Programming Skills.  Duk da yake akwai ilimin gina gidan yanar sadarwa na musamman, ta amfani da fasahar Hypertext Markup Language (HTML), a yanzu masana kan ilimin manhajar kwamfuta (Computer Programmers) sun kwace fagen.  Don yanzu galibin gidajen yanar sadarwan da ke giza-gizan sadarwa ta duniya da wannan fasaha ko ilimi aka gina su.  Domin masu wannan ilimi ne suka kirikiro masarrafa irinsu Dreamweaver, Frontpage da dai sauransu.  Gidan yanar sadarwan Gamji na dauke ne da Frames a matsayin babban fuskan da ke zauren gidan.  Shi Frame wani kwarangwal ne da ake ginawa a makala shi a saman  zauren gidan yanar sadarwa, ta inda duk dakin da ka shiga a gidan, ba zai bace maka ba, za ka ci gaba da ganinsa.  Da zarar ka shigo Gamji, abin da za ka fara cin karo dashi shine tambarin Bismillaahir-Rahmaanir-Rahim, wanda aka lika cikin harshen larabci.  A kasan basmalan ne za ka ga Home a tsakiya, Disclaimer daga dama, sai kuma Chatroom daga hagu.  Dukkan wadannan a saman Frames suke.  Don haka duk shafin da ka budo a gidan yanan, za ka ga wannan  bayani yana binka.  Frames kenan.  A dore yake a saman shafin zauren gidan gaba daya, don haka duk inda ka bude, zai kasance a kasansa.  Daga nan kuma sai aka kasa zauren, wanda ke kasan Frames, zuwa bangare hudu, daga sama zuwa kasa, kuma wadannan bangarori ne suka kunshi dukkan abubuwan da ke cikin gidan yanar sadarwan gaba daya.

Me Ke Ciki?

Akwai tarin bayanai wadanda suka shafi makaloli (Articles), da hotuna, da sauti da kuma rariyar likau (links).  Bangaren farko daga hagu, za ka samu tarin bayanai na makaloli da mutane ke aikowa ana dorawa don masu karatu da nazari.  Wadannan kasidu ko makaloli na samuwa ne daga hanyoyi biyu; hanya ta farko ita ce  ta masu aikowa gama-gari, irika iri na.  Idan kana son duniya taji ra’ayoyinka, sai ka aika ma Uban Gidan Yanan a webmaster@gamji.com.   Ka tabbata ka aika da cikakken adireshinka.  Zasu buga, don a karanta.  Hanya ta biyu kuma ita ce, ta hanyar marubutan Gamji, wato Gamji Writers.  Gamji na da marubuta da dama; wasu na raye, wasu kuma sun riga mu gidan gaskiya.  Akwai Muhammad Haruna (shahararren dan jarida), marigayi Wada Nas, Marigayi Abubakar Jika, Mr. Mobolaji Aluko, Mr. Paul Mamza (Malami a ABU), Malam Aminu Magashi, Dr. Aliyu Tilde da dai sauran marubuta da dama.  Wadannan marubuta ne na musamman  da Gamji  ke da su.  Kuma kasidunsu ne ake watsawa a bangaren hagu da ke zauren gidan yanan.  A bangaren da ke biye kuma, takaitattun labarai ne da suka shafi Nijeriya gaba daya.  Wadannan labarai sun hada da babban labari (Editorial) na jaridun Nijeriya, da muhimman labaran cikin gida, na kasa, da labarai daga jihohin Nijeriya, da labarai musamman kan siyasa, sai labarai kan wasanni (sports).

A wannan bangare, ba labarum karara za ka gani ba, a a, rariyar likau ne, wadanda zasu kai ka inda za ka samu labaru cikakku.  Sai bangaren da ke biye da wannan, wanda ke dauke da rariyar likau na takaitattun labarai kan duniya gaba daya.  A wannan bangare, an nau’anta labaran ne ta la’akari da gidajen yanar sadarwan su.  Akwai labaru daga gidan yanar sadarwan BBC, da na Al-Jazeera sashen turanci, da CNN, sai kuma sauran gidajen yanar sadarwa da ba wadannan ba.  Dukkan labaran na samuwa ne ta hanyar bin rariyar likau, wanda zai sadar da kai inda kake son zuwa.  Sai kuma bangare na karshe, wanda ke hannun dama, daga sama zuwa kasa.  Shi wannan bangare ne na musamman, inda aka tanada ma masu ziyara musamman daga wasu kasashe, don samun bayanai kan hanyoyin kasuwanci a Nijeriya ta hanyar jaridun Nijeriya irinsu Daily Champion, Daily Independent, Daily Sun, Leadership, Newswatch, Punch, Guardian, The News, Triumph, Vanguard, Weekly Trust, da Al-Mizan.  Har wa yau, a kasa an tanadi wasu gidajen yanar sadarwa na musamman irinsu EFCC, Gumel, Kanoonline, NigerDelter, Amanaonline, da Arewa Online.  Wadannan su ne abubuwan da ke tattare a Gamji.com.

 Manufa

Ga duk wanda ya saba shiga wannan gidan yanar sadarwa ta Gamji, zai fahimci cewa duk wannan jigila da suke yi, manufarsu shine baiwa mai karatu daman samun bayanai ko labaru cikin sauki, a tattare a wuri daya, ba tare da kayi ta yawace-yawace ba wajen neman labaru.  Idan ka shiga Gamji, za ka samu dukkan labarun da kake bukata.  Idan ma bincike kake son yi, na tabbata sai ka gaji da kasidu wadanda zasu taimaka maka wajen kafa hujjoji kan abin da kake bincike a kai.  Za ka samu kasidu kan siyasar Nijeriya, tattalin arzikin kasa, addini, al’adu, zamantakewa, shakatawa, shugabanci da dai sauransu.  Wadanda suka fi kowa amfana da Gamji su ne galibin ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje.  Domin a nan suke samun dukkan bayanai duk safiya ko yammaci.  Na sha buga waya ko aika ma wasu abokanai na da ke turai waya ko sako don sanar da su wani sabon abu da ke faruwa a gida Nijeriya, sai su ce mani ai sun karanta labarin a Gamji.  Sau tari ire-iren kasidu ko labarun Gamji ne za ka ta cin karo da su a majalisun tattaunawa ana yadawa.

Shahara

Alal hakika gidan yanar sadarwan Gamji ta shahara fiye da yadda mai karatu ke zato, daga Nijeriya har wajenta.  Wannan a fili yake.  Biyu daga cikin abubuwan da suka haddasa haka kuwa su ne; nau’in bayanan da ke ciki (labaru, kasidu, makalu da sauransu), da kuma Zauren Hira da Tattaunawa (Chat Room), in da galibin masu ziyara kan yi rajista don zuwa hira da tattaunawa da sauran maziyarta ‘yan uwansu.  Saboda yawan masu ziyara a kullum da wannan gidan yanar sadarwa ke samu, babban gidan yanar sadarwa ta kasuwancin Intanet ta duniya, wato AMAZON.COM (http://www.amazon.com), ta baiwa Gamji lambar yabo na kasancewarta na daya a sahun gidajen yanar sadarwan da ke Nijeriya, wajen samun mafiya yawan maziyarta a kullum.  Har wa yau, idan mai karatu ya shiga gidan yanar sadarwan sashen Hausa na BBC (http://www.bbc.com/hausa), zai ga cewa bayan Gamji, babu wata gidan yanar da suka lika gidan yanansu da ita, sam sam.  Sannan idan aka zo kan gidan yanar sadarwan da ke makare da tarin bayanai na gida Nijeriya zalla, wadanda ‘yan Nijeriya ne suka rubuta (a ko ina su ke), wato Local Content a takaice, a nan kuma Gamji  ce ta zo ta biyu, a dukkan gidajen yanar sadarwan da ke Nijeriya.  Wannan ke nuna irin karbuwan da Gamji ta samu a duniya gaba daya.

Uban Gidan Gamji

Bayan duk mai karatu ya ji wannan, watakil zai so jin ko wa ke da Gamji?  To a takaice dai ba wata kungiya bace ko wata jiha daga jihohin Nijeriya ta kafa wannan gidan yanan ba.  Mai wannan gidan yanar sadarwa wani bawan Allah ne, mai suna Dr. Ismaila Iro (PhD), masanin kwamfuta da manhajojinta (Computer Programmer).  Yana zaune ne a kasar Amurka, duk da cewa yana nan Nijeriya a halin yanzu.  Shi ya gina gidan gaba daya, ya kuma dora a giza-gizan sadarwa ta duniya, don amfanin al’umma.  Kuma shi ne Uban Gidan (Webmaster).  A kullum shi ke lura da gyatta kasidu da labaru da makalu, don kayatar da masu ziyara.  Wanda ke taimaka masa a nan gida Nijeriya kuma shine Malam Magaji Galadima, shi ma wani mahiri ne a fagen kwamfuta da manhajojinta.  Malam Magaji ne ke lura da tafiyar da dukkan wani abin da ya shafi Gamji ta bangaren Nijeriya.  Kuma duk wannan aiki suna yinsa ne a matsayin kyauta ga jama’a, ba mai biyansu ko sisi.  Wannan na daya daga cikin abin da ya kamata mu rika dabbaka shi; duk lokacin da Allah Ya hore maka wata kwarewa kan ko mene ne, yana da kyau ka ciyar da al’umma don ita ma ta karu.  Allah saka musu da alheri, amin.

Shawarwari

Kafin mu karkare zan so sanar da mai karatu wani abin da ke da muhimmanci dangane da wannan gidan yanar sadarwa ta Gamji.  Tarin kasidu ko makalolin da ke makare a ciki, ba kadan bane, gaskiya.  Ina da yakinin cewa idan aka tattaro su, aka buga su a matsayin littafi, zasu gina babban dakin karatu mai zaman kansa, tabbas.   Don haka na ke son ba masu wannan gidan yanan shawara wajen karfafa tsaro (security) musamman a banganren rumbum kasidu (archives).  Domin na san wani dan ta’adda (hacker/cracker) ya so rushe rumbun gaba daya, wajen shekarar 2002 in ban mance ba.  Don haka a kara tsaro ta wannan bangare.  Shawara ta biyu kuma ita ce, a yi kokarin sanya manhajar Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine Programme), wanda zai rika taimaka ma mai neman bayanai (musamman kasidu) ba tare da bata lokaci ba.  Duk da yake an shirya kasidun baya ne a tsarin shekara-shekara, amma samun tabbataccen rumbu da kuma manhajan da zai taimaka wajen zakulo kasidu masu nasaba da abin da ake nema zai dada taimakawa.  Allah sa mu dace baki daya, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA says

    AMIN

Leave A Reply

Your email address will not be published.