Kimiyya da Fasaha a Kasashen Musulmi (5)

Bukatar Sauyi a Kasar Musumlmi

An buga wannan makala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 10 ga watan Disamba, 2021.

430

Duk da dai har zuwa yau, wato qarni na 21 da muke ciki, abun takaici za ka samu akasarin addinai a duniya na ganin wasu sashin ilimai na kimiyya kamar su Ilimin Asalin Halittar Babbar Duniya (Cosmoslogy), ko kuma Ilimin Asalin Yadda Halittu Suka Samu (Evolution), na kawo wa imanin su farmaki. Amma idan ka kwatanta wannan ra’ayin nasu da na babban katafaren malamin nan xan qasar Persia dake da ido a kusan kowanne fanni na ilimi da ake kira da al-Biruni (973-1048) za ka ga sun bambanta, ga abunda yake cewa:

- Adv -

“Masu qaramin sani ququmi suna cewa, ‘To wai menene ma fa’ida da amfanin waxannan iliman na kimiyya da fasaha?’ Kai ka ce ba su kwana da sanin cewa babban falalar da Allah ya bambanta mutum da dabbobi baki xaya ba ita ce ta ilimi. Wanda a dunqule, duk halitta, xan adam ne kaxai ke da irin wannan xabi’a ta qwaqwa wajen gano haqiqar abubuwa ta amfani da su ilimi, wato sani, kuma xan adam xin na neman ilimin ne kaxai saboda girman ilimin da buwayar sa, saboda shauqi da sururin zuciya da farincikin dake samun waxanda ke tafarkin neman ilimin ba zai tava kwatantuwa ba har abada ga sauran jiye-jiyen daxi na jiki ko na zuciya da makamantansu. Saboda duk inda xan adam ya kai ka gujewa sharri ko cuta, ko kuma duk son sa ga riskar alheri ko ci gaba, hakan har abada ba zai tava samuwa ba sai ta amfani da ilimi kaxai. A nan, sai mu ce bambancin amfani da fa’idar a bayyane suke. Haka kuma za mu iya tambaya shin wane alfanu ne yafi rinjaye dangane da Musulmai su rungumi kimiyya da fasaha da sauran ci gaba ko kuma suyi watsi da su?”

Alhamdulillah! A yau, akasarin Musulmai sun yarda cewa babu wani karo ko kishiyantaka tsakanin Musulunci da kuma Kimiyya da Fasaha. Alal haqiqa ma duba da yadda ake samun tinga-tinga ko musayar yawu tsakanin qasashen Musulmai da kuma qasashen Yamma za mu ga yadda qasashen Musulmai ke jin ba daxi duk yayin da aka nuna gazawarsu ko rashin katavus xinsu a vangaren ci gaban kimiyya da fasaha da sauran ci gaban duniya ba kamar takwarorinsu ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.