Web 3.0: Fasahar “Artificial Intelligence” (3)

Tsarin “Biometric” a Wayoyin Salula

Masana harkar sadarwa da dabi’un dan adam suka ce a yanzu dai, babu wanda yafi kowa sanin dan adam irin wayar salularsa, da kwamfutarsa, da kuma shafukan Intanet din da yake ziyarta. Wayar salularka, ta wani bangare, ta fi matarka, da dan uwanka, da abokanka sanin hakikanin sirrinka. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 1 ga watan Afrailu, 2022.

191

Tsarin “Biometric” a Wayoyin Salula

A galibin wayoyin salula da kwamfuta yanzu suna zuwa ne da fasahar tambarin yatsu (Biometric Lock/Fingerprint), wacce da zarar ka shafa dan yatsanka sai kawai ta bude, ba sai ka yi ta hankoron shigar da Kalmar sirri ba. Haka akwai masu zuwa fasahar bude kwamfuta ko wayar salula ta amfani da fuska (Facial Lock/Unlock). Wayar salular da nake amfani da ita – Huawei Y9 (2019) – tana dauke da wannan tsari na fasahar “AI”. Duk wanda na taba kiranshi da wayar, ko ya taba kirana, na amsa muka yi magana – ko bayan shekara ne – da zarar na budo lambarsa don sake kira, nan take zan ga sako a gefen sunansa cewa mun taba magana da juna ta hanyar kira. Idan layukansu biyu ne a wayata, wacce muka yi waya dashi ta karshe, ita ce za a sanya wa alama. An dabi’antar da wayar ne tun wurin kera ta, da irin wannan siffa, ta amfani da wani tsari mai suna: “Supervised Learning”, karkashin fannin “Machine Learning” da bayaninsa ya gabata a baya. Dukkan wadannan tsare-tsare sun samu ne ta hanyar wannan fasaha ta “Artificial Intelligence”, wato: “AI”.

Masana harkar sadarwa da dabi’un dan adam suka ce a yanzu dai, babu wanda yafi kowa sanin dan adam irin wayar salularsa, da kwamfutarsa, da kuma shafukan Intanet din da yake ziyarta. Wayar salularka, ta wani bangare, ta fi matarka, da dan uwanka, da abokanka sanin hakikanin sirrinka. Wannan zance ya fi gaskatuwa a kasashen da jama’a suka rajja’a kacokam wajen amfani da hanyoyi da na’urorin sadarwa don gudanar da rayuwarsu.

Domin wayarka ce kadai tasan wa da wa kake kira ko suke kiranka. Wayarka ce kadai tasan wasu shafukan Intanet ne kake ziyarta; a bayyane ko a boye. Gidajen yanar sadarwa ne kadai suka san wani shafi ka hau, kuma me da me ka aiwatar a shafin. Wayarka ce ta san ina kaje yau, ta wani titi ka bar gidanka, ta wani titi ka dawo gidanka. Wayarka ce kadai ke sanin hotuna nawa ka dauka, sannan wa da wa ka aika musu. Wayarka ce kadai ke sanin mutum nawa ka rubuta wa sakon tes, kuma mutum nawa ne suka rubuto ko aiko maka. Ita ce har wa yau ta san, cikin sakonnin da kake aikawa ko aka aiko maka, guda nawa ne ka goge, sannan guda nawa ne ka boye su a wayarka. Shafin Youtube, da Dandalin Facebook, da manhajar TikTok, da WhatsApp, da SnapChat, duk sun fi kowa sanin abokan huldarka, da jujjuyawarka. A takaice dai, wadannan na’urori da kafofin sadarwa sun samu wannan kudura ne ta hanyar wannan fasaha ta “Artificial Intelligence”. Bayan su, ba wanda ya san abin da suka sani kanka, sai Allah Mahaliccinka.

- Adv -

Nan Gaba…

Wadannan, a takaice, su ne kadan daga cikin misalan wannan fasaha ta Artificial Intelligence, ko AI a gajarce. Kuma daya ne daga cikin fasahohin da zasu samar da gamammen tsarin sadarwar dake tafe a marhalar sadarwar Intanet zubi na 3, wato: “Web 3.0”.

Kamar yadda bayani ya gabata, daga yanzu duk wata na’ura ta sadarwa; kwamfuta ce ko wayar salula ko waya nau’in “tablet” ko “tab”, za a rika gina su da wannan fasaha ta “Artificial Intelligence”, wato: “AI”. Ba su kadai ba, hatta gidajen yanar sadarwa da za mu rika ta’ammali dasu nan gaba, za su zama suna dauke da fasahar AI. Su ma jakar sakonninmu na Imel, da fasahar AI za su kasance. A tare da cewa ma jakunkunan sakon Imel na kamfanin Google mai suna: “Gmail”, tuni suna dauke da fasahar AI a tare dasu. Sun san wadanda ke aiko maka sako akai-akai, sun san galibin maudu’in sakonnin, sun san adiereshinsu (wannan shi yafi komai sauki), sun san lokuta da kuma bangaren duniyar da sakonnin ke zuwa. A la’akari da wadannan bayanai da kake karba ko aikawa, a hankali za ka rika ganin tallace-tallace masu dauke da wadannan siffofi, a jakar Imel dinka.

Don haka sai mai karatu ya fadaka, ya kuma zama cikin shiri. Rayuwa za ta canza ta bangaren sadarwa, kuma gaba gaba za a yi, ba baya ba. Kusan duk wani fanni na rayuwa da ake iya gudanar da shi ta hanya da na’urorin sadarwa na zamani, wannan fasaha ta AI za ta shiga cikinsa, tayi uwa da makarbiya, ta mamayeshi don tabbatar da tasirinta a ciki. Daga aika sakonni zuwa karbansu, da hada-hadar kudade na zamani ta hanyar kafafen sadarwa, da ma’amala a shafukan sada zumunta, har zuwa fannin likitanci da kere-kere, duk wannan fanni zai mamaye su nan gaba.
Shi yasa, idan nan gaba kaji ance ga wata wayar salula mai Magana ko hira da mutane tare da basu shawara kai tsaye, kada kayi mamaki. Idan kaji ance ga mota tana tafiya ba direba a cikinta, kuma ta dauki fasinja, kada kaji mamaki. Idan kaji ance ga gidan sayar da abinci ko wajen mai shayi da na’ura c eke kai wa mutane abincinsu har kan teburinsu, kada kayi mamaki. Domin yadda bincike da ci gaba a fannin kimiyya da fasahar sadarwa ke tafiya a gaggauce ba kakkautawa, haka sababbin abubuwa za su rika fitowa, a yanayi da kintsin da suka sha bamban da al’adar rayuwa a baya. Abin da ya rage wa mai karatu kawai shi ne, ya kintsa tunaninsa, da ya sallama wa Allah lamarinsa, ya koyi ta’ammali da wadannan hanyoyi da na’urorin sadarwa iya gwargwadon hali, domin nan gaba baka san inda za ka tsinci kanka ba.

Mu zama wayayyu; idanunmu a bude.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Yahaya Almajiree says

    Aslm gaisuwa da jinjina zuga
    BABAN SADIQ .Allah ya Kara ilimi da fahim
    Kuma Allah yakara imani

Leave A Reply

Your email address will not be published.