Sakonnin Masu Karatu (2021) (4)

Kwarewa a Fannin Kariyar Bayanan Sadarwa (Cybersecurity)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 12 ga watan Fabrairu, 2021.

227

Assalamu alaikum Abban sadik, ina maka fatan nasara a dukkan al’amuranka na rayuwa.  Ina da sha’awan zama kwararre a fannin “Cybersecurity” a rayuwata. Shin, a matsayina na wanda ba shi da hali, ta ina zan fara? Sako daga Muhammad bin muhammad Numan: ibnumuhammadnuman@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Muhammad.  Ina godiya da addu’o’inku.  Fannin “Cybersecurity” shi ne bangaren dake bincike kan hanyoyi da dabaru da kuma ka’idojin tsaron bayanai a giza-gizan sadarwa na Intanet.  Ma’ana, hanyoyin da ake iya kare kai daga matsalolin kutse da satar da bayanai da gurbata su, ta hanyar Intaney.  Fanni ne mai kyau, kuma shi ne fannin dake tashe a yau, musamman ganin cewa kusan dukkan al’amuran rayuwa yanzu sun koma kafafen sadarwa ta Intanet.  Mafi girman tsarin da ke tattare da wannan kuwa shi ne tsarin ma’adanar bayanai na tafi-da-gidanka, wato: “Cloud Computing”.  Wannan bayani kan abin da ya shafi fannin “Cybersecurity” kenan.  Amma korafinka kan yadda za ka iya koyon wannan fanni da kwarewa a ciki alhali ba ka da hali, in na fahimci zancenka, shi ne baka da halin da za ka iya zuwa makaranta ka koyi karatun a nazarce.  Wannan, ta wani bangaren, ba matsala bace.  Domin, duk da cewa baka yi bayanin matsayin saninka da fahimtarka ba a karatun fannin kwamfuta, za ka iya karantar abubuwa da dama a Intanet, ta hanyar kwasakwasai na kyauta da ake tallatawa ko bayarwa a shafuka daban.  A baya na yi bayanin wuraren da ake iya zuwa a koyi karatu kyauta a Intanet, har ma a samu shedar karatu.  Wadannan wurare dai sun hada da shafukan yanar sadarwa inda za a koyi ilimin a nazarce.  Da kuma shafukan sadarwa inda za a koya ta hanyar bidiyo, kamar Youtube da sauransu.  Idan kana bukatar bibiyar wadannan bayanai da nayi, kana iya ziyartar shafin dake dauke da bayanin a Taskar Baban Sadik dake wannan adireshin: https://babansadik.com/sakonnin-masu-karatu-2016-15/.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, dole ne ka mallaki kwamfuta ta kashin kanka.  Domin na fanni bane kawai da za ka zauna kana ta zabga karatu a nazarce; dole sai da kwatanta abin da kake koyo a kullum.  Wannan ke nuna maka cewa, duk da nace akwai wauraren da za ka iya koyon ilmin na kyauta a Intanet, amma kuma sai ka yi hidima.  Ma’ana, dole ka mallaki kwamfuta, hakan na bukatar ka saya ko ka samu wanda zai baka.  Dole ya zama a galibin lokuta kwamfutar na jone da Intanet, domin sai da Intanet za ka iya isa aji, sannan da Intanet za ka rika samun Karin bayan ikan abubuwan da ake koya maka.  Wannan na bukatar kudi.

Wannan shi ne dan tsokacin da zan iya yi a halin yanzu.  Ina maka fatan alheri, kuma Allah sa a dace.  Na gode.

- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya amin summa amin.  Na kasance ne mutum mai matukar sha’awar son iya gina manhajar kwamfuta (Programming) amma na rasa ta inda zan fara. Shi ne nake neman shawara gun masana. Nagode. Kuriga Network: mustysham@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Kuriga.  Koyon gina manhajar kwamfuta na bukatar abubuwa da dama na fahimta da kwarewa dangane da kwamfuta kafin a kai ga batun gina manhaja.  Ban san iya fahimta da sanayyarka da yadda ake iya amfani da kwamfuta ba.  Amma mu kaddara kana da sanayya kan yadda ake amfani da kwamfuta, da yadda ake rubutu (Typing) – wanda shi ne ginshiki wajen gina manhajar kwamfuta.  Akwai dabarun gina manhajojin kwamfuta, wato: “Programming Language”, ya danganci wanda kake son koyo.  Duk da haka, tsarin gina manhajar kwamfuta yana da manyan bangarori guda biyu ne.  bangaren farko shi ne bangaren da ya shafi bayani gamamme kan yadda ake gina manhaja, da hikimomin rubutu, da yadda ake tsara aikin gina manhaja, da harshen fannin gina manhaja, da dai sauransu.  Bangare na biyu kuma ya kunshi yaren da kake son koyo ne.  Shi ma yana da nasa tsarin.

Akwai wurare da dama da za ka iya zuwa don koyon ilimin gina manhaja.  Kana iya koyo ta hanyar Intanet, kamar yadda na sha yin bayani a baya.  Sannan kana iya koyo ta hanyar zuwa makaranta.  Sai dai ka sani, makarantar da za ka je don koyon wannan ilimi, a dai Najeriya, zai zama na kudi ne.  Domin jami’o’inmu ba su da kwasakwasai kan koyon gina manhaja shi kadai, sai dai ka koyi ilimin a cikin jimlar kwasakwasan da ake yin digiri a kansu, kamar su: “Computer Science” ko “Information Technology” da dai sauran makamantansu.  Kuma galibi shekaru biyar ake yi a jami’o’inmu.  Don haka, ko dai kayi rajista don koyo karkashin wata makaranta ta kudi, ko kuma kayi amfani da makarantun dake kafafen Intanet don koyo.

Shawarar da zan baka ita ce, na farko dai ka mallaki kwamfuta taka ta kashin kanka.  Domin wannan ilimi ne dake bukatar a rika kwatanta abin da ake koyo a kowane lokaci; a dimance shi.  Abu na biyu, ya zama kana kowane lokaci, musamman lokacin karatunka, kana da siginar Intanet, don neman Karin bayani kan abin da kake koyo ko ake karantar dakai.  Abu na uku, idan ta Intanet kake koyo, ka tsara lokacin da zaka rika halartar wurin darasi.  Ya zama a duk yini ko a duk mako ko a duk wata, misali, kana da wani adadi na sa’o’i da ka kebe don nazarta da nakaltar wannan ilimi.  Abu na hudu, ka dauki yaren gina manhaja mai saukin koyo da fahimta.  Wannan zai taimaka wajen kara maka kaimi.  Amma idan ka dauki yare mai tsauri, kuma aka yi rashin sa’a kana da karancin hakuri, ba za ka kai labari ba.  Daga cikin yaruka masu sauki akwai yaren “Python”, wanda ba shi da wahalar koyo.  Sannan bayanai kan yadda ake amfani dashi suna nan ko ina a Intanet.  Bayan haka, idan ka fara kwarewa, yana da kyau ka zanbi bangaren da kake son yin fice a cikinsa.  Akwai bangarori da dama.  Akwai bangaren gina manhajar kwamfuta zalla.  Akwai bangaren gina manhajar wayar salula na Android, da na iOS da sauran makamantansu.

A karshe, don neman Karin bayani, kana iya ziyartar taskar dake dauke da dukkan makalolin da na rubuta a baya kan salo, da yare, da tsari da kuma hanyoyin gina manhajar kwamfuta, ta wannan adireshi: https://babansadik.com/category/gina-manhaja/.  Ina maka fatan alheri, kuma Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.